Rashin Gata 166-170
🌼🌼RASHIN GATAH🌼🌼
```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```
*NAH*
```FOUR STAR'S```✨✨✨✨
*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*
```SADIYAH ABDULLAHI SHEH
(STYLISH BCH)```
*ZAINAB Y HUSAYN*
*(AUTAR HAJIYA)*
```ZARAH BUKAR```
```(CUTE ZARAH)```
Masoyan *RASHIN GATA* ```muna neman barar addua'ar Ku Allah ubangiji yabawa maman Yar ficika lafiya😭😭😭 pls kusata a addua'a don Allah😘
```
*TEAM# RGT*❤❤
166__170
Yana cikin wanan hali na tsananin mamaki da rud'ani tare da al'ajabi, yaji ringing d'in wayarsa, binta yayi zuwa kasa ya d'auka koda ya duba sunan Daddyn sa ya gani, cikin wani irin hali tare da faduwar gaba ya d'aga k'iran. "Sameer kazo Ina nemanka now" abinda Daddy ya fada kenan ya kat'se kiran batare da yajira amasar da Sameer d'in zai bashi ba..
Jiki a sabule yaje ya shirya, karasawa yayi wajan t.v ya d'auki key d'in motar ta yayi gidansu .
koda yaje bai zarce ko inaba sai part d'in Daddy, da sallama ya shiga d'akin sai dai ba'a amsa mishi ba, hakan yasa ya kuma Kara wata sallamar, daga cikin bedroom yake jiyo gyaran muryasa alamun sallah yake, guri ya samu ya zauna yana wani lumshw ido tare da kara shin-shina hannunsa ko zai jiyo kamshin cikin motar Nana dan tun da ya shiga motar yaji k'amshi kawai takeyi, ya d'an murmusa kadan.
Anan yayita zaman jiransa har ya idar ya fito zuwa parlourn nashi.
Yawwwa Sameer kazo?
yajiyo muryar mahaifin nasa yana kokarin fitowa yace "eh Daddy na karaso,"
Dai-dai lokacin da mahaifin nasa yake karasowa cikin makeen parlourn mai kyau.
Rissunawa yayi har k'asa yace "Daddy Ina wuni?" Cike da mamaki mahaifin nasa ya d'ago yana kallonsa, tare da matukar murna da mamakin wai shi yau sameer ya t'suguna har kasa yana gaidawa!, lallai Nana khadijat tafara gyara sameer, ya fad'a cikin ranshi aman har yanxu Daddyn nasa bai d'aina mamaki ba, haka ya daure yace," lafiya lau sameer ya khadijan?"
Tana nan kalau Daddy ya fad'a cikin sauri, babu wata matsala koh? yace "Eh Daddy babu matsala" mungode Allah yajikan mahaifa..
yafada cike da dauki dan bai son su gane cewar bai t'aba sanin itace ba bare kuma bata kullawa wace kowanne ma'aurata ke jinta. Jijjiga Kai mahaifin nasa yayi yana mai Kara kaunar Nana a ransa, dan duk a tunanin Daddy itace sanadin ladabin nan nasa.
To Allah yayi albarka, Sameer yace "Amin Daddy" ya Dora da cewa daman na kiraka ne saboda viza da nayi muku zuwa kasashe uku saudia, china & England dan zuwa honeymoon kai da ita nan da 3days zaku tashi dum gaban Sameer ya fadi tuni har kwala ya fara zuba masa yayi saurin ya share, shi yanxu yazaiyi daransa! idan Nana tace baza taba? Yasan daga ranar dasu Mummy sukaji baiko tab'a ganinta ba to zasu San komai, kuma yasan Ummansa ba karamin aikinta bane ta raba auran tunda sun ga baya so ga kuma wulakantar da ita da yaya.
Zaro viza Daddy yayi tare da mikawa sameer, a sanyaye yasa hannu biyu ya Karba tare da karayi mai wata godiyar cike da girmamawa wadda Daddy baisan shi da itaba, hakan kuma ta kara sashi jin kaunar yaron nashi da matarshi a cikin zuciyar shi.
Mikewa yayi dan shi yanzu hankalin shi yana ga Nana dan yanasan ya tabbatar da zargin shi na cewar itace matar tashi ko zuwa tayi, da wannan tunanin ya karasa wajan Momy.....
"My son whats wrong with you ne? Sai kace ba ango ba kabi duk ka wani susuce tamkar ba Sameer dan gayu da nasani ba" cewar Momy da tun shigowar shi taga duk yawani fada ga wata uwar kasumba daya bari hakan yasa duk yayi wani kamar dan 40years.
"Nothing Momy kawai tun sanda na dawo daga wannan tafiyar shine banajin dadin jikina so ina kokarin hutawa Daddy yace nazo yana nemana that's why kika ganni haka" ya fada yana shafa fuskan shi. Murmushi tayi tace "kaida keda babbar doctor a gida saita duba ka ko tsoron Allura kake?" Dariya yayi yace "Mummy nikam yar yarinyar nan bata dubani ai saita raina ni" dariya Mummy tayi sosai tace "yar yarinya ai tagama raina ka tunda kunyi aure" murmushi yayi dan yaga Mummy na neman juya mashi magana "yanzu kaje kayi wanka saika kwanta ka huta" cewa Mummy OK yace tare da barin d'akin yayi wajan Umma cike da faduwar gaba....
Sameer! ta kira sunan shi cike da tsoro, kallonta yayi tare da cewa "yes Umma ya gida?" Lafiya lau ta amsa tana kare mai kallo tsab sannan tace.
"Wai shin yaushe rabanka da kallon madubi?" Shikam ya rasa yadda zaiyi kowa sai magana yake mai ya kamata yaje yaga wai ya ya koma ne mikewa yayi ya karasa wajan madubin Umma yana kallon kanshi kafin yasaki wata dariya kamar wani tababbe, yace "wallahi Umma abubuwan ne sai a slow" yadan yi shiru sannan yace "inajin ma shi yasa Nana data ganni ta gudu daki."
Jin ya ambaci Nana yasa Umma cewa ahhto ai dole ta gudi kai ka ganka kuwa? ya kamata kaje kayi aski wlh da gyaran fuska ko ka dawo Sameer d'inka.
Mikewa yayi suka yi sallama sannan ya wuce ya shiga motar sa dan Yanzu ya tabbatar Nana ce matarshi dan haka yau zai fuskanceta su fahimci juna sai da ya fara zuwa yayi gyaran fuska sannan ya dan yi siyayya ya wuce gidan yana tunanin ta inda zai fara tunkarar Nana da wani zancen shine mijinta.
Yana shiga gidan direct kofar d'akinta yaje, knocking yayi mata ta zo ta bude dan gara tasan meya, zoyi tun kafin mai gidan yazo ya same su a haka.
"Da kallo ta bishi kirjinta na bugawa dan ganin kara wani kyau dayayi daga fitar shi yanzu......
Four stars🌟🌟🌟🌟
Comments
Post a Comment