TUNA BAYA 10-105

[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

ZAINABU Y HUSSEAIN

Page 10

Ko da Abba ya fita baizame koina ba, sai makaranta 'yammata ta GGUC Kachako dan samawa Zainabu takardar shaidar takardar fara makaranta tunda tayi comment Entrance.
Yaje batare da yasan kowa ba, amma cikin ikon Allah abokin sa da suka hadu a Ilori sukai cinikin goro dashi sosai dan yazo masa biki da gaisuwar Rahma shine vice a makarantar.
Sosai suka gaisa da tambayar juna da bayan rabuwa.
Saida suka gama sannan "ya gayamasa abinda yakawoshi da dalilin sa nason zainabu ta gyaru.
Hmm ikon Allah wallahi nima daka ganni sati biyu kenan dana kawo 'yar yaya ta, Maryam kwata kwata yarinyar bataji ga tsiwa da rashin kunya, all desame itama ummana ke riqeta.
Abin kunya kamar ni vice amma yarinyar nan kunyatani take, bata seniority duk wanda yamata yimasa take saidai aji kunyata a qyaleta, Allah ya kyauta dai zance ashe ba ita kad'aice bace, akwai zainabu.
Akwai kam, dan ni zainabu ma a yanzu bansan yadda za'ayi ta biyo niba.
Babu komai a wayo zaka mata, ko jibi zaka iya kawo ta, amma fa da munrufe karb'an mutane dandai kaine.
Nagode to sosai kuwa, dame dame za'ayi kenan?, no! ba sai kabada komai ba akwai uniform da books kayan provision kawai zaka mata.
Nan ya zauna godiya yayi, wani sanyi yaji a jikin sa ganin Allah ya taimake shi, Allah yasa zainabu ta gyaru haka ya mik'e suka qara musabaha ya fita.
Har wajen motar sa ya rakasa, saidayaga tafiyar sa shima ya shiga cikin makarantar.
Abban zainabu kodayafito daga makarantar cikin gari yai wato kano ta dabo cigari, mai mata da mota.
Kasuwar singa yashiga nan yaciro kud'i cikin First Bank 60k dan yiwa zainabu siyayya.
Yanson 'yar sa over zai iya qarar da dukiyar sa akan ta, bayajin fitar kud'i indai a hidimar zainabu ce.
Kayan tea ya siyo mata madara pick da Bunet blue gwangwani 4 milo ovaltine Lipton haka ya siyamata komai na kwali 4 na gwangwani 4.
Cornflakes da coaca ort carbin chocolates komai haka ya siyamata da yawa yana gamawa ya zuba cikin booth sai wanbai anan ya siyomata scandals da slipers ga sucks itama uku komai da akema yar gata shi akayiwa zainabu.

************
Baba a gaskiya baikamta kinaiwa zainabu wannan gatan ba, yai yawa ace akanta matar ubanta ta fita da sake wallahi ko ki gyara kona d'auke ta dan nagaji da ganin ta tana sangarta haka.
To uba na da zaka sani a gaba, kanamun fada, wani munafukin ya gayamaka?, ah kiji qarfin hali to wallahi bazatayuyu kuzo kuna aibatan yarinya ba, jibeka da wani kanka tashi ni tunda ba gaisheni kazo yi ba munafurci ya kawo ka
Murmushi Abban kano yai, yace ni kenazo gaisarwa ba wani ba, Hajiya Baba mai Rahma da Zainabu sannu uwa ga Aliyu da Umar Baba mai kalwar yan gayu.
Nan da nan saiga Baba ta ware sai sabuwar hira.
Baba! wayyo fitsari nakeji zai zubo, zainabu to kije kiyimana koba ruwa?.
Baba da mutum aciki kuma wallahi yakusa zubowa wayyo, gafara kaga waye cikin bayin nan yanaji zainabu zata shiga aisaiya fito.
A'a Baba ba'ayi haka ba to tayi acikin lungun can tunda da akwai wani cikin bayin. Bazatayi ba kaji taqi tayi, waye nace ya fito dan ita nasaka aka gyara bayin badan wasu ba, kowa da bayin sa ai daga yau ma kullewa zamuringa yi ehe kuma fito kona shigo.
Abban kano dai tsaye yai yana ganin drama lallai Baba tab da sake dole nadauki zainabu kota gyara.
Au kaine ma Idi meyasaka zaka shiga?, zainabu maza jekiyi kada ya zubo.

@ut@r  H@jiy@ ce
أم لزهرة
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

         ®NWA

ZAINABU Y HUSSEAIN

PAGE 12

"Tun safe Baba ta tashi zainabu tai wankanta tasaka kayan ta masu kyau(dama kunsan duk maisuna zainab da kwalliya da gayu to itama hakan take ga wannan zainabun).
Kud'in machine ta bata a hankali sad'af sad'af Baba ta bud'emata qofa yi sauri kitafi, kiyi nesa da gida sannan kihau machine kada aji qaran shi, "Baba ke wannan maganar.
Tana fita Baba tamaida sakata ta koma taci gaba da baccin ta.
Sannu tafara tafiya gashi duku duku ne, abin hawar ma yai wuya tunda gashi tafiya take amma ba taga ko d'aya yazo ya wuce ba.
Tafiyar mota taji, bata juya ba saima qara sauri datake cak taji motar ta tsaya kusa da ita.
Abba ne! ganin sa tai ya fito arcewa zatayi taku biyu kacal yai ya damqota sai cikin mota.
Ihu tafara Baba kizo wallahi ya biyo ni wayyo ku taimaken jamaa makarantar Aljanu zaikaini,lol su zainabu ansha kuka kafin me bacci ya tafi da ita shikam jinsa yake tamkar ya ajiye wani kaya ne akan sa.
Tafiyar awa biyu ce takaishi Kachako har lokacin Zainabu bata farka ba illa ma qara gyara kwanciyar ta datayi abin ta.
Har cikin makarantar ya shiga bai tsaya koina ba, sai saitin ofishin mataimakin shugabar makarantar.
Hannun sa ya miqa baya ya d'an bubbugi kafad'ar ta juyi tai na farko saidaga can kuma ta bud'e idon ta tar.
Kallo ta bi Abban nata da shi kafin ta tuno boarding school fa yaka ta ihu tasaka tana kiran Baba amma ina Baba tai nisa.
Bud'e murfin motar yai tana tirjiya tana komai haka ya jata sai ofishin.
Ko da suka shiga batabar kukan ba saima qaruwa da yai lokacin da taga malamin ya bawa Abba hannu sun gaisa daga baya kuma taga ya miqo uniform blue da farin Hijab nan ne kukan ta ya qaru.
Dariya vice yai yace tab wallahi Maryam 2 kenan kasan haka yarinyar nan taimun harda rantsuwa bata sanni ba wai sato ta nai naga tijara wannan rana amma gashi harta saba da ita zan had'a su.
Waya ya janyo, magana yai akan akirawomasa Zahra, Sadiya Feedoh dukkan su yaran yayun sane da qanne.
Basu jima ba suka shigo nuni yai musu da zainabu akan su kama ta suje tacanja kayan sawar ta sannan sutafi Hostel tare
Allah sarkin zainabu taga ba halin guduwa dole tasa ta mikewa wajen Abban ta taje rungume shi tai tasaka kuka bayan ta ya bubbuga kana ya d'ora da nasihar zama lafiya da kula da addini.
Jan ta sukai suka fita, suma suna tuna randa aka kawo su haka sukai ta bore.
Wajen Maman kitchen suka tafi Mama Lubei itace komai nasu a school d'in kuma itane chief a b'angaren girki.
"Gayamata sukai ankawo sabuwa itama cousin d'in  suce yau aka kawota uniform zata saka, nan Mama Lubei ta karb'i zainabu hannu biyu itama ta d'oramata da nasihar "kiyi haquri zakiji dad'in makarantar nan baran ma gaki 'yar uwa suma rarrashin ta sukai daga nan suka koma Hoste tunda time en shiga class ya kusa suma uniform zasu saka su tafi.
Abban ta yaga lokacin tawowar su jiyayi kamar yace ya fasa amma ina yanason zainabu tai karatu.
Sallama yaiwa vice d'in yatafi bayan ya ajiyemasa kayayyakin zainabu d kud'i dubu Talatin.
*******
A can gida Baba tagama shirin ta kaf, an had'a kaya ana shirin wai Abban Zainabu yazo tace masa unguwa zata sai kwatsam sallamar Abban kano taji
Kicin kicin tai da fuska bataso zuwan sa a wannan lokacin ba .
A'a Baba wannan kaya haka saikace masu shirin barin gari bangane ba?, hararen sa tai "tace idan ma garin zan bari ina ruwan ka kaji yaro da munafurci kul banson shishiggi.
Dariya yafara qasa qasa sabida yasan zancen, shiyasa yazo ayi komai a gaban sa
Baba ganin Umar baidawo ba yasaka"tace Aliyu nidai zantafi kacewa Umar saina dawo gobe zan dawo ba jimawa zanyi ba.
Ina zaki to amma sainaga kamar kayan tafiyarki irin wata biyun nan zakuyi?
Wata biyu waya gayamaka, to kwana bakwai zanyi kuma ni d'aya.
"Assalamu alaikum a'a Yaya ne sa sanyin safiya haka? Eh nine ina kaje haka kaima?.
Nasha tafiya kam daga kai zainabu makaranta nake.
Makaranta? Wacce zainabu kuma? Taki mana ai dama inajin duk qullin ku da ita shiyasa nai timing naku yau Allah yaban sa'a nakaita nabarota tana kukan rashin ki "tace nagaisar mata dake.
"Wayyo Jama'a kuzo ya cuceni Ummaru sun had'a baki sun kaimin zainabu makarantar Aljanu wayyo amma kun cuceni ha'inci qiri qiri Amina Allah ya isa kece silar komai yanzu saidai naga yaran wasu zainabu Allah ya isar miki.
Cuta ancuceki kun barni da TUNA BAYA tsakanina da zainabu, Aliyu harda kai ko?.
Kuka take bilhaqqi sosai, Umar kam shiru yai matan gidan ne dai suketa bata baki kiyi haquri Baba idan da aure tai fa?, kamar yau ne kiyimusu afwa amma hakan shine ya dace da zainabu.
Eh naga alama kaf da had'in bakin ku munafukai. Ranar dai Baba har wani fever ce takamata haquri kam da qyar tayi shi duk da haka dai saidata make Abban kano shi dariya yake mata sosai
Washe gari ne kuma suka tarkata sai Kano ta Dabo tare da Amina ansha kukan rabuwa Baba ta kowa ayi fad'a a shirya.
Abban Zainabu kam kukan nasa harda na tuno Rahma itama Baba haka dan ita saidata furta"Rahma Allah yakai haske qabarin ki kinyi shahada Rahma munyi rashin ki ga kuma zainabu da suka d'auken saboda mugun ta sudai shiru sukai.
Amina datafara kawo shawara cikin mota itama saidata kwashi rabon ta na jarabar Baba.

Autar Hajiya ce

أم الزهراء
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

        ®NWA

ZAINABU Y HUSSEAIN

PAGE 11

Kai Abban kano kawai yake kadawa, sai ido dayake binsu da shi, amma shi abin Baba qara girma yake dadai ba haka Baba take ba amma ji lokaci d'aya ta canja.
Maganar ta Itace ta dawo dashi hayyacin sa dayaji tana fadin yauwa zainabu kinfito? Eh Baba bara wanke qafata da hannu na kinsan ance idan kashiga bayi to kawanke hannu da qafa saboda datti.
Yauwa d'iyar arziqi, maza to kici abinci sai a huta koh? Eh amma sainayi sallah. Tom.
D'aki suka shiga anan suka fara tad'in su shikam Abban kano kallo kawai yake binsu da shi.
Lah Baba kinji Kamar muryar Abba ko ya dawo? Ke rabu dashi ba fushi yake ba to yayita yi, kinji gidan mu shiru ba Amina shima yazo sainacimasa mutun ci.
A'a Abba karki masa haka, to yar albarka.Abba ne da sallama ya shigo rinfar Baba, a'a Yaya ne sannu da zuwa kasha hanya nima fa kano naje Kamar na biya saidai nace dare ya kusa ashe kana nan sannu.
Yauwa Umar sannu kaima nazo naga baka nan? Eh wallahi ya MOHD da ZAHRA?
Suna lafiya Mohd yana gaidaku kasan munyi waya jiya yace Abba wallahi kano tafi koina dad'i Cyprus d'in nan kamar prison nakejin ta.
Ayya ai karatu ne banda abinsa, kuma da aiyana tare damu, nan da shekara uku ai yana gida ya gama insha Allah.
Allah ya yarda.Zahra kam kullum Abba zanzo Rano ina zainabu nace kibari idan kika candy sai kizo, yanzu dai a haka muka bari idan tai candy zatazo.
Hira sosai suka fara daga nan sukai alwala sai masallaci.
Zainabu oh to mezamuci yau?, Baba nima sai tunani nake mezamuci ga Aunty Amina bata nan dama baki koreta ba.
Aikuwa to yah kenan?, bara nayi nafa iya, taliya zan dafa, ke me kika iya ba ruwa na ki qone, Allah Baba zanyi, da qyar take barin ta.
Taliya leda guda ta d'akko, sannan aka yi jajjagen albasa da attaruhu, yadda taga Aunty Amina tayi kwanaki haka tayi, tafara source din kayan miyar, sannan aka zuba ruwa aka kawo kayan spices aka zuba, Taliya dai ta had'u koni Auta saidanayi santin ta azuciya ta dandai nasan basamu zanyi ba amma da sainaci.
Ko da su Abba suka fito daga masallaci, tadin Baba da zainabu suke, Abban kano ne "yace Umar kamun wata alfarma guda mana? Mene ita yaya komene zanmaka indai zan iya.
Zama ka iya, zainabu nakeson kaban ta koma wajena da zama, nagaji da ganin ta haka, Baba zata b'ata mana ita, bakaga d'azu ba wallahi Idi yana fitowa waje kawai yayi, saboda tijaran Baba gaskiya kai frankly dai zaman ku ya qare cikin qauyen nan cikin week d'in nan katarkata komai naka kadawo cikin gari.
Matar ka Amina kuma ko gobe ne kuje biko da ita za'a tare Baba zata zauna gida na nagaji da ziryan hanya kaji?.
Yaya haka ne amma banqi ta taka ba,nidai da Baba zamu komo amma zainabu banda ita.
Saboda me?. Nagamai mata komaie na tafiya makarantar kwana gobe insha Allah zan kaita, nima nagaji da ganin ta haka shiyasa na yanke wannan hukuncin,ko Baba batasan da tafiyar ba saina kaita na dawo sannan zangayamata.
Ikon Allah Umar kayi tunani, kuma hakan shine daidai Allah ya taimaka, karkacewa yayi ya zago rafa ta five hundred yabashi "yace a qara mata, karb'a yai sosai yai godiya sannan ya qara masa wata godiyar "yace on behalf of ur daughter wannan godiyar.
Murmushi sukai a tare sannan suka juya sai cikin gida.
A tsakar gidan suka tarar da Baba da zainabu a zaune sunacin abinci, Abban kano ne yace a'a kaga 'ya da uwa ba bissmillah? Zainabu ce "tace Abba nazubomaka nice nayi kuma tai dad'i ko Aunty Amina sai haka.
Da gaske zainabu na lallai to qaro akan wannan takun muci na zumunci dan wataran bazamuci ba yanayi yana dariya.
Miqewa tai ta juyo duka cikin qaton tray ta d'akko pure water ta ajiye.
Abban kano bai qyamaci abincin bq zama yai sosai yaci yamaisa dad'i Abban ta ma haka nan dai tasha shi albarka harda gift na dubu d'aya ya bata zainabu sai murna.
Lokacin da zai tafi sallama sukayi da Baba sannan suka fice zaure shida Umar.
Baba ta tawo kenan dan tagayamasa ya siyowa zainabu Takalmi saitaji maganar data tarwatsamata tunanin ta lokaci guda.
Lallai wato had'a baki sukai zasu kaimata zainabu makarantar Aljanu to zasuga tsiya gobe ma zasu kaita, hmmm basai kunganta ba da sauri ta koma da baya tai cikin d'aki.
Zainabu tasamu tagayawa, "tace zainabu kinga gobe da sassafe saimu fice kullum haka zamuringa yi harsu gaji mugwaye kawai musa raba hanta da jini nan da sukaita hiran ko da Abba ya shigo basu nuna masa sunji komai ba.
Washe gari koda Abba ya tashi wanka yai ya d'ebi kajin da ya siyo mata yasaka a mota.
Shiga yai wajen su, turus yai ganin kwad'o ajikin d'akin kenan fita sukai?.
Haka suka runga yi harwajen kwana hud'u, yaukam da sa'a dan hiran su yaji harda shewa suke masa akan yadda suke asha ruwan tsintsaye dashi.
Zainabu gobe da wuri saikitafi Jan garu kinzauna, nikuma zan qarasa had'amana kayan, daga can sai Damagaran kinga saisukai wata zainabu amma ba keba.
Wata biyu zamuyi, koba haka ba? Haka ne Baba, yauwa mu kwanta da wuri kada lokaci ya qure mana.
Dariya ce takamashi sosai baishiga ba illa gaba da yai yana tiqar dariya, bai tsaya yayi dariyar shi d'aya ba saida ya bugawa Abban kano suka dara.

أم الزهراء
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

      ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEAIN

PAGE 13

CIKIN MAKARANTA

Haba ke zainab kiyi haquri mana kuka ba abinda zaimiki saima cutar dake da zaiyi, wallahi muma haka mukai amma gashi Kamar bamuyi ba, kiyi haquri yanzu class zamu tafi kada aganki kina kuka amiki dariya yi shiru mune qawayen ki yanzu kuma duk wanda ya tambayeki kice ke qanwar muce tunda Uncle yace ke 'yar aminin sace kinga munzama 'yan uwa kenan ko ace FOUR STARS.
D'an murmushi tai tace tnq all especially u ta nuna Feedoh yar ficika. Dariya sukai duka sannan suka kama hanyar wajen Assembly tunda yau Monday.
Tun daga nesa zainabu tace Feedoh yanaga bulala? Ke yi shiru Adda Benazir kenan itane headgirl tanada kirki amma kad'an, waccen fa Sodangi kenan Compound prefect farar can kuma Rookei kax wallahi zainabu ba'a tab'a duka naba a duniya kamar yadda Rookei kakumi tai mun takoina duka take Sodangi kam bala'i ke kaf....
Kuuu me kuke jira bazakuyi joining line ba?, ba komi sister yanzu zamuyi ok Junior classes according to ur hight senior ma haka.
Layi kowa yabi itakam zainabu ido ne nata.
One by one sister Rookei da Sodangi sai Fatee Shuwa suka fara duban farce da kitso wanda baiyi ba zainabu saidai taga anzubamasa mari sannan yai kneel down, kai ta jinjina ganin anzo kusa da ita yasaka tafara gyara hijab d'in ta, ke mene haka ki bud'e kanki sai wani qara gyara hijab kike, oya lemme see ur hair? Hhhh su zainabu ba turanci ko da akwai kad'an ne nata batasan me tace ba itadai ta kalleta sai ta juya da kanta gefe.
Sodangi ce "tace ke anamiki magana bud'e kanki agani ko babu gashin ne?, Kamar tace babue saitai shiru abin ta.
Bud'ewa tai hasbunallu wa niimal wakeel gashi ne baqi sosai ga yawa ga tsawo wanda har ya kere kafad'un ta  sosai da kyauro ta qulle shi.
Hannu Rookei ta tafa "tace good gal ke gamai gashi koh? ana kitso amma ke bakiyi ba dats good.
Sodangi jeki gun Anee ko Shuwa ki amsomin scissors dan saina miki ado da gashin, ina kike so rabi zan raba abar gaba ko baya?.
Shuwa ce tace kubarmata bayan tayi parking dashi dariya suke sosai, Anee ce tazo da scissors d'in a hannu gashin nata zasu kama saisukaji magana a bayan su.
Hey mene Haka? Adda Benazir "tace haba dai kwa bari ku amshi uzurin ta idan na accepting ne to if not saikumata komai ne.
Ke meyasaka bakiyi kitso ba? Adda she's new commer yanzu aka kawota ma batasan komai ba.
Ayya sorry kinji yarinya, to kunji plx guys u better maintain ur self wannan ba rayuwa bace idan mutum yai laifi sai a hukuntashi amma idan ba haka ba dan Allah kujanye daga garesa plx.
Maida hijab naki zama a fara tafiya class lets go ko? "Tace dasu Sodangi da Rookei kax, kwafa sukai kana sukabar wajen.
Cikin class suka sami gu suka zauna kafin malami yashigo saida sukayi tad'in wajen Assembly.
Mathematics dashi suka fara sannan sai English da Home economic sosai zainabu ta tsaya ta fuskanci abubuwan da ake koyarwa hartaji garama da aka kawota tasan zata iya turanci itama tazama irin Zahra ta kano.
Break aka fito nan ma taga sharri kala kala na prefect sosai tafara jin haushin Sodangi da Rookei kax taga sune mugwaye cikin sauran prefect d'in.
Time en tashi yanayi suka koma cikin Hostel su a Blue House suke itadai binsu take a baya last kwana itace tasu nan taga kaya da loka qatuwa Mama Lubei itace ta shigo ta nuna musu kayan zainabu "tace gashi nan vice ya kamata sosai taji dad'i daga sukai alwala aka tafi mosque.
Wajen alwala taga jaraba tab kokawa kowa yake yayi amma prefect suna zuwa za'a matsa suyi sannan wanda yake layi ya biyo bayan su.
Amiran masjeed itace kad'ai taga kamar mai kirki dan komai nata cikin sanyi take Aunty Hasy taji ana cemata 'yar lukuta mai kirki da ita.

Autar Hajiya ce
أم الزهراء
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

         ®NWA

ZAINABU Y HUSSEAIN

PAGE 14

Suna idar da sallah aka tafi dining, shinkafa ce da miya sai nama ga salad abincin mai dad'i kamar na gida.
Taga wasu na rubibi amma su kiran su Mama Lubei tai tabasu nasu cikin flask.
Suna gama ci aka shiga islamiyya basu tashi ba sai 6 nan ma kafin suje Hostel sukai alwala.
Zainabu tazama 'yar kallo dan duk maganar ta ajiye ta gefe tai take fuskan tar komai da kowa.
Zainabu tashi yau dutyn Aunty Shuwa wallahi kaf school d'inan tafi kowa tsiya itace Labour prefect yau kuma za'ayi sanitation tawo muyi sauri mu d'auki tsintsiya mufara share steps karda arigaamu ace muyi wankin toilet.
Mts nifa nagaji wallahi da aikin makarantar nan agida bana aiki dan haka bazan zo nan nayi ba.
Haba pretty kiyi haquri muyi kinga rannan badan niba wallahi a tuqa-tuqa da tuni Aunty Sodangi ta zaneki kiyi haquri Autar Baba mai kalwa Pretty ta FOUR STARS sannu qawata aminiya ta.
Dariya tafara "tace kunji ku wace ni ai pretty sai Sadiya badai zainabu ba.
Munji tashi mudai muje,to "tace sannan ta miqe.
Riga da wando suka saka kitson ta qanana ta bajesu a bayan ta sannan suka fita bayan sun adana key nasu cikin pants d'in su mai zip.
Kan Step suka had'u da Aunty Sodangi duk tsayawa sukai a baya itakam zainabu gefen ta zata wuce saiji tayi anja rigan ta tabaya keech ta yage.
Ke nafa lura bakida kunya bakisan Sodangi ba kenan?. Qa'ida ta idan naho steps tsayawa akeyi saina wuce ba nabin right hand mutum left dole katsaya harna wuce amma ke naga alama kamar kanki na rawa.
Kut wallahi bazan yadda ba tunda kika yagan riga ba ke kika siyamun ba wallahi saikin biyani.
Keee tas ta d'auketa da mari taqara d'auke ta wani, da hannu ta nuna zainabu "tace tunda nake ba yarinyar data tab'a yimun haka..saini zainabu ko a haka naci riba nayi cacar baki da ke.
Tabbas haka yake pretty tamu kin rama mana ko baki duketa ba kin yagamata qima muguwa kawai sauran Rookie kax Feedoh tace tana maganar tana nuna ta da yatsa.
Ihu ne Sodangi kawai batayi ba, amma ta shaqa sauka tai da sauri sukam suka bita da ihu suda sauran students.
Rookie ce ta hango Sodangi tana tawowa alama ta nuna hawaye take zubarwa da sauri taqarasa gunta sisto mene haka ko maran ce? Hmm sisto... Sai hawaye nan da sauran prefect d'in suka rikice lafiya? Da qyar tai musu bayanin abinda yafaru.
Wayyo zo kuga qufula da harzuqa wajen Shuwa da Rookie da sauri suka bazama sai wajen da suke.
Su zainabu kam anashan ana cin dariya saijin duka sukai ta koina Allah sarki su Sadiya basuji ba aka had'a da su.
Bush sukai dasu sannan "su kace kowacce ta yanko reshe daidai tsayin ta ba yadda sukai haka suka hau bishiya suka yanko.
Dasu aka lafce su, sunji jiki sun doku sannan Rookei tai alama da suyi growing ba sassauci haka suka jibgesu son ransu daga nan sukai tafiyar su inda zasu.
Shuwa kuma tazo "tace su miqe aje ai sharan lab da yanke ciyawa
Ranar FOUR STARS sunsha wahala koni Auta saidana tausaya musu.
Kowacce tana shiga Hostel kwanciya tai Zahra ce ta miqe a kasalance ta tafi wajen vice.
Da shigar ta zubewa tai kuka kuka tafara jeromasa bayanin qarya da gaskiya. Hooo ransa ba qaramin b'aci yai ba ace Haka akayiwa yaran sa impossible hannun ta yakama suka tafi.
Yadda su Sodangi sukaiwa FOUR STARS haka vice da kansa yai musu yace su tsallen kwad'o zasuyi sunayi yana dukan su.
Zane su yai tas, daga nan yakafamusu worning akan yaran.
Kowa yasha wahala. Haka rayuwa taita tafiya dad'I da rashin sa su zainabu ansaba rashin mutunci sai abinda yai gaba suna foam one amma iskaancin su yakai na SS3.
Yau duukan su idan kagan su sanye suke da check(House wear) red colour ne nasu zasu prep duk ran Thursday akeyi so zainabu ce a gaba anata repeating karatun Intergrated science da wata formula datake son ganowa ya akayi aka sameta shiyasa ko hmm d'in ta ba'aji.

Autar Hajiya ce.
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

     ®NWA

ZAINABU Y HUSSEAIN

PAGE 15-17

"Hmm Pretty zo kiga halal kema baki gane wannan English?, da sauri ta juyo tace wanne? Na yau mana idiom nake magana kai, haba Zahra nagane saikce ke bari a fito night prep saina miki bayani.
Ok wallahi ni nashiga duhu akan sa tunda pretty tagane kamar mungane ne
Naji back to our business yarinya tana gama fad'a ta juya karatun ta.
FOUR STARS ga su Sodangi a block naku wallahi ku kuma suke nema naga harda Asy khaleel assistant prefect na prep kuzauna kada ku fito wallahi.
Tab wallahi saimunje ayi ta qare Feedoh ce ke maganar, haka sukai kam ta Purple House suka bi sukaje block d'in nasu.
Tun daga room 1 sukaga mutane a tsaye harzuwa room 4 gashi kowanne mutum tai tsintsiya ce a hannun sa.
Omg 'yam uwa we forgot at all yau bamuyi potion ba munshiga uku wayyo mu wallahi saidanace Feedoh kibari na share kikace yanzu zamu dawo gashi nan yau ta hau kan mu
Kinsan shiga toilet dai da jaraba, gashi bucket d'in namu ma anfasa shi garin bugo ruwa, munga ta kanmu.
Rookei kax itada Sodangi sune suka fara checking kwanar FOUR STARS, dats good Sodangi "tace basuyi ba kinga munada hujja akan su yau ko ba haka ba?.
Haka ne kam dama natara kaya su zasu wanke har pants da bra saisun wanke shi, basu yaran vice ba wanki ma yi musu ake to yau sai sunyi.
Kin musu mai sauqi, ni wankin qafa zasu min d'aya tana gogemun d'aya na susan kai yau zasuci qaniyar su ai.
A gaba suka tasa su Sodangi itada Asy kaf kayan wanki suka jibgo musu, ranar sunga takan su kam.
Abin haushi pants nasu duk wasu yai staining a haka suka wanke suka shanya da Sadiya da Pretty ruwa kuwa dama da kokawa ake d'iba, inda Allah yaso su Adda Benazir tana wajen so basubi layi ba tunda wankin prefects ne.
A can Zahra da Feedoh sune harda tausa da yanke farce saikace wata sarauniya yadda ta hakimce a kwanar su.
Suna gamawa wajen 4 wanka sukai kawai sannan suka saka Orange wear nasu, wasuw blue wasu red its depend da block d'in da kake. da akwai sports yau tsarin Benazir ne wai da yamma zasuyi abinda ake early in d morning amma yau sun kaishi  evening, kai da wahala zainabu tace.
Zainabu Allah sarki yau an tuno Baba shiyasa take shiru, ba wanda yaimata magana sabida sunsan ko sunyi ba kallon su zatayi ba yau lokacin na Baba ne.
****
"Tab amma Sir Idris ya iya mugun ta bulala 20 a qafa kuma?, hmm kekikejin zafin ta wallahi batashigan ba, kai zainabu naga har kuka kikai?, kukan saina rama masa, dan hawayena bazai zuba a banza ba, kukan na takaici ne yadda mukayie aikin mu cikin kwanciyar hankali amma yace bamuyi dai dai ba shima saiya d'an d'ana.
1:50 lokacin za'atafi dining sukuma suka sad'ad'a machine nasa suka sawa qusa tayar gaba data baya kaf saida suka sace ta wajen petroleum kuma,suka tsiyayar da kaf dinsa a cikin wata jarka goge wajen sukai yadda baza'ace tsiyayewa akai ba.
Da sauri suka koma kitchen abincin su suka amsa wajen Mama Lubei da gayya suka fito suna dariya dan a tunanin Sodangi itace zata zubmusu yau mairaba abincin batazoba shiyasa prefects suke bata san yaran 'yan gayu bane.
2-10 suka fita aka kad'a komawa Hostel, haushi sukaji saboda basuga yadda Sir Idi zaiyi ba.
Murna Sadiya "tace, kunganshi turowa yake dariya suka kwashe da ita harda riqe ciki ga shi akwai nisa tsakanin su da get, taimkon su guda baigan su ba kuma a tunanin sa baiga wanda zaimasa ba shiyasa yai shiru yakama gaban sa.

3 Months later.

Yau idan kaga yara da manya kaf d'insu cikin annashuwa suke saboda yau visiting wasu tun safe ma iyayen su sunzo wasu kuma da yawa suna tsaye a bakin gate suna jiran tsamanni.
Inda Mama Lubei take kwana nan FOUR STARS suka share qaton parlour ne so kowacce gefe taje tasaka daddumar ta ana jiran 'yan gida.
Iyayen Feedoh sune suka fara zuwa daga Katsina zokaga tsalle baran dataga kwalaye da cooler tasan ba magana abin.
Kaisu tai masaukin su nan suka zauna ga Yaya Kito da yaya shuni Amira Aunty Beeboh kai anzomata da yawa a gida bakin ta yaqi buduwa.
Sadiya ma da Ya Sadam tafara cin karo sai Ya Hajja da Aunty  suma da abin arziqi a hannun su itama dai yadda Feedoh tai haka tai.
Wajen iyayen nasu taje zainabu aka zauna anata hira dama su duk family d'ayane har Zahra itama da nata suka zo duk tare suke abin su anata hira suma suna basu labarin school da dad'in ta.
Zainabu har 11 shiru ba kowa nata nan da nan idan ta ya kad'a kasa zama tai cikin su da sauri ta fita, bayan ta suka bi Hostel zata koma suka tsaidata ita tana dole saita koma su suna ta tsaya za'a zo mata.
Can acikin speaker taji ana zainabu talwaran Baba tana inaa?  kasa kunne tai yes itace da gudu tai hanyar gate.
Ido ta bud'e ganin yawan 'yan gidan su ga Baba kamar ba ita ba.

Autar Hajiya
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

          ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEAIN

PAGE 18-20

Baba ta canja totally Swiss ne a jikin ta d'inkin yaimata kyau ga mayafin ta a ka, haqoran ta duk ba goro qafarta tai kyau d'as wallahi da bazata gane Baba ba.
Sai Aunty Amina Maman kano Zahra Abban kano da Abban ta sai Anker qawar ta da gudu taje takama Baba, abin dariya sai kuka kuma.
Zainabu me kike ci haka, inacan inata tunanin ki, zainabu Umar ya cucemu koh? A'a Baba da sweet school d'in amma naqaro wulaqanci sai mun zauna dai.
Zahra kema kinzo sannun ku habeebaty Nafee I miss u much yarinya masifaffiya.
Abban kano sannun ku Aunty ashe kin koma nazata kinyi zuciya lale dai gara Abba da kadawo d ita.
Daquwa Maman kano taimata.
Tarkatawa sukai sai inda sukaiwa iyayen masauki, labari kam kowacce iyayen ta sunsha dan a tare sukai komai abincin su kam agaban iyayen suka had'e abinda yake iri d'aya nama kowacce kamar had'in baki kaji biyar sai soyayyiyar miya kowa anmasa.
Baba taji dad'in ganin zainabun ta sosai.
Har ita suka fita gaisawa da qawayen su da kuma senior d'in su. Sodangi suka had'u da ita abin arziqi suka gaisa da su zainabu Baba harda mata addua.
Sunsha yawo har village saida aka kaisu Mama Lubei tasha godiya wajen Baba.
Zahra ita kakar su taje Umrah shiyasa da tuni itama tana tata shagwabar.
Komai yatafi yadda ake so, time yayi na tafiya maimakon ayi murna sai kuka Abban kano "yace zainabu kamar yau ne wataran zaki dawo gida fatana kiyi karatu kinji?.
Iyayen su fad'a suka qarai musu na nutsuwa da kula, daga nan kowa yakama gaban sa.

5 Months later time en CANDY.

Ranar 12-7-2008 ne ake gudanar da bankwana na candidates students cikin harabar makarantar Kachako.
Kaf SS3 students sunyi shirin su kowacce daka ganta zakaga trolley nata a baya tana ja.
Ashobe sukai na green white green, sunyi kyau sosai ga malamai a jere ga wad'anda sukazo d'aukan su the remaining students kuma a can gefe masu murna nayi mugwaye sunyi candy masu kuka sunayi wad'anda da kirki tsakanin su.
Speakers ne reras a wajen sauti yafara tashi na waqar da sukai (kunsan 'yan boarding da waqa kamar mawaqan gaske).
Sodangi ce a gaba tana kuka saboda sabo turken wawa, a bayan ta Shuwa, Rookie kax, Asy khaleel, Anee, Benazir da yawan su dai kowacce hawaye take sharewa baitin farko daga bakin Sodangi yafara "tace.
"Bankwana..Bankwana Bankwana.....bankwana....
"Bankwana yau za'aiyo rabuwaaa.....rabuwar nan da ba'a sake gamowaaa. 2008 'yan candy na kachako mundage munayi muku bakwana heehee.
Abin tausayi kaf daukan amshin sukai idaniyar su na zubda hawaye na rashin standard yes zasu qara ganin juna ko a'a?
"Ni Sodangi ninake kuka na d'akko akwati zana wuce katsina.
"Ni Rookie kax yau inata bakwana, na d'auko jaka ta zana wuce Yobe state.
Kowa zaizo yayi wasu Bauchi irin su Adda Benazir, shuwa Maiduguri, Asy khaleel Lagos, Anee Rimi Amiran Masjeed (Hasy) kano kunga kenan kowacce garin ta daban yafiya suke nema ga kowa da Malamai wasu suna sunyafe saboda tausayin su daya kama mutane.
Zainabu itama kuka take ganin kowacce idon ta nakanta.
A tsarin waqar da kuma yadda babu mai shigowa cikin filin, amma zainabu tausayi ya d'ebeta da gudu ta tafi cikin su kuka tasaka tare ta zagayo da hannun ta tai huging nasu sai kuka, suma rungumeta sukai na yafemuku dukkan ku Allah yabaku good results, Ameen sukace ba qaramin kyau abin yai ba dayake akwai masu videos a wajen.
D'aya bayan d'aya suka fara tafiya, Sodangi harta shiga mota da gudu ta fito ring ta ciro a hannun ta zainabu tasawa peck taiwa hannun sannan ta rungumeta da gudu ta juya sai motar.
Shuwa kam ribbons na kanta ta ciro tasawa zainabu, sannan ta juya, Rookei Takalmi ne sabo d'an yayi a qafarta yake itama shi ta ciro tabawa zainabu, take it idan kinje SS3 plx kisaka kinji pretty?I will suna magana like sunyi mutunci before d'in nan
Malamai da students abin sai ya burge su kuka kuma dole kai dan tausayi.
Haka kowacce ta tafi anayi ana d'agawa juna hannu.
Adda Benazir head girl itace last d'an kwalin ta na head girl ta ciro ta d'aurawa zainabu, kai ta jinjina mata u ar so much sweetheart pretty I really like ur style, plx vice principal abawa zainab matsayina idan takai kumun wannan taimkon?.
Vice da kuka yaci qarfin sa, a hankali yace insha Allah daga nan ta kama hannun Zainabu sai wajen FOUR STARS ta had'e hannayen "tace FOUR STARS FOREVER Insha Allah wishing u all da best in ur life, tana fad'a tai gaba.

Nikaina Auta kuka ne yaci qarfina saboda tausayi, dole tasaka na ajiye abar typing d'ina dan na huta.

Autar Hajiya ce
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

       ®NWA

ZAINABU Y HUSSEIN

PAGE 21-23

Tun bayan candy da abinda ba a rasa ba zainabu tadawo silent sosai kuma takejin kewar Aunty Sodangi da Aunty Rookei dama baya zata dawo data goge rashin jituwar dake tsakanin su.
Haka komai yacigaba da tafiya kafin sufara jarrabawa ta qarshen zango
Anytime FOUR STARS cikin prep suke evening da night ko sports basa zuwa sosai dan sunason zuwa na d'aya shiyasa suka dage.
Alhamdulillah angama exam, amma sunada remaining 2 weeks before atafi hutu da wannan students d'in da 'yan SS2 masu shirin zuwa SS3 da malaman su ake had'a debates wani classes kuma Hausa Drama gashi nan dai.
Cikin FOUR STARS kowa da club nasa ba a waje guda suke ba, Zainabu a Hausa club take, Feedoh Igbo, Yoruba shine wanda Sadiya da ZAHRA suke ciki.
Ba bacci kullum cikin kad'e kad'e da raye raye suke ba kama hannun yaro.
Yau itace ranar hutu kowa anbashi result nasa a hannu, zainabu first, Zahra second itada Sadiya third Feedoh kaf d'in su dariya da murna suke, lokacin tafiya ne yasaka kowacce idon ta raina fata sunaji Kamar idan sunje bazasu dawo ba amma ba halin cewa bazasu koma gida ba.
Zainabu Abban kano ne yazo d'aukan ta, shine ma kowanne hutu yake kawota yakuma zo d'aukan ta.
Feedoh Yaya Shuni ne yazo zasu wuce Abuja Zahra Lagos zata wuce sadiya kam tare da zainabu suka tafi idan taje gidan su ita azo a d'auke ta.
Hawaye dai saida aka zubar, cikin motar Abba dariya yake "yace kaga zainabu wato kukama kike zakizo gunmu naga kamar ma kinfi son su akan mu yanzu murmushi tai kawai a haka suka qarasa gida.
Baba tun da Abba ya tafi ta dawo gate ta zauna su Mama dariya kawai suke mata da zahra ganin tun jiyama baccin Kirk takasa yi.
"Taita cewa oh gobe i yanzu muna tare da zainabu, ko tayi bacci ko kuma hira zatamun zance dai kala kala.
Qaran motar da Baba taji aida sauri ta miqe, oyoyo d'iyata oyoyo zainabu ta dawo zainabu ta dawo.
Da gudu zainabu ta tako sai jikin Baba,murna sosai sadiya ita kanta saidata dara kafin nan suka shiga gida.
Wanka zainabu tafara tana gamawa abinci suka zauna ci daga nan sai hira har wajen 4 sadiya tana gidan su zainabu taga yadda Baba ke sangartata kwanon dataci abincin ma da kanta Baba ta d'auke ruwa ma da kanta ta kamata, tana bacci anaimata tausa.
Abba shidai kallo nasa idan yai magana tasace zatayi d'umi haka ya zuba ido.
har lokacin da Sadiya zata tafi Zainabu bata farka ba, gashi Baba "tace ba a tashin ta daga bacci haka tai sallama dasu ta tafi.
Zahra Iokacin datashigo ganin zainabu na bacci yasata zauna suka d'an tab'a hira duk akan MOHAMMED ne yayan su na Cyrus.
Oh zainabu kitashi wannan bacci haka saikace na mutuwa?.
Mutuwa kuma? saidai ke ki mutu marasa iya magana, tashi ni kiban waje kada kirsarmun 'ya.
Baba bafa wani abu nake nufi b a, kinga saici hanya basaikin tsaran magana ba uwar zance, narasa mai zainabu ta tsaremuku wallahi saimubar gidan nan.
haquri itadai Zahra take bayarwa, tasan Abban ta tsaf zai iya dukanta akan Baba shiyasa bama ta zuwa wajen ta sosai.
Zainabu dai babu abinda ya canja, canjawa d'aya ce karatun da take saikuma Mama tanaganin Gorman ta amma ko a islamiyyan da aka sakata kafin ta koma bata barin ta kwana koda malami ne.
Qaran ta kam Baba sanda tasamu sosai, dasu take kora mutane.
Makarantar kam, zuwan ta ba adadi akan me zasu doki zainabu?, Malamin "create yai Baba ta makara ne shiyasa.
Eh wato kasamu baiwa ko jaka, marainiya da ita amma kaimata dukan garada to kotu zata rabamu, mugu kawai danta makara a makaranta kai baka makara wajen sallah ko ka makara sahur?, dan cin zali.
Wannan rigimar Abba da qyar ya kasheta amma tundaga lokacin ta daina zuwa.
Masu aikin gidan dalilin zainabu saida aka koresu tofah?.
Abban kano "yace Umar anyi ba'ayi ba,nan ya zayyanomasa abinda ake ciki, Yaya nikam bazan iya cewa komai ba wallahi nakasa gano mafita saidai addu'a, aikam saidai ita.

Watarana, wani lokaci, wani yanayi,wani ikon Allah. Ayau su zainabu suna SS2.
Lokaci ne yaja haka du, da kuma ikon Allah,idan kaga zainabu bakace itace ba tayi wani girma da kyau ba fara bace amma tazama kamar wata halfcast dan kyau.
Kaf cikin school d'in babu wanda baisan PRETTY ba, da Cute Zahra,STYLISH da FEEDOH FOUR STARS kenan.
Sun gagari dukkan wata Prefects maiji da kanta, duk tsiyar ka saika sauko malamai kam suma saidai ashafa fatiha.
Vice shidai ido ne nasa, tunda Principal d'in da aka canja Umma Jegal Auntyn PRETTY ce kuma ita bata hanasu komai.

Autar Hajiya ce
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

         ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEIN

PAGE 24-26

Pretty wai ke sai yaushe zakiyi note d'in ki, kinsan dai halin Ma Azland ba mutunci tacika ba garama kibar wannan tunanin kidawo hanya.
Humm nifa wallahi bazan yi copying note tundaga first time ba, I know wallahi nabata amma shine zatace banbada ba kukan ku shaidane akan yanda nake note d'in Biology kaf zanen cikin book d'in wallahi ba wanda ban ba har yabamun take amma lokaci d'aya ace nakaimata tace baya nan.
Qarin haushi gaban juniors d'ina tamun 20 lashes, wallahi bazan yadda ba ba'amin na kyale.
Dole ta fuskanci itama hukunci wajen manyan ta.
Like how Pretty ai malami malami ne babu abinda za'amata wasa kike wallahi yarinya.
Feedoh kenan wallahi saina rama kuzuba ido kuga, bana yafiya bakuma zan fara akan ta ba, komai akamun saina rama saidai daga baya ayi afuwa duka.
Banda time d'in ku, guys let wear our sports clothes kada lokaci ya quremana yau table tennis zamuyi Allah nagaji da basket ball d'in nan.
Ok kutawo muje. Stylish ce "tace cute Zahra gaskiya Orange abu yanamiki kyau kinga yadda kika fito haryafi na prep yimiki kyau blue baicika amsar ki ba.
Nifa? Pretty ce tana magana tana juya bayan ta. Wow aike u ar d best my lady komai kyau yake miki tamkar ajikin ki aka yisu.
Wallahi kullum muka saka sainace haka, dan a tunani na wataran idan tana gudu sainaga wandon kamar zai tsage saboda.... Saboda me kinganki kunfiya sharri wallahi narasa mai boobs d'ina suka tsare muku amma zanfara shan lahaula.
Ke idan ana maganar saka shegun kaya baki saka baki wallahi Feedoh keda cute, uhum Allah yasa mubama jan under kawai sama mufita har tuqa tuqa ko wajen block.
Hee aikanku kuke fad'a masu.... Uwaki maqaryaciya kada kijamana jangwam, aikam rad'a taimusu ku duban idon Amsad akaina wallahi yarinyar can ta shiga uku tamaida mata kamar maza.
Hmm a kullum addu'ata d'ayace da Allah ya tsaremu daga fad'awa halaka amma 'yan les cikin block d'inan kamar tsamosu akai aka kawosu.
Kudai sai addu'a nifa qiri- qiri Sagas tamun tayin kanta tazata 'yar hannu ce kodan taga muna saka kayan da ranmu ke so ne? Kodan muna kwana gado d'aya, to mu we trust our self shiyasa muke kwana.
(Plx 'yan boarding adena shiga any how, hakan ke attracting masu son jikin ku akan ku kodan shaid'an ka tsarkake kanka dan Allah a gyara har ku 'yan universities masu zama cin camp, hakan is not good ko ga mace 'yar uwarka ba'ace kana nuna jikin kaba Allah yasa mudace).
Me ake jira ne?, babu mutafi to, oh STYLISH plx kinga pad d'ina akan loka d'auken yanzu saimu dawo muga anyi outing nata.
Pretty ido tabi pad d'in da shi, itakam sai yaushe ne zata fara mp?, I think their ix any kind of illnesses dake damu na ace kamar ni banfara mp ba to sai yaushe?
Pretty.... Agogon dake hannun ta ta nuna mata, basu qara komai ba sukai waje.
Acan suka sha table tennis nasu da guje guje duk da ana kaucewa juniors saboda rainin su.
Kee Feedoh zo ki rakani, inaa ? office mana kinga sunshiga meeting kuma 30 Minutes zasiyi so tawo dan Allah muje kada kiyi delaying d'ina.
Mts tawo kekinfiya naci wallahi  , ni nagode yi zaman ki basai kin rakani ba amma ni jiya na iya rakaki toilet 2am ba komi tanagama fad'a gaba tai.
Pretty tsaya gani kebakisan wasa ba?, wasa? mts basai kinrakani ba inada ido da qafa nasan hanya.
Wucewa tai da sauri ta aiwatar da qudiran ta ta fito batare da kowa yagan ta ba ko tarasa abinda taje nema.
Da daddare kaf students suna sanye da kayan su yau social nyt music zasu sha, oh su pretty sune kan gaba ba kunya suka baje jiki suna kwasar rawa juniors nasu ma hanasu sukayi.
Ss3 kuwa babu wanda yake shiga sabgar su dan yanzu zasu maka sharri ko su daukemaka abunda sukasan yanada amfani idan babu shi zaka doku ne ko tara.
Bazasu manta last year ba, wata khaleesat data zane su kuma tace su kalli rana na 20 Minutes bayan haka kuma aka zubar da kalkashi "tace kowa ta wuce.
Ramuwar da sukai tafi abinda sukai mata, dan saida suka bari akayi sabon cement sukaje suka saka sunan su da FOUR STARS.
Wata yarinya suka aika akan ta kirawo musu khaleest, aikam tsabar masifa khaleest da bulala tazo suna ganin ta suka fara kuka da ihu kankace me antaru dayake break aka fito so suna kusa da teachers da su mama lubei.
Abin haushi kam da gudu tabisu sukam kuka suke suna Aunty kiyi haquri wallahi bazamu qara ba.
Principal tana zuwa ihu tasaka, omg waye FOUR STARS da suka b'atan cement lallai sunga jidali kowacce saita kawo buhun cement cikin ku bayan punishment dazai biyo baya. Kuna inaaa?
Qarasawa gurin ta sukai suna kuka, pretty ce tai qarfin halin magana.
Ma nidai amaidani gida, haka kawai Aunty khaleesat tace muzo mu zana sunan mu nace a'a shine tace ko muyi kokuma idan munje Hostel taimana wanka da qaiqayi ma itace tasamu har mango da aka kwashe ita tace nakwaso mata.
Plensheet ma suna cikin lokar ta jiya tasaka wai dole saina samomata.
Wayyo khaleesat magana ma kasawa tai saboda shiga turiri.
A ranar akabata takardar sallama bayan an hukuntata..
Saidaga baya wasu sukaji sharri sukai mata, tundaga time en babu mai takuramusu.
Da gadara suke komai, wanki tsifa kaf juniors nasu ke musu.
One week later.
Shiru malamar Biology batashigo ba, kowa yai ready amma shiru, wata malama ce ta shigo tai musu da zata fita ne "tace afwaan class malama taje hutu sati biyu, lesson plan nata ta b'atar kuma a jiya akazo checking plan d'in daga ministry ganin batadashi yasaka akabata suspection na two weeks.
Feedoh Pretty ta kalla, anci sa'a itama ta kalleta murmushi tai tacigaba da abinda take.

Autar Hajiya ce
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

         ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEIN

PAGE 27-30

"Zainabu seriously me kika sani akan lesson plan d'in  Ma Axland?.
Bangane ba menasani kuwa, mts kinga Feedoh kada kimun shirme dan ba d'auka zanyi ba, kirabu dani kamar yadda nima narabu dake bansan hayaniya a ka.
Nice mai miki hayaniya?, banzan kallo pretty ta jefeta da shi tace  na fad'a da matsala ne?
Kudai Allah ya kyautamuku fad'a da girman ku, bakuyi kuna yara ba saida girma yazo kunban kunya aminan juna.
Stylish bazaki gane bane, ni matsa na wuce d'aki inada abin yi.
Fita tai ta barsu gun, hmm Feedoh me ya had'aku ne kinsan pretty wataran da zuciya kamar kuturwa jiyadda take wani fizgar kai ana magana.
Kyaleta Stylish akan fa kawai nace nagaji banrakata shikenan tad'auki zafi aje a haka.
Allah Ya daidaita amma abin kunya ne ace keda kuke aminai akan mu yau kune da fad'a?.
Hostel suka nufa suma, cute tana qara bawa Feedoh haquri akan taje su sasanta tunda itace tafaraiwa pretty.
******
  Time d'in da Pretty tashiga room nasu, yunwa dama ta dawo da ita, key ta d'akko zata d'ebi nama da bread,amma me?
Ba naman ba bread d'in gashi ankwashi wani gefe daga cikin kayan provisions d'in , tsalle tai ta dire.
"Masifa sabuwa wallahi yau sainaga wanda ya tsayawa wannan b'arauniyar arasa ma kwanar suwa za'ayi sata sai tamu tab
Fitowa tai gaban block nasu,tace kaf juniors su fito ayi layi, daga kan jss  har SS 2.
Ku me akeyi naga pretty tsaye anci d'amara?, yo wayasanar mata jarababbiya wannan qawar tamu A ce ba B ba, kyaji dashi idan kayana ne stylish "tace da Feedoh.
Yauwa cute plx kiramun 'yan SS1 na Orange house, su zo sumin checking kowanne bed da loko da saqo na kowa anmana sata.
Da sauri suka had'a baki sata pretty? Eh ansace kwanan naman mu ke kayadai da yawa ba madara Luna d'innan ba Milo ba All butter ban ma iya lilssafawa, amma waje guda aka kwashe.
Jaraba wallahi sai anfito da shi, Feedoh ina kud'in nan?, yana ciki, ohh maza duba. Ahayye babu su tab amma b'arauniya yau kinga ta kanki wallahi saikin yi danasani mara amfani.
Kowacce ta cire kayan ta abi layi, ku kuma ashiga kowacce kwana adubamin kaya ko key, dan alama ya nuna da key akayi using ba b'alleta kaiba.
Sannu suka fara checking jikin kowa babu, kan Umma suka tsaya itama sun dubuta har zata wuce pretty tace zo tana zuwa kuwa cewa tai d'aga wondon ki ki kuma yi qasa da pant naki.
Pretty mene haka? Saboda me zanwa kaina tsirara? ba tsirara zakiyi ba daga ciki zaki ja pant d'in. amma kafin nan ungodly, mari tabata tace pretty zallah bama Yaya koh? Saboda ke kece.
Announcement daga yau ni pretty nasoke Aunty pretty saidai Aunty ko Yaya banaso idan kunne yaji, jikin mu ya tsira suka amsa da qarfi.
Murmushi tai, a duniya tanason girma, hoo wani abu kuma sai anje SS3.
Juyowa tai tace bud'e nagani,
Allah ya kiyaye to ina Mp so kike pad ta fad'o kome?.
Stylish, cute da waccen baqar yarinyar kuzo nan tunda gardama zakiyi wallahi saina bud'e.
Ku riqeta plx, mene zakiyi? Idon matambayi. Janyo Umma sukai anan tafara tirjewa pretty ba kunya ta saka hannun ta saigashi ta ciro key qasan pant nata.
D'agawa tai tace gashi nagani mene haka banga kuma alamar Pastor yai miki sallama ba.
Ihu aka fara, Umma sai kuka tana roqon su suyi haquri, Inaa ai ba maganar haquri kije inda kika ajiye ki kwaso mana kayan mu B'a kawai.
Tafiya sukai, 10 Minutes nabaki pretty "tace.
Umma anji kunya, sata qiri qiri kuma kayan marasa haquri, habaici babu wanda ba'ayi mata ba baran da sukaga tafara shigowa da kaya habawa sai sowa da ihu.
FOUR STARS ne suka tsawatar da duk wadda taqara musu ihu aka sai ta kalli rana, sunsan hali ba shiri kowacce tai shiru wasu kuma suka fita.
Saidata gama kawo kayan suka b'ude tamaida kayan yadda suke, sannan suka sakata gaba sai sai village, anan sukasaka sakata hawan bishiya, kallon zomo wahala kala kala harsaida seniors sukace enough sannan suka kyale ta.
Duk bidirin tare suke, amma pretty bata kallon inda Feedoh take.
Kayan ta suka kwashe mata, a canja kwana yarinya amma wallahi bamu zama dake.
Kwana ta canja house dai, inji pretty dan idan tana gidan nan nikam saidai nabarshi. Kibarshi inji students d'in a'a Aunty saidai ita tabari B'a b'a atafi abi wani sarkin
  Fad'an Feedoh da Pretty har gaban vice da qyar ya sasanta, dan ita pretty ta d'auki zafi, tace ba ruwan ta da Feedoh da qyar aka sasan ta su.
*****
Waye haka yake lalubata, zanyi rashin mutunci fa, balai wace?, saboda jaraba to ba abokiyar ki bace pretty ce bari konamiki ihu.
Bakin ta taji an rufe saijim......., ai da sauri ta gantsaramasa cizo tafara agudu GARDI yazo GARDI ne kowa ta tashi, kafin kace me harya mik'e zai gudu pretty ta riqeshi jamaa kuzo gashi, akunna wuta nakamashi shege mugu azaalumi.
Nan da nan akafara dawowa, lailah Adamu Jumping ne duka suka sakamasa wasu harda bucket wasu takalmi ranar dai da qyar ya sha bayan anmasa jina jina da jiki.

Autar Hajiya

أم الزهراء
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

         ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEIN

PAGE 34-36


  Yammaci ne wajen irin qarfe 5:00 d'in nan na ranar Asabar ruwa ake kamar da bakin kwarya ga walqiya da tsawa da akeyi qarin wani abu kuma qanqara ce take zuba sosai.
Kowa kagani cikin makarantar kachako wasu wanki suke daga gefe wasu kuma shanya suke ba wanki ba.
FOUR STARS kuwa suna tsakiyar fili cikin farar vest da gajeran wando fari wadda suka bawa Mama lubei kud'i ta siyomusu iri d'aya a kasuwa.
Ga kitson su zane na hausa anmusu shuku manya da qanana ya zubo bayan su duka abinka da masu gashi baran ma pretty da nata yafi nasu yawa da tsoho, idan ka dube su bakace yaran hausawa bane sunfima kama da 'yan Ethiopia sak.
Tsakiyar filin Hostel nasu suke, da yake trazo ne ba qasa ba, a tsaye suke ruwa na dukan jikin su, sunayi suna hira da rawa da waqa abin su, Idan akayi tsawa da sauri suke hadewa gu guda daga nan sai su bushe dariya, sosai abin ke bawa kowa sha'awa masu kallon su.
Qanqara ce ta fad'o qatuwa kuwa, da sauri STYLISH ta je kafin tasaka hannu ta d'auka CUTE ZAHRA ta d'auke bakin ta zata kai PRETTY ta warce sainata bakin.
Feedoh kam hannu tasaka a bakin tanason kwacewa amma inaaa Pretty ta shanye, kanta suka hau suna dariya saikace yara.
Kwanciya sukai a qasa kowacce kanta na qasa suna hira qasa qasa, Pretty ce "tace guys anyi ba mu, kamar yah?, wallahi yadda muke d'innan ace da camera kusa musha selfie daba haka ba, amma ankwafsa kai abindai baiyi ba.
Wallahi haka ne 'yan uwa, amma da time, badai munkusa shiga ss ba, zamu buga show d'auri ma sai mun canja ba sani ba sabo wulaqanci zamu qaro, daga baya saimu saitu.
Hhhhh hakane fa pretty tamu, dole muyi suna ko a haka ma ansan FOUR STARS bare ace, kinzama head girl, nazama Labour prefect, CUTE ZAHRA tazama assistant head girl, STYLISH tazama Prep prefect wow ya abin zai zama ba dama.
Dariya suka saka, daga nan pretty ta kira wasu yara.
"Ku kuje kuce ina Basmah idan tace gata, kuce tabamu biscuits cikin loka da alewan madara, ok Aunty tana fad'a ta juya.
Inalillah yaran nan meyasameku?, amma dai hankalin ku kad'an ne kuga yadda...kafin Mama Lubei taqarasa tuni suka baibayeta suka rungumeta, jairai ku cikani zan jiqe, Mama Lubei aidama jiqewa muke so kiyi, oh ni Lubabatu Allah ya shirya ku, Ameen Maman mu.
Dama da tea da kin burgemu wallahi, da akwai kuwa yanzu na sauke zankaiwa Malamai bara nakamuku, yauwa Mama.
Cikin cup takamusu, itama yarinyar takamusu biscuits d'in, sunasha suna cin biscuits abinsu har ruwan ya d'auke duka aka kira sallah.
Tashi sukai sai wajen Mama. Mama da ruwan wanka? Oh da akwai to, yauwa bara muzo, kowacce towel ta d'auko suka kira yara su d'ebomusu ruwa na sirkawa, Mama dakanta ta zubamusu ruwan yaran suka kaimusu cikin toilets.
Da alwalar su suka tafi kaya kawai suka canja zuwa na bacci sai hijab suka tafi masjeed.
Basu bi takan abinci ba, dan sun qoshi yau kuma ba wasa ko da akwai ba club nasu bane 'yan ICT club ne da young farmers club suke rihazar.
Katifar su, suka yadda qasa sai bargon su dasuka ware hira dai bata qarewa dan yanzu ma ita suke duk kuma akan seniorities da zasuyi.
Pretty jikin ta ba dad'i daurewa take dai amma jikin nata tun tana wanka tafara jin yai weak, ci gaba sukai da hiran su har lokacin bacci yai sukai addu'a kowacce tafara baccin ta.
Wajen 2:30 na dare pretty ta farka sakamakon rawar d'ari datake, ga haqoran ta da suke had'ewa kaf kaf kaf.
Kuka take mara sauti kanta kuwa tamkar Dala da Goran Dutse aka d'oramata dan nauyi sai yada kai take gwanin tausayi.
Feedoh ce tai juyi, numfashi taji alamar dai bana lafiya ba, kasa kunne tai tabbas numfashi ne, torchlight ta kunna da sauri ta yaye bargon da suka rufa.
Pretty meke damun ki, ko cikin kine?, a'a tace, omg! to mene? Kai ta nuna mata, jikin ta ta janyo ta ayya pure blood sorry amma meyasaka baki tashen ba?, jijjigata tafara amma ciwon kamar qaruwa yai dan cewa take pure blood sanyi nakeji rufeni sai kuka
Bargon taja tare ta rufesu duka, tanayi tana shafa kanta tanaimata addu'a.
Su STYLISH ne suka farka, suma layi suka bi, wannan ta riqe hannu wannan ta riqe d'ayan hannun suma sai kuka.
Ruwa CUTE ZAHRA ta d'ebo addu'a tai ciki takafamata abaki , kad'an tasha ta kauce, Feedoh karb'ar cup d'in tai tasamata abaki dole tasakata shanyewa.
Ragowan ajikin ta suka shafamata, bata jima ba bacci ya d'ebe ta sukam kwana sukai akanta har gari ya waye.
Gashi yau Labour haka sukabar fara shirya kayan su har lokacin bata farka ba.
Ba ita ta farka ba sai wajen 12 time d'inma ankusa gamawa, sukam babu inda suka je suna wajen ta abincima kasa ci sukai.
Mama Lubei itama tazo ganin jikin nata.
Lokacin data farka jikin nata ba sauqi, dole tasaka akatafi da ita clinic kan sick bay aka d'orata, Allah yasa  Nurse d'in na nan agajin gaggawa tafara bata.
Drip ta d'auramata, sukam qawaye nan yini nan kwana abinci saida principal tai da gaske sannan suka ci.
Kwanan ta biyu taji sauqi, ruwan daya daketa ne, dama tana ciwon kai ta shiga ruwa kuma ya tashi.
Ga gefen cikin ta daya riqe shima, tadaiji sauqi amma duk da haka ran Thursday zataga Doctor tunda duk ranar yake zuwa.

Autar Hajiya

أم الزهراء
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

        ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEIN

          2017

PAGE  37-40

Allah sarki Pretty anji jiki,tai laushi sosai, rama kam ba'a magana saikace tai wata tana jinya.
Qawayen ta suma saida sukai ramar, sunzama so silent cikin school ko a kwanar su kagan su, shiru kake jin su.
Doctor yazo ya dubata, magani dai yaqarama mata sai kuma na ciwon cikin da take fama dashi shima yabata magani tundaga lokacin kam komai ya lafa jikin yafara kyau.
B'angaren MOHD kuwa, ya huta a gida tsawon sati biyu, daga nan yafara halartar asibiti.
Washe garin daya dawo, mahaifin sa ya kwashi takardun sa sai asibitin AKTH cikin ikon Allah take nan aka buga stamp cewa yazama staff shima.
Ranar Monday yafara zuwa, kafin ya fita saidayai addu'a da karatun sa, kana yasaka kayan sa qanana fa farin glass nasa cikin motar sa qiran Formatic ya shiga nan da addu'a ya shiga da kuma addu'ar kakar sa da iyayen sa na samun d'auka ka ya tafi.
Alhamdulillah ranar farkon sa baisami shiga office ba, zagaye yai da d'an abubuwa Lokacin tashi nayi yatafi gida.
Washe gari yakama talata shine ranar da aka bashi office nasa na kansa.
Komai complete akwai cikin office d'in da girman sa ya qayatu da pics na former leaders da kuma calender ta sassan jikin d'an Adam abindai sai ni dana gani, lol.
Wards d'insu daban dana Abban sa, Amma dai suna had'uwa sosai.
Cikin wata gudan da yayi cikin asibitin ba qaramar karb'uwa yai wajen jama'a ba, saboda kirkin sa da kula da patients wad'anda akayi admitting nasu, da visitors kuma.
Mata da dama sunsan Dr MOHD kodan guddumawar dayake basu ta ingata lafiyar su.
Gynecology ya karanta fannin mata ma yafi karkata wajen karatun sa, da yawa mataw nacikin matsala amma har yanzu ankasa magance musu matsalare datake damun su, shiyasa a yanzu daya sami dama yake baje tasa basiran da taimkon sa wa mata 'yan uwan Maman sa.
Yanzue haka zaune yake a office nasa. Kansa a sama idon sa rufe kome yake tunani oho?, nocking akai, idon ya saukar akan qofar, massenger ne yashigo, yallab'ai sufara shigowa naga lokaci yayi harya haura ma.
Ido ya zaro, agogon dake tsintsiyar hannun sa ya kalla, Ya ilah haka time yatafi afwaan dan Allah sufara shigowa.
Ok. Mata ne kowacce kaganta cikin shiga ta alfarma take wasu 'yammata wasu matan aure. D'aya bayan d'aya yake dubasu har Allah yasa suka qare kodaya tambayi massenger da saura?, yace babu miqewa yai, toilet ya shiga alwala ya fito da ita, kana ya wuce massallaci dan samin jam'in sallar Zuhr.
Ko daya idar ya dawo office, kansa ya dafe yana tausayawa mata sosai, gasu tsaf wasu mijin su yakasu wasu da kansu sukai driving suka zo,wasu kuma Napep suka hau dan zuwa samun lafiya.
Infection dai duk wacce tazo, har yanzu shine babbar matsalar Mata, kaga mace da kyan ta amma ina.... Infection yana neman maidata ba mace ba.
(Plx mata kowacce ta tashi dan bawa kanta kariya ga wannan cuta mai karya tattalin soyayya da qauna tsakanin matan aure da mazajen su.)
Wata tasan tana dashi, bata nemi magani ba, kizo kishafawa mijin, daga nan idan yaqaro aure shi yazo ya shafawa 'yar mutane, duk dalilin wa? Ke mana baki nemi magani tun wuri ba.
Kinsan kiyi wanka, ashafa humrah agyara baki, amma bazaki gyara inda nan shine alamar ki nazama mace ba.Dan Allah mata mu kula ko pant da pad kasan time d'in sasu da cire su badan komai ba, saidan lafiyar sa. Infection yanasaka cuta kala kala wasu ciwon kai wasu b'arin ciki gashi nan dai kunsani kuma.
Allah yasa mudace.
Kwazon sa da kuma ganin yes idan yabada magani ko yace ga yadda zakiyi ana samun waraka, yasa likitoci sukai meeting akan mezai hana yaringa ziyar tar Makarantun kwana suma ya taimaka musu da tasa baiwar wajen magance wasu matslolin da su yaran ke fama.
Sosai maganar tasami karb'uwa wajen kowa, Abban sa murna Allah yq azurtashi da yaro wanda duniya zata amfana da shi.
Cikin makarantu uku da aka ware "akace yaje yaga tsarin yaga wacce zataimasa da zai ringa zuwa.
GGSS Dala nan yafara zuwa, sosai makarantar taimasa amma kuma saiyaji baida hop akan ya d'auke ta, daga nan yatafi gezawa itama haka bai amsheta taba.
Kachako itace last, lokacin daya je, sosai tsarin makarantar tai masa, baran dayaga principal d'in Aunty Sadiya ta jegal 'yar uwar sace ga wasu dayasani ciki take yasaka hannu zai ringa zuwa duk Thursday insha Allah yanajin matsalar kowa.

  Tofa ga MOHD ga FOUR STARS shin zaisan su koko zaiyi abinda yakawoshi ne yatafi batare dayaga PRETTY ta FOUR STARS ba.

  Amsar nagareki AMMIN ZAHRA.

  Autar Hajiya ce.
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

         ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEIN

             2017

PAGE 41-43

"Oh pure blood kinji jiki, Allah sarki duk kin fad'a sai aukin nan.... Lailah Feedoh ta lalace ba ruwa na to, amma kuma twinny nafara murmurewa qashin yafara komawa gaskiya na wahala nazata ciwon cikin nan da nai MP zan fara har ina duba pant sainaji shiru.
Ayya soon zaki fara Insha Allah pure. Allah yasa kinsan ance duk wadda bata period bata haihuwa, nikam ko yaro guda Allah yaban inaso amma rashin haihuwa ba dad'i sai hawaye sharrr
Omg ke kinfiya shirme wayace miki haka?, da Allah duk bige ne keda zaki haifi 'yan goma.
Ni kuma?, Allah ban iya haihuwar 'yan biyu ma bare goma, to niwama nake so?.
Ke muma haka, Allah ni ba'a tab'a tsaidani ba, nima haka inji cute Zahra.
Nikam a tab'a stylish ta fad'a.
Yauwa guys ku zo muje ICT zanyi research cikin system, kai PRETTY ana hira zaki wani ce gaskiya mudai anjima aje.
To iya jaraba, naji kema haka.
Yau takama Thursday Doctor MOHD tun safe yai sallama da iyayen sa yakama hanya sai kachako.
Cikin baifie 1hour ya isa cikin harabar makarantar.
Office na principal yaje anan suka gaisa kana ya tashi da kanta ta gwadamsa office nasa d clinic d'in.
Ya yaba da tsarin amma dai da akwai abubuwan da za'a siya wasu kuma a canja.
Zama yai kan kujeran yana nazarin abubuwan rayuwa.
Principal Umma Sadiya ce da sauran malamai sukaje class by class akan idan kanajin wani ciwo da masu ciwon mara ko ma dai mene su fito.
To fa yara da manya kowa tafito, haka dai ta rabasu wasu sai next week wasu upper week ma.
Sannu yafara dubasu wasu ciwo suke ji kafin zuwan Menstruation wasu kuma sai yazo ya d'auke masifar.
Da yawa kuma, basayin two weeks da gamawa zai dawo, wasu yanamusu wasa kowcce da matsalar ta dai.
4:00 ya gama da kowa, kuma Alhamdulillah ya fuskanci yanayin ciwon su, qarancin magani shine yaja ma yakai 4, da bazai kai ba.
Kano yayo waya Bata inda nan ne Dila babba ta Drugs aka aikomasa da maganin.
Godiya suke d'aliban kansu bare malaman.
Oh wallahi tunda nake bantab'a ganin Doctor maikyau a sanyin hali irin wannan new Doctor d'in.
Wasu ne suke ta tad'in sa akwana ta biyu.
Mts ji b'ata Lokaci tunda jiya naji kowa ke tad'in wannan likitan kodai latse su yai shiyasa.
Ashaaa Fal yaqul khairaan, Au li yasmuut, baikace ki ba pretty ka kyautata zato nagari ga d'an uwan ka musulmi.
Haka ne fa, Astagfurullah. Yauwa koke fa.
Zahra da kinje kema wallahi, keda kike fama da ciwon qirji, abinda naketa tunani kenan My STYLISH amma bari wani satin yazo Insha Allah zanje.
Mts ni kutaimaka kusamo yara su wanke mana outing wears d'in mu kunga jibi excursion.
Haka ne fa, zadai mufita daga nan kuma sai masu candy suyi sai abawa FOUR STARS fili.
Yeaah wayaganmu  SS3, ai saimun canja tsari dole doka ta canja.
Haka ne Allah dai ya cikamana burin mu.
Ameen

******

  BAYAN CANDY
Doctor nazuwa makarantar sosai, taimako sosai yake, kirkin sa kaf ya karad'e school d'in.
FOUR STARS kuwa har yanzu basu had'u ba, har kawo yanzu da yau ake bada hutu wanda shine na qarshen zango ana dawowa changing classes

Autar Hajiya ce
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

     ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEIN

           2017

PAGE 44-46

12-8-2014 ake resuming kowacce makaranta ciki harda makarantun kwana wad'an da su tun 11 ga wata suka dawo.
Takama Monday kowanne d'alibi sauri yake yaje ya tsaya a filin assembly duk da ba doka amma zama a gaba shine zaisaka kaga duk abinda ke wakana a filin.
Lokacin da kowa ya hallara a wajen tsaf tsaf kowa yake dosuwar taurarin makarantar shiya maida hankalin yawancin d'alibai zuwa ga kallon su.
Uniform ne dai jikin su amma d'inkin jikin su dana hijab ya sha bambam dana sauran d'aliban kayan su sabbi yaci guga, ga takalman su cover shoes, ga faran safa kan nan yayi tum an qulle gashi tafiya suke a hankali suna d'an darawa kana suka qaraso sukabi layi.
Pretty ce ta fita, lokacin da aka sanar cewa wata ta fito ta bud'e taro da addu'a shine ita ta fita.
Annabi SAW tace aiwa salati, daga nan ta karanta sunayen Allah sannan aka shafa. National anthem akai da national pledge. Vice ne ya fito bayani yai akan dai andawo sabon zango yanayi ya sauya gashi nan dai kowa yasan bayanin Malamai wa students ranar farko.
Daga nan sai zab'ar masu muqami da makaranta zata na d'a abisa kula da sauran students.
Head girl ba kowa bace face zainab Umar nan aka kirata aka d'auramata assistant head girl Zahra Bukar, Labour prefect Fiddausi Jibo, sai Prep prefect Sadiya A Shehu sai sauran wad'anda makarantar ta zab'a.
Sowa aka saka daga nan kowacce tai bayanin sunan ta da class d'in da take.
Anan qarshen assembly d'in ya tsaya aka shiga classes.
Bayan aji FOUR STARS sukaje wayyo zokaga murna gurin su qarin dad'i prep prefect itace ta social night rawa da tsalle sukai daga nan akayi sabon d'aurin da suka tsara zasuyi suka shiga class.
A wajen break kowa yai yadda yaga dama, amma ana komawa kaf pretty ta tarkata sauran prefect d'in suka shiga classes dan basu sabon oder da suka saka.
Farko girmama nagaba dakai tilas.
Labour duk friday kowanne class zasu yi roster akan ga wanda sukai selecting wannan week d'in yayi, wani week d'in ma haka.
Andena fitowa da yawa, wasu basuyi sunacin bulus.
Yin break fast da lunch har dinner atsari za'ayi andena rubibi class by class za'ana fitowa.
Tuqa tuqa shima dole wanda ya riga ya d'iba.
Wanki indai ba laifi kaiba, to babu wanda zakayi wa.
Punishment shima laifin ka daidai punishment d'in ka.
Zagi ko harara ko gulma aka kamaka saika raina kanka.
Sata ko aka kamiki kunshiga toilet ku biyu, hoo babu kalar cin mutuncin da baza'a maka ba.
Kowa yayi na'am da wannan dokar dan juniors sunyi murna tsalle suka fara suna sai Aunty pretty Allah yaja daran Aunties d'in mu FOUR STARS.
Aji suma suka koma, farin ciki ba'a magana.
Tsarin da sukai na son rai d'aya ne shine, Indai suna balcony to fa babu mai wucewa kada a takuramusu wannan shine tsarin FOUR STARS dole abi kuma.
Su dai wanki za'a musu amma wani bazai bada ba. Kaji aikin manya.
Aikin FOUR STARS na tafiya daidai kullum kagan su fuskar su sake har yanzu basu kama wata da laifi ba sai abinda ba'a rasa ba.
******
Feedoh me kike jira ne anan?, hmm I just look something ne dayaban mamaki, mene?, wannan yarinyar nan mana last week tace kanta ke ciwo batayi kitso ba wanccen wanccen haka wannan ma wai batayi ba, tana magana like da sa'anta take yi anya ba raini.
Mts naci uwar ta, jata gefe wallahi sainaji uban waye akan ta da batayi ba. Aljanu ko me?, ninafi qarfin su saboda haka  cute Zahra jata gefe let us finish da wanda ke gaban mu.
Baya suka kaita ana gama assembly suka tafi inda aka ajiyeta
Basu tsaya komai ba pretty tasaka almaakashi kaf tasa suka riqeta taimata sol.
Yarinya basaiga tana bada haquri ba, ko sauraran ta basuyi ba suka shiga kitchen wake suka d'ebo.
Ungo jeki village ki yi kunya ashirin da hudu kuma wallahi a yau zaki gama idiot kawai dama rashin kunyar ta qarya ce.
Hoo anyi wanda suka fiki oya start kafin fad'uwar rana zaki gama

Autar Hajiya
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

        ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEIN

           2017/1438AH

PAGE 47-50

A tsaye suke a kanta tanayi tana kuka harta dena abin tausayi saidatayi kunya 24 d'in sannan suka matsa daga wajen.
Sallah anan sukai abinci nan sukaci, tana tsayawa bulala zataji a bayan ta.
Wanwar ta fad'i tana gamawa, ba suma taiba amma wahala iya wahala tasha ta ta kuma gane shayi ruwa ne koda yaji madara da milo.
Yara suka kirawo aka d'auketa sai block nasu tunda almost 7 o'clock a wajen tai musu.
FOUR STARS suka shiga room d'in su a gado suka zube tsabar gajiya gashi da prep yau amma inaa saidai wakilai badai su ba.
Zahra gyaramana shinfid'a mana bacci nakeji wallahi ma tashi ko wajen 2 ne amma yanzu nasan bazan moruba.
Tab wallahi kece da gyarawa yaushe rabon da ki gyara?, ni d'in to bazan gyara ba nan fa suka kama cece kuce.
Feedoh Itace "tace to tunda haka ne ayi kama kama, eh ayi to atare suke kama katifar suyar a qasa, bedsheet ma kama kama akayi suka shimfid'a.
Yauwa sai bacci, tana fad'a ta wad'a kan katifar, kut nice fa da gefe wallahi ni atsakiya, eh baku isa kubarni a gefe ba.
Kokawa suka fara wannan tayi na wannan tayi can dole dai akabar pretty a tsakiya Feedoh a qarshe.
****
Zahra waike bazakici abincin ba?, haba tun jiya fa kike qin cin abinci wani abu ke damun ki?, babu komai fa.
Ba komai, fine tunda kinqi muma bazamuci ba idan yaso yunwa ta kashemu duka.
Haba pretty bafa wani abu bane, cikina da qirji sune kemun ciwo sosai kamar ma zanji numfashina yana neman d'aukewa.
Wannan shine abin ba kamai ba?, kinga tashi kici abinci sai ki kwanta.
Allah banson cin komai, da dai da ruwan sanyi shi zansha, tana fad'a ta dafe cikin ta.osh STYLISH ruwa dan Allah kuban ruwa cikina zafi qirjina kuka tasaka.
Suma abinka da marasa qwarin zuciya sai sukabi sawun ta wajen kuka.
Feedoh "ce ta miqe wajen Mama Lubei taje ta karb'o ruwan da sanyin sa kuma, b'incine ledar tai suka sakamata ruwan a baki.
kurb'a d'aya biyu tai, daga nan taja doguwan ajiyar zuciya ta sume a wajen.
Ido suka bud'e maimakon su d'auke ta a'a saisukabi jikin ta sukafara kuka.
Wasu prefects ne, sukazo ciccib'arta sukai sai clinic.
Zahra dai anji jiki, dan kuwa ko numfashin kirki batayi haka ta kwana a clinic tareda 'yan uwan ta FOUR STARS wad'anda sukabi layi suna share hawaye.
Bacci b'arawo shine yai nasarar d'auke su amma badan sunso yi ba.
Safiya nayi wanka sukai da sallah, da class amma basuga ta zuwa ba, baqar duguwar riga suka zura sai mayafin ta da suka yafa sai clinic.
Har time d'in bata farka ba, zuru sukai ba uhum ba uhuuhm, Lokaci lokaci suna tab'ata kozata farka.
8:00 Dr ya shigo, suna gaisawa tai masa bayanin patein d'in da take clinic tun jiya.
Da sauri ya qaraso ciki, sallama yai kafin suka gaisa da nurse d'in wajen ta fita.
Wajen gadon yayi, anan yaga yammata uku sun kifa kai jikin gadon sai shesheqa datake tashi cikin clinic din.
Qamshin turaren da sukaji shine ya ankarar dasu suka d'aga kansu lokaci guda.
Miqewa Feedoh tai cikin kuka tace Doctor kaine koh?, kansa ya d'aga alamar eh.
Yauwa dan Allah kataimakamana ka duba Zahra tun jiya batajin dad'i tadena motsi doctor kai wani abu mana akai kaje.
Baigama yanke hukunci ba yaga wata cikin su ta so, stylish ce, itama roqon sa take akan yayi sauri ya dubamata My ZAHRA dan Allah.
Shikam atsaye yake yamakasa motsawa.
Pretty cikin dasassiyar murya itama ta miqe, Doctor tsaiwar me kake kazo ka dubamana jumping d'inmu hannun sa takama wani irin shock yaji tundaga kansa har 'yan yatsun sa.
Had'a ido sukai wani irin magnet ne yaji yana fuzgar sa akanta kallo ya bisu dashi na 'yan sakkani daga baya yafara aikin sa akan ta.

Autar Hajiya ce
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

        ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEIN

           2017/1438AH

PAGE 51-55

Dubata yai sosai bakomi ke damun taba, face unlcer itace tai mata mugun kamu, qarin abin kuma ruwan sanyin da tasha ne da batasha ba cuwon bazaiyi worse haka ba.
Nan dai yaimata allura yasakamata drip saikuma jiran farkawar ta.
Doctor ya bata tashi ba, My ZAHRA ki miqe zaki warke fa, stylish ce taje kusa da ita Feedoh ma haka.
Pretty ana gefe tamakasa magana sosai take qaunar FOUR STARS tanaji dama ciwon ya dawo jikin ta yabar na Zahra.
Enough plx kudena kuka zataji sauqi bafa ciwo ne me zafi b, wataqil ma ta tashi yanzu.
Da gaske Dr?, yes yanzu Insha Allah.
Hannu pretty ta d'aga danyiwa Allah godiya.
Duk abinda take idon sa na kanta
Gaba d'aya shifa ya shiga shoct, tabbas wannan itace zainabu 'yar Aunty Rahma dan ita kanta idan tai duba dashi zataga kamaannin dake tsakanin su.
Exactly ma itace, saboda kachako takeyi ga kamar Abban sannan a fuskar ta, lallai Allah yayi hallita ajikin wad'annan yaran duk kansu.
To ita zahran 'yar uwar suce ko qawaw?, bashida amsa sai nan gaba zama yai gaban kujeran da Zahra take hakan shikuma dama tabashi na qarewa zainabu kallo wallahi nidai nasami matar aure Alhamdulillah.
Zugum suke ba mai magana lokaci zuwa lokaci suna d'aga ido su kalli Zahra amma shiru ba alamar zata farka.
Can wajen 12 tafara motsi da sauri suka miqe Zahra bud'e idon ki kiga mune?, tar kuwa ta sauke su akan fuskar FOUR STARS.
Murmushi tai musu, ihu suka saka da sowa aka rungume juna dan farin ciki da annashuwa.
Shikam tashin da pretty tai a sace yabita da kallo baran ma da d'ankwalin ta ya zame gashin ta baqi Sid'ik ya bayyana a akanta da bayan ta.
Fatabarakallahu ahsanal khaliqeen, kalmar dayake furtawa kenan baimasan sun miqe ba wai zasu tafi da ita.
Baimusu magana ba saima Ido daya bisu da shi har suka fita dukkan su.
Kan gado suka sakata, brush tafara kai ranar Zahra taga gata batasan qaunar ta wa FOUR STARS tai nisa haka ba.
Dr kam shauqi ne yake binsa, alal haqiqa baida ra'ayin aure amma ganin zainabu one time yasaka shi yafara tunanin ajiye komai ya tunkari aure, koya huta da jarabar Baba.
Kafin ma ya fito saidatace masa, oh waikai MOHD bakada lafiya ne?, baigane maganar taba sai cewa da yai haba Baba lafiya ta lou me kika gani?
Aikam ba lafiya ba, ko aljana ta aure ka ko kuma bakada lafiya yaro budurwa ma bazaiyi ba, da sake dole naje Rano na amsomaka magani nagajie da ganin ka ba aure.
Dayake iyayen suna zaune dariya su maganar ma tabasu, shikam haushi yaji ya fito abinsa.
Dan ya gasgata maganar sa, Umma Sadiya ya tambaya takuma bashi amsa daidai, qarshe harda fad'an ta akan wani irin sakaci ne ace wa baisan qanwar sa ba?
Uzurin school ya kamata da kuma itama boarding school d'in da aka kawo ta.
******
Zahra jiki yai normal ankoma kuma fagen rashin m, dan a yanzu ma suna zaune qarqashin inuwar dirimi.
Ku wai ni ba marasa kunya ne a wannan year d'in naga bama deeling sosai ko dan bamu zagaya wa ne?, pretty nima maganar dana gama fad'a kenan jiya.
Hhhh sainaji inama su Aunty Sodangi, Aunty Shuwa, Aunty Benazir da sis Anee suna nan?, wayyo bar tunamin wallahi matuqa ina qaunar su ba ka d'an ba baran Aunty Rookei rayuwa gashi babu su, saimu akan matsayin su.
Kedai bari ina su khaleesat Sis Asy ma, wataqil sunyi aure, haka ne fa hiran su suke da tad'in su sai ganin wata yarinya sukai da bucket a hannun ta.
Kee zo?, da sauri taje ta tsuguna, me zakiyi?, wanki zanyi ok ayi lafiya.
yauwa ban gayamuku ba, ankawo wata sabuwa SS 2 naga kanta yana rawa sau uku ina hanata dukan yara wanki kuwa sau biyu nakamata tanabawa yara nai mata magana amma bansani ba ko taji?.
Kardai wata fara Zahra tace?, itafa kan masifa jiya a tuqa tuqa wallahi yara biyu ta mara akan sunce ance adena d'iban ruwa akai cikin Hostel kuma layi ake bi banyi aune ba naga ta zubamusu mari.
Mari pretty "tace cikin angry voice, mts amma shine kukai mata shiru?, kee me wanki zo, da gudu ta qara dawowa, wayabaki wanki?, ba kowa nawa ne.
Duk wannan kayan kine, kai ta kad'a, tsawa pretty taiwa yarinyar wadda hawaye har sun fara wanke mata fuska.
Nace waya baki, zan zane ki fa, wata ce tace nayi mata, idan nasake nace natane saita zaneni.
Good wace ita, SS2 take fara batajima a school d'in ba.
Itace pretty wallahi Feedoh kuzo muje nama yasamu, dariya suka fara anan suka tasa yarinyar a gaba aka tafi kwanar su.

Autar Hajiya ce
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

           ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEIN

    2017/1438AH

PAGE 56-60

Yellow house take nan yarinyar tai, tana gaba suna binta a baya har suka isa wajen da take.
Shimi ce a jikin ta, ta hakimce anaimata tsifar kai wata kuma naimata yankan farce kwaki take sha abinta.
Kanta suka tsaya takaici gaba d'aya kusan kashesu yai, su ba'a musu haka ba sai ita lallai.
Tana kula sa tsaiwar su amma kota d'aga ido saima harare harare data fara da tofar da miyau.
Zahra da zuciya, batasan lokacin da tasaka hannu ta kwace cup d'in kwakin ba tasha ramata akai kana ta ciri hannu ta zabgamata mari.
Da tsiwa ta miqe, ke wace ke wallahi bazan yadda ba, tunda kika maran saboda rainin hankali?.
Hannu ta d'aga zata rama marin Feedoh ta riqe tamaidamata nata kalar marin, tana ajiye marin Stylish ta d'ora nata.
Pretty kam kasa magana tai, tsabar mamaki eh da sake.
Yarinya ganin abinda akaimata yasaka tafara zage zage harda tsinuwa, oh dawa Allah ya had'asu kuwa bada ita ba.
Kaf prefects na makarantar ne suka shigo wajen hannun ta suka ja sai village.
Ba duka da hannu amma zagi dungure kai tsata miyau dundu hauri da qafa jan hancin ta da cire mata hijab babu wanda basuyi mata ba.
Feedoh tsabar haushi kamar tayi kuka, crolling suka sata tundaga gate har qofar blocks.
Taurin kai gareta, haquri ko na second batace suyi ba. Kneel down kam a ranar shita yini tanayi.
Safiya nayi aka kirata, up&up tai na 5 hours, gumi da gajiya kunsan ba magana, saidataga tana neman mutuwa kuma saitafara bada haquri, amma ina sukace basusan da haka ba.
Hawan gado stylish tasata, babu irin magiyar da bataimusu ba amma ko a jikin su.
Kwana 3 sukai ana bata wahala, ranar na hud'un yakama Labour hooo Feedoh ce kuma Labour prefect.
Wankin toilets kaf ita tayi, da daddare kuma oga pretty tace abat fage.
Dan Allah kuyi haquri kutaimaka wallahi bazan kuma ba, na tuba na biku, wallahi bazan qara ba, shi taketa fad'I Lokacin da aka aika kiranta.
Dariya tafara bawa wasu students d'in ma.
Koda shigo kwanar FOUR STARS  ihun ta qaruwa yai, me su pretty zasuyi ba dariya ba.
Haka suka ringaimata dariya kyakyakyakya, bending tayi tafara roqon su amma pretty d'aure fuska tai ta kalleta.
Tace kinga kincikan kunne da hayaniya, kama bakin ki, da sauri ta kama, good for u baby.
Kinga nuni taimata da qasan gado, oya maza kishiga ciki kimun kwai, ido ta zaro tace mezanyi?, kinji ai abinda nace kwai zaki sakan na kazar Hausa dana agwagwa saina jimina yi sauri na had'a wuta zan soya kona dafa.
Shiga maza mana, kuu ku rufeta taimana muci kuma zakuci?.
Eh Aunty zamuci wallahi to maza kusaka zani taimana.
Abin tausayi shiga tai sai kuka da majina hawaye ba qaqautawa.
FOUR STARS tana shiga ciki suka kwashe da dariya, Besty ina kikasamo wannan salon?, hh bakusani ba ai time d'in su Sodangi, naimata laifi saitace naje naimata kwai.
Ina shiga kuwa nasakarmata......kai amma kin iya.
Basubar yarinyar nan ba saida sukaji tana wani numfashi na wahala.
Tundaga lokacin kowa yaqara saituwa babu mai kace nace.
Kwana goma suka qara akaimusu hutu. Sai gida basuji dad'in hutun ba gani suke kamar bazasu dawo suga juna ba amma a haka dai suka tafi.
*******
Dr an shiga salon SO, har d'oki yake Thursday tai yatafi kachako, kodan yaga matar sa a cewar sa kwatsam saijin hutu yai anyimusu.
Baiyi baqin ciki ba, tunda gida zata dawo ma.
Baba ina wayata naiwa FOUR STARS waya nagaji da rashin su.
Rigace iya gwiwa a jikin ta, kunsan 'yan boarding ba kunya kowacce shiga yi ake a fita ko a zauna hakan take ga zainabu wayar Baba tabata bayan ta tajuya suna waya da Feedoh.
Shikuma lokacin ya shigo, da kuzarin sa ya shigo,amma cak ya tsaya ko ba'a gayamasa ba wallahi yasan zainabu ce.
Ya ilah itace juyowa tai tana wani irin murmushi mai qayatarwa ga wushiryar ta mai kyau.
Ido suka had'a dashi, da sauri ta koma d'aki tana tuna inama tasanshi?.
Bata tunaba cikin ta yai wata irin murdar'awa mai zafi, qara tasaki a wahalce jin qaran ta a d'aki bashiri shida Baba suka miqe sai d'akin a qasa suka ganta yashe tana riqe da ciki sai wash take had'e da qara da kiran sunan Baba.
Wajen ta yai zainabu! Zainabu me yasameki ba amsa Baba kam ta rikice sai kiran zainabu take amma takasa amsawa mutuwar Rahma itace tafara mata gizo.
Kafin ta farko ya rufamata wani zani daya gani, ya sunkuceta sai mota.

Autar Hajiya ce
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

          ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEIN

      2017/1438AH.

PAGE 61-65

Baba anga masifa, batasan lokacin data bazama ba, tafita da gudu tashiga motar sai asibitin. Gudu sosai yayi shiyasa sukai saurin kaiwa asibitin Baba kuka tasaka sosai gani take zainabu zata tafi tabarta ne.
Emergency yayi da ita cikin ta personal room yakaita, shida wata Doctor kwaiseh sune suke akan ta.
Ganin yakasa gano daga ina problem d'in yake, wani gado ya d'orata na'ura ya jonamata akan cikin ta wata a kanta nan da nan yagano komeye.
Ido ya zaro, cikin ransa yana jinjina ikon Allah.
Oh Allah mai hikima, ace mutum ya zauna da ciwo haka batare da yaimasa ciwo haka ba, kuma ita abin bai dameta ba.
(Kunsan pretty bata menstruation?, ashe wajen da jinin zaifita ne yake a toshe, yanzu haka ciwon da cikin yake mata jinin daya taru ne yai baqi harya daskare, shine yake juyawa sai wajen yanamata zafi).
Allurai yaimata daga nan ya jona wata na'ura ita d'umi ne da ita, yanasawa yana kallon computer ganin jinin yafara narkewa gakuma alluran sun fara aiki yasashi fita.
Baba yaiwa bayani, kije ki zauna wajen ta zanzo yanzu kilula da ita fa.
Naqi kaji yaro, ko uwar ta tanada rai bazata gayan kulawa da ita ba sai kai.
Pad yaje ya siyo da kaya sai panties dozen yakawowa Baba bayani yace Doctor kwaiseh taimata na yadda zata gyarata idan abin ya zubo.
Haka akai suna cikin maganar ma, tafara shure shure da kuka, can kuma saiga abin yafara zuba, bata tashi ba saida taji cikin ta ya saki.
Baba ta taimaka mata suka shiga toilet.
Wanka da canja kaya tayi, ta kuma gyara.
Bayani yadda Dr taimata shi tamaimaitawa zainabu ba qaramin murna tai ba kuma sai a yanzu tagane shi.
Ya MOHD ne shine likitan school nasu.
Maimakon taji tana qaunar sa, kawai jitai ta tsanesa har da taji alamar za'a shigo idon ta ta kulle.
Kwana tai a asibitin, Iyayen su sun godewa MOHD sosai Baba ma haka, ita a tunanin ta Zainabu na al'ada tuntuni ashe da cuta take zaune ba wanda yasani.
An salloma ta, aranar taiwa FOUR STARS albishir natafara ta gayamusu komai cewa wannan likitan yayan tane.
Haba wallahi naga kuna kama, kamar zanyi magana sainai shiru, Ikon Allah amma yanada kirki Allah yasa ma yace yana son ki.
Kut amma kun cucen, wallahi ni tun a school ma jinina bai had'u da nasa ba, ban gasgata ba sai yau dana qara jin ko muryar sa banson ji.
Kinsan had'uwar jini, ke pretty kiji tsoran Allah handsome guy kamar wannan Dr d'in?.
Feedoh wallahi banganin kyan sa, ke gata iyanzu muna school dama hutun 2 weeks ba hutu bane.
Wallahi kam muna komawa zasu fara maganat exam WEAC da NECO.
Haka ne kwanci tashi ba wuya *Ank'ure an kai Bango, Jam'iyyar mad'ora, Ank'ure ba'a damu ba* sunan candyn mu kenan.
*****
Dr dai yau yayiwa mahaifin sa maganar zainabu ya nuna cewa shifa yana ciki tana candy sai biki.
Sosai mahaifin sa yai murna, yakuma bashi goyan baya 100%.
Baba da Abban zainabu kamar ma sunfi kowa murna.Allahu akhbar Rahma tai auren zumunci ga 'yarta ma zatayi sosai sukai farin ciki.
Duk bidirin da ake zainabu bata sani ba, saima shirin komawa school datake.
MOHD dan ita yake shiga d'akin Baba yanzu amma saita b'oyewa ganin sa tai shigewar ta d'aki gaisuwa ka d'ai ke had'asu da shi harta koma.
A Satin aka kai kud'in aure da sa rana wata biyar Rano wajen iyayen su da kakanni.
yakama tana candy ta two weeks.
Ankoma school wannan karan karatu suka saka a gaba, ko social night sai sunajin rawa suke zuwa wasannin clubs kam sun aje gefe saidai wasu badai FOUR STARS ba.
MOHD duk ran Thursday sai yasaka ankiramasa pretty da qawayen ta wad'an da ya fuskanci aminan tane kuma batada kamar su.
Sosai suka saba dashi, anan yake ma gayamusu yanason qawar su amma ita bama ya gaban ta.
Sosai suka nunamasa zasuyi mata magana, saita soshi godiya yai musu.
Lokacin da suka sameta da maganar kaca kaca sukai, akan wata ta aureshi mana cikin su ita bata sha'awar auren zumunci kuma bashidaga cikin tsarin mazan da zata aura.
Sudai shuru sukai mata amma suna ganin wautar ta da rashin hankali, sunsan dai dole shita aura tunda yace musu ankai kud'i rabuwa da ita sukai.
Aka dena hiran sa, idan yazo saidai su suje amma ko gaisuwar ma ta dena.
Kwanci tashi Allah yaka lokacin da zasu fara jarrabawar WEAC kowa yashiga hankalin sa sai karatu zallah.

Autar Hajiya ce
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

          ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEIN

    2017/1438AH

PAGE 66-70

A yau suka fara WEAC ba zama, sai karatu zallah, lokaci na ja abubuwa na sauyawa hakan take ga FOUR STARS ganin sun kusa bankwana da makarantar yasa duk wani makaman yaqin su suka ajiye gefe.
Dama ba wani abu suke ba, sai ankama mara kunya shine suke fito da true colour nasu, amma idan babu suna shiga cikin juniors ayi hira da tatsuniya.
Mama Lubei tun kafin lokacin rabuwa yai tafara kewa tunda aka kafa makarantar take babu wanda ta tab'a shaquwa dasu sama da FOUR STARS group d'in Ank'ure ba'a damu ba.
Yaran sunada hankali da barkwanci sosai kuma suke mata biyayya dole tafara jin kewar su.
Suma sunzama silent ko a kwanar su suke, babu wannan hayaniyar irin ta da saidai su had'e kai wataran sukama hawaye ko kuma suyi jugum kowacce tana tuna idan suka rabu yazasuyi?.
Ga shi kuma kaf cikin su kowacce da kawo kud'in ta Feedoh da sa rana ma itada Pretty duk da bata sani ba.
Doctor kam babu abinda ya canja dangane da shariyar da pretty ke masa saima wadda ta qaru.
Yau aka gama WEAC. Wasu bazasuyi NECO ba hakan yasa suka fara tarkata kayan su dan komawa gida.
Kowacce saboda shaquwa kasa ganin tafiyar juna sukai, saidai bye bye da baya da sukai.
Tun daga wannan ranar suma FOUR STARS kowacce ta ajiye duk wani murna da da suke akan Allah yakawo candy.
Shikenan bamu ba qara kwana gado d'aya, bamu ba sake cin abinci tare, wasa da dariya a social night da rawa bamu, Feedoh dariyar da mukesha ranar Labour yanzu babu ita meyasaka ba'amana repeating ba muna SS2 sai kuka.
'Yan kwanar su wad'anda sukaga sukaji yadda suke magana sai kuka suma.
Yara da suka sami 'yanci wajen seniors d'in su suma kuka suke ahakan fa wai ba'a farama NECO ba amma ganin rabuwa tazo yasa suke kewar juna.
Pretty daga ranar da mukayi candy ni Bichi,ke Kano, Hajiyana Katsina, My ZAHRA Lagos sai kuka koni saida suka ban tausayi matuqa.
Kwana ki na tafiya rabuwa na qara matsowa jarrabawa kuma gobe.
Malamai kansu suna jimamin rabuwa da students irin FOUR STARS badan komai ba qoqari da hazaqa da barkwanci nasu.
FOUR STARS kayan su na loka da kayan sawar su da uniform kaf rabawa sukafara abinci saidai Hollandia ita vice yake saimusu shima kansa mamakin shaquwar su yake saiya tuno ranar da akawo kowacce tana kukan bazata zauna ba amma yau gashi wai basusan rabuwa.
  Doctor yana kula da rashin kuzarin su, da da hali dasaiyaje ya rarrashe su amma ba hali zainabu na tare dasu always.
  CANDY na 2014.
A yau ranar baqin ciki ce wajen su duk da ayau suka gama exam maimakon farin ciki sai baqin ciki kuka suke tun daren jiya Mama Lubei natayasu da d'alibai.
Anko na Green doguwar riga sukai sai d'an kwali fari takalmi fari, amma ita pretty Takalmin da Aunty Rookei tabata shi tasaka, ribboms na kanta wanda Aunty shuwa tabata ne d'an kwalin kanta fari ne saita d'ora wanda Adda Bena tabata ranar candyn su.
Cikin wawakeken filin makarantar su suke ga speakers dai kamar yadda akayi na su Aunty Sodangi shi aka maimaita a nasu.
Jakar kowacce da trolley nata na ajiye kusa da ita dama ba maganar kwalliya malamai ma kuka suke kodan shaftar FOUR STARS amma gashi yau zasuyi bankwana mai nisa da makarantar gaba d'aya.
Waqar da sukai ita aka buga kowacce da baitin ta.
Kaset d'in aka saka waqa tafafa.
GGUC kachakooo, Muna murnar candy..candy..murnar candy gaba d'aya munzo ending sai kuka.
Pretty ce ta janyo jakar ta Abban tane yazo d'aukan ta da Dr kaf suna gun suma hawayen tausayi suke subdawa.
Amshi.
GGUC kachako ce munata murnar candy gaba d'aya munzo ending.
Ni ZAINAB 'Ya ga Umaru pretty kuyi kirana nice head girl d'in ku bankwana nayi qawaye gaba d'aya munzo ending.
Fiddausi Jibo nake fa, Feedoh yar ficika ce, Labour prefect ce ni muqami mai qayatarwa Allah ya harhad'a kanmu gaba d'aya munzo ending.
Sadiya Abdullahi shehu, stylish kuyi kirana
Ni Zahra 'ya ga Abbakar cute Zahra ne sunana gaba d'aya munzo ending
Haka suma ragowan kowa tazo da baitin ta tanayi tana kuka.
Waqar qarshe itace wadda suke su ka d'ai hannun su rungume da juna suka fara.
Saimu na GC Kachako 'ya'ya gun Momy Sadee, 'yayan Mama Lubei, saimu vice uncle Sani.
-Bismillah Allah muzamufaraa 2014, Arrahmanu kabamu basira Allah 2014, domin muwaqe kachakoo lamarin ta yana burgemu soyayya ce mun nuna dole mu tallafa GC  kachako.
Zainab pretty ce ni kowa yasanni da sunan cikin FOUR STARS nake dole na jinjina GC kachako.
Saimu FOUR STARS aminan juna, 2014 pretty, Feedoh stylish cute Zahra ce 'yan candy muna muku bye bye yan uwa kutunamu cikin sallahr ku soyayya ce mun nuna saimu FOUR STARS Yaran vice.
-Allah kabarmu da duk 'yan kachako, kuma kabarmu da duk 'yan 14 soyayya ce mun nuna saimu FOUR STARS Yan kachako.
Suna gama fad'a ko kallon juna basuyi ba kowacce ta wuce motar da akazo d'aukan ta tana kuka.
Mama Lubei itama da gudu ta  koma cikin kitchen.

Autar Hajiya ce.
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

      ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEIN

    2017/1438AH

PAGE 71-75

Anyi candy lafiya kowa taje gida cikin salama.
Baba murna Allah yadamata da jikar ta har liyafa aka had'amata amma agunta batayi dad'i ba tunda babu FOUR STARS.
Kullum kaga pretty to da waya take ba komai suke ba illa musanyan pics da hira ji suke dama su koma ko su had'u guda.
Zahra anashan hiran school itada Baba.
Mama ma anabata labarin school wataran haka kawai zatayi hawaye na tunanin school.
Andai yi candy angama anmuku fara sabawa da gida, cikin satin ne Abba suka kirata akan maganar auren ta wanda ya taso dan a satin gaba za'a fara rabon card.
Duk abinda aka shirya da FOUR STARS ake Zahra qanwar sa tashiga cikin su Dr kuwa da kansa yaje ya tawo da su Feedoh sai ganin su pretty tai kwatsam dukkan su kuma.
Da daddare suna zaune abinci suke ci mamakin zuwan su take tadai share kawai.
Pretty naji Kamar Abba na kiranki?, eh nima naji bara naje ina zuwa ok yammata amaryar gobe.
Juyowa tai baki ta tab'e tai gaba.
Yauwa zainabu zo mana, gani Abba Alhamdulillah mungode Allah mai kowa da komai dan kuwa yaimana abinda muke so akan ki.
Duk kyan mace da gwallin ta, da taqamar ta, da ilimin ta da dukiyar ta d'akin mijin ta shine gatan ta.
Kasamawa yaran ka uba nagari shine cinyewar aure, wallahi zainabu ina alfahari dake baran ranar candyn ku yadda naga kowa yana yabon ku da fad'in kyakyawar kalma akanku.
Bamu muka had'a ba, Allah ne ya qulla d'an uwanki MOHD yaganki yanaso kuma mun amsa bikin ki nan da sati biyu ina fatan zakimana biyayya?.
Lefen ki akwatu goma sha biyu suna nan ankawo ankai can Rano sungani yanzu suna d'akina.
Zainabu ya kika CE?.
Abba nizakuyiwa aure?, da Ya MOHD Wallahi banso daga gama makaranta ta ko hutawa banyi ba tabbas saiyau nasan ba'a sona dan mama na ta mutu?.
Tashi tayi da gudu sai wajen Baba nan ta fad'a kanta.
Baba nashiga uku auren dole zasu min wallahi nibana so nashiga uku.
Kee dan uban ki yimun shiru wallahi zan zaneki, dama har yanzu rashin mutunci yana nan baki dena ba dama ba'a yabon d'an kuturu saiya shekara da yatsa halin ki yana nan.
Ai MOHD taimaka miki zaiyi dazai aureki shashasha mara kamun kai.
Umar zagin ya isa, tunda bataso baza'ayi ba yi shiru abinki zainabu babu mai maki auen dole.
Tabbas kuwa Aliyu tunda bataso bazaayi ba.
Nikuma indai nina haifi zainabu batada miji sai MOHD idan ba haka ba wallahi na yafewa duniya ita.
Ashsha Umar ba'a haka, yaya nariga nagama magana biki ba fashi sai anyi mara mutunci hannun d'an uwan sa yakama suka fita.
Kiyi haquri zainabu kinji abunda baban ki yace koh banda ta cewa umar yai fushi banda abinki babu makusa jikin MOHD ai.
FOUR STARS kam tatas sukai mata ranar taga duhu.
Mama itama cewa tai a kyale zainabu tunda bataso Abba yace inaa ai dole ba fashi idan yaso ta kashe kanta.
  Tunda akayi haka, tadena shiga harkar kowa har Zahra ma Baba kawai da Abba sai Mama take kulawa amma su Feedoh ma fushi ake dasu, bare uban gayyar.
Rabon IV ya kankama dan har katsina, Bauchi Lagos Maiduguri saida sukaje dan kaiwa seniors d'in su.
Amarya da qyar tabari akayi gyaran jiki fushi take sosai amma zuwan su Sodangi da kuma Adda da Rookie kax saita ware.
Fad'a sukai mata akan yadda sukaga tayi, shuwa harda tsaraba gaskiya sunyi qoqari, guddumawa tasamu sosai FOUR STARS Kowacce 20k tabata.
D'inkin Amarya ango dasu Feedoh sune suke jele mai qunshi ma takanas aka d'akko ta tazanawa amarya jan lalle wanda yaji kayan qamshi da komai.
Cikin Biki.
  Amarya sosai ta zuba kyau kamu a gida akayi, Alkyabba tasaka Bjay tazo ta zanemata fuskar ta da kwalliya.
Baba sai buduri ana auren 'ya kuma jika sai shaani.
Abba da qyar ya haqura yadena fushi.
A Meena akayi dinner wadda tasamu halartar manyan likitoci da manyan qusoshin gwamnati.
Mama Lubei da principal Umma Sadee kaf sunzo ranar anyi shagali.
Ango da amarya sun fito sak, dama gasu kamar su d'aya sai suka qayata wajen.
Yau Asabar itace Ranar d'aurin aure wanda akayi a masallacin Malam Isyaka Rabiu akan sadaki dubu Hamsin.
Anyi walima ta angwaye da daddare aka qara wata dinner.
Safiya nayi Mama da Baba da Aunty Amina matar Abban ta sukai yini.
Yanzu kansu a had'e yake tunda zainabu ta girma ba B'arna.
4:00 amarya tai wanka fuskar nan cukus ba faraa dama ta dole ce wadda take a baya dan kada a gane yanzu kam kuka ma tafara a haka aka shigar da ita wajen su Abba.

Autar Hajiya ce
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

       ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEIN

      2017/1438AH

PAGE 76-80

Zainabu dan Allah kiyi biyyaya ga mijin ki, ki kyautata masa kizama mace tagari da mijin ki kodan kisamu aljanna madawwamiya.
Abban tane shida Abban kano da Baba dasu Aunty Amina suke mata fad'an.
Itakam ko ajikin ta wallahi bazata zauna ba saiya saketa tunda ya aure ta dole ai batace tana sonsa ba.
Kukan datake bana komai ba saina rashin Baba kusa.
Haka aka shigar da ita motor tareda rakiyar qawayen ta FOUR STARS dasu Sodangi, Shuwa, Bena, Rookie Mama Lubei da yawa cikin 'yan school d'in su sunzo mata sunmata guddumawa sosai wasu da yaran su ma, amma a haka suka zo suka kwana kuma.
Gidan ta a gwammaja yake gida mai kyau basaina gayamuku komai ba , amma dai babu ce bangani ba kawai cikin gidan amma akwai komai na more rayuwa.
Nasiha suka qarai mata, daga nan aka maida kowa gida FOUR STARS ne kawai suka zauna suma kukan suke tayata na rashin ta da sukai duk da suma bikin su baifi wata ba, Feedoh ita wani week d'in ne ma.
Tsayuwar motar angwaye sukaji da sauri suka gyarata aka qara saka turare a d'akin da parlour.
Basu zauna cikin bedroom d'in ba, parlour suka dawo itakam sai cika take tana batsewa.
A haka suka shigo, barkwanci aka d'anyi sai addu'a data biyo baya da nasiha duk dai akan zama lafiya da girmama juna.
Miqewa sukai zasu tafi, FOUR STARS ma suka miqe, nan suka ringume juna aka saki sabon kuka da qyar suka tafi itakam d'aki tai shigewar ta tasaka sakata.
Baibi takan taba, saidayai alwala da wanka yazo mata sallama yaji a rufe yasan a rina dama.
Ko da safe gaisuwa kawai ta had'asu sai a dining da aka aikomusu da break.
Dr yarasa mai yaiwa Pretty datake nuna masa tsana haka, shi wani abu na rashin dad'i bai tab'a had'asu ba, yasan kuma batada wanda take so amma akwai time.
A ranar 'yan uwa da qawayen ta suka koma duk sunzo mata sallama.
FOUR STARS ma da yamma suka zo, hira ma kasawa sukai dan gaba d'aya rayuwar school ita suke tunawa.
Tabbas badan aure ba babu abinda zai rabasu da juna.
Cute Zahra, stylish, Feedoh babu wanda bai zubda hawaye ba sosai lokacin da zasu tafi fad'a da nasiha babu irin wadda basuyi mata ba.
Sun nunamata aure dai ba abin wasa bane, idan ta kinji kanki mudai mun fita zamu kuma ringa tambayar sa kincanja ko kuwa.
Kowacce motar gidan su itace tazo d'aukan ta, Zahra Enllemn zata ba lagos ba.
Kuka dai baya qarewa, dama bamu gama school ba, wallahi haka nima nakeji inji pretty.
Amarya dai kowa ya watse anbaarta da halin ta da mijin ta.
Kowa sabgar gaban sa yake babu mai shiga ta kowa, ko ya shiga tata bata kulashi shiyasa shima yadena kulata abinci ta iya sosai wataran tayi wataran taqi.
Ga bikin Feedoh yazo dama tsiran sati d'aya ne to sai aka qara yazama sati uku na stylish kuma wata guda.
Batagyamasa bikin ba, saishine yaimata magana akan ta shirya gobe zai kaita, batawani yi d'okin komai a gaban saba saima murgud'amasa baki da tayi.
Shi dariya abinta ke bashi ma.
D'aki ta shiga sai murna nan da nan ta had'a kayan ta washe gari sai katsina.
Itama Feedoh anyi biki ankuma kaita Abuja amma zasu dawo kano.
Sun qara had'uwa yadda suke da Dr Kamar ba komai tsakanin su shiyasa basiyi wani binciken yimata fad'a akan ta gyara ba.
****
  Sunje gida Baba murna yauga zainabu, sunsha yawo har Rano yakaita bawan Allah.
Bikin stylish anyi shima Zahra ce da saura kano aka kawota zumunci qulluwa yake taqarayi abinsu.
Bayan wata uku.
Ba canji,akan yadda take masa saima yanzu taita shiga ta English wears zama da towel duk wata hanya datasan zata tsokanoshi saitayi.
Allah sarki bawan Allah tun baijin komai harya dawo yana kwana da pillow akan ciki.
Yau tun safe ta tashi abakin qofar kitchen ta zauna jiran sa take, haka kawai wallahi nagaji da saidai kullum kakaini unguwa yau kafito ayi taqare dole ayi wani abu.

Autar Hajiya ce
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

     ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEIN

    2017/1438AH

PAGE 81-85

A'a My precious yau bakijin bacci kenan?, eh banaji magana nazo muyi ta qare kaji.
Toh gani nazo amma ba ko ina kwana?
Au ina kwana katashi lafiya ya kwanan kai d'aya ya rungumar pillow?.
Dariya tabashi sosai hakan yasa ya dara, duka lafiya lou amma kema naga kwanan kike ke d'aya?.
Eh aibance ina kwana da wani ba.
To me matata ke so agareni hartake nemana?.
Bafa wani abu bane kawai inason nafara driving da kaina nagaji da kaini da kake ga Feedoh itama ansiyamata.
Shikenan abinda kike so? Eh to angama yanzu kishirya muje ki zab'a.
Da gaske? Eh mana. Wow batasan time d'in data tashi ba ta rumgume shi tnq Yaya amma kanada kirki wow really appreciate kai amma naji dad'i.
Pecks tamaishi a kumatu da hancin sa tamanta da wa datake zaman ta tai kan cinyar sa tace Yaya to wa zai koyan?
bagani ba aikin me nake weekend sai muna training koh?eh yaya amma fa a hankali zakana koyan, Insha Allah a hankali kuwa ya za'ayi nayi hanzari da wadda ko mai sunanta naji raina sanyi nake.
hararen sa tai "tace koh humm ni matsa nasaka kayana muje kadafa kaga wai... Nidai basaikin mun rashin kunya ba jeki kishirya, konazao natayaki? bara jaki yai qaho.
Haka kikace eh, da sauri ya mik'e ya kamota abinda bai tab'ayi ba itama haka shiyafara mata. kwace kanta takeson yi amma ina takasa dole ta saduda su pretty an yamutsa saidayaga itakanta ta kamu sannan ya kyale ta.
Yawu ta zubamasa mugu azzalumi menaimaka zaka zuban miyaun ka.
Wallahi bazan yadda ba, au ramawa zakiyi to zo rama abinda naimiki.
Hhhhh hauka manya, maimakon ta rabu dashi saitaje wai zata rama aikam ta ramo dan bai saurara ba dama irin haka yake so sai yau Allah yabada dama.
cikani mugu waikai bakada zuciya ancemaka dan wani abu nace zan rama?.
Badan haka ba My precious.
To cikani idan kuma baka siya ne sainaji?, ni zan siyamiki mana yi sauri nima nai sauri ariga fitowa.
Da dariya tace saina riga ka wallahi, da gaske murgud'amasa baki tai da da wasa tana fad'a ta shiga d'akin ta.
Gudu gudu tai wanka simple make up taiwa fuskar ta , kana takawo lace maroon da mayafi milk da takalmi tasa sai wayoyin ta data d'iba.
Kicib'us sukai da shi zai shigo, lalala mene haka kaban ajiya ne da zaka shigon d'aki last warning kada ka qara ban fara son ka bare kace zaka mun shishishigi ba kuma zan soka ba mts.
Tabbas yaji haushi amma haka ya kanne ya juya bayan sa ta biyo shi tana mita.
Gaba ya bud'emata maimakon ta shiga saita bud'e baya bai hanata ba illa shiga shima da yayi yaja motar sa.
Wajen saida motocin suka nufa, tun daga gate tafara hangar motoci masu kyau sosai.
Suna tsayawa ta fito abinta, tawo muje koh?, basaika gayan ba zan bika ai inada ido, nasan kinada idon nace kizo.
Haka suka qarasa office d'in director d'in, gaisawa sukai sosai bayan ya nuna musu kujera ta zama.
Yauwa Alhaji Mota muke so mai kyau ko zamuje saita zab'a? Eh maizai hana kutawo.
Gaba d'aya idon ta ya rufe takasa zab'a ma, daga ta kalli waccen saita kalli waccen, daga can ta marairaice murya "yaya ka zab'amun nakasa amma mai kyau kaji? Anya Judaism zab'a da kanki zanta rakaki har kiga daidai da zab'in ki.
Haka akai kuwa, a tsakiya taga wata GMC da LEXUS kaf Ash colours ne bayan sa ta matsa a kunne tarad'amasa Yaya kaga wasu can sunyi kyau koh?, juyowa yai ido ya zubamata na 'yan sakanni daga baya yace to wacce kika d'auka cikin su?.
k'afa takama diddirawa a qasa nidai yaya Allah bansani wacce zan d'auka ba kazab'an kawai.
To Alhaji duka biyun zamu siya ido Alhajin yazaro! Kai kasan kuwa kud'in su? Ko nawa ne kagayan amma da service d'in su dai?.
Alhaji komai ma akwai ga bonus na petroleum ga wanda ya siya.
Nan yagayamasa kud'in take ya bud'e booth ya bashi cikon 500,000k ne yace masa yabashi POX nan yabashi yakwa ciro masa kudi'in su.
Ita mamakin sa take dama yanada kud'i kodai d'an qarya ne to ai banga alama ba.
My precious tunanin me kike tawo mutafi yanzu zasu biyomu gida da ita, a farfajiyar gate saina koyamiki koh? Eh yaya angode. Shhh hannu yasa a bakin ta babu godiya tsakanin mu, tarkata tawa sukai sai gida.
Wajen koyawar ma saida tasai da hali, ni kabarni haka ake kace wani saika zauna saina zauna inama ake zama mutum biyu cikin one sitter kuma kana baya ina gaba?.
Bakiso kenan amma idan ba haka ba ya za'ayi na koyamiki tawo inada abinyi.
Dole taje ahaka ya koyamata na ranar.
Motar d'aya tasace d'aya tata, amma yace ta ringa d'auka tunda tanaso.
BAYAN SATI UKU.
  Cikin satin ta kware sosai, babu ma L gaban motar ta, wata sabuwa kuma fita ba time baran da Feedoh suka dawo Kano badai dindin ba, amma kano nan mijin yake yanakuma neman transfer yakoma kano da zama.
Yayi yayi ta dena amma taqi, Feedoh ma fad'a take mata akan yawo amma bataji ba.
Zaman su kadaran kadahan, chat shine aikin ta abincin ma ba sosai takeyi ba.
Bai tab'a fushi ba saima komai idan tayi kyau yake masa a idon sa.
Yaukam tana gida tun safe shima yana gida sai zirga zirga take abin ta ko kulashi batai ba.
Can ne daya gaji "yace "zainabu Allah yabaki lafiya da hankali.
Murmushi tai "tace yaya bara nazo naji me kace.
Cinyar sa ta hau, Yaya kace banda hankali eh mana bakidashi zainabu.
Amma idan kinada shi gayan mene aure.

Autar Hajiya ce
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

      ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEIN

  2017/1438AH

PAGE 86-87

Aure yaya tana magana irin ta shagwabbabun yara.
Hmm aure shine kasami miji nagari Kamar ni danayi dacen miji maisona yanamun komai nake so.
Aure shine kayi girki abinci kayi kwalliya tafiya shopping zuwa cinema kallo, saka maka recharge cikin waya aishine aure ko ba haka ba My king? tana magana tana kad'a ido hannun ta na zagaye na wuyan sa.
Murmushi yayi mata yace tabbas bakiyi qarya ba, amma baki fad'i ginshiqin auren ba wanda yanzu zaki ganshi yarinya.
Baijira cewar taba ya sab'ata a kafad'a  sai Gadon aba'i.
Wayyo pretty taga qaryan rashin kunya, taga qaryan shagwaba dan MOHD A wannan ranar saidaya ququta ya maidata cikkakiyar mace.
A yau MOHD jinsa yake tamkar babu wanda yakaishi farin ciki, albarka kam babu wadda batasha ba.
Wanka da kansa yaimata itakam banda kuka da Allah ya isa babu abinda take masa, hawaye yaqi tsayawa a idon ta tunanin ta ya tsaya cak.
Banda ciwo babu abinda jikin ta yake magani ma yakamata yanzu amma ko kallo bai isheta ba.
Tundaga wannan ranar ta tsiri rashin kunya da yawon ta.
Baba kuwa koda yakaiimata qara fad'a da zagi ya rabasu aidama bataso dole akaimata zainabu yi yadda kike so idan yagaji yamaidomin dake gida nima ina buqatar ki.
Maman sa tasan komai amma batada yadda zatayi, Zahra qanwar a kuwa fad'a sukai kaca kaca akan abinda takewa Yayan ta.
Duk budurin da suke basudaw masaniya.
Yaukam taci alwashin wallahi saiya saketa tagaji da zaman gidan, itadai qaunar sace batayi badan yamata wani abu ba.
Kwatsam Zahra takamata bikin ta kwanan ta uku ta koma dole ta ajiye komai har sai angama biki.
Bayan sati biyu.
Wankan ta tayi tasaka kaya na alfarma abinci tai mai kyau wanda rabon da tayi harta manta .
Ganin haka yasaka shi murna da karsashin sa ya zauna yafara kwasar girki saidaya gama tas sannan ta buqaci yazo magana nakeson yi dakai.
Gyara zama yai ya fuskan ceta sosai..
Yaya tambayar ka zanyi

Autar Hajiya ce
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

      ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEIN

    2017/1438AH

PAGE 88-92

Hmm Yaya namaka wata tambaya?, ina jinki pretty Allah yasa nasani, eh to kasani tana magana kanta na sama.
Kace kana sona?, tabbas Allah kuma shaida. Fine.
Duk abinda nake so kanason shi?, kwarai kuwa, kome nakeso zakamun?.
Haqqun matuqar bai sab'awa addina naba da Shari'a ba, zanmiki da jikina da aljihuna idan zan nemi taimakon wani ma zan nema dan na faranta miki.
Murmushi tai tana tafa hannu, daga can ta sara masa alamar jinjina.Baravo baban soyayya.
Inaso kamun alqawari tsakanin ka da Allah inaso kuma kayi dan iqirarin da kake cewa kana sona.
Pretty be straight forward mana, kifito frankly kigayan ko mene.
Nidai kafara d'aukan alqawarin cewa zakamun, nayi to Allah kuma yaban ikon cikamiki shi, Ameen.
Takarda ta miqa masa da biro, pretty what should I do with dis paper?, eh inaso KA SAKE NI?, da sauri ya miqe yana zare ido, SAKI kuma noo! Pretty i can't u know I LOVE you fa, u ar my hrt design, I will never do with out u i really love u pretty, plx kada kimun wannan horan zan iya zama dake haka duk da nasan baki sona.
Miqewa tai itama"tace oho alqawari ka d'auka, kuma kenan duk zancen kana sona dama qarya ne?.
A'a inason ki mana, to kayi abinda nace indai kana sona.
Naji zanyi amma kema saikinmun wata alfarma guda kema zan miki, kinsan zan iya kaffara nai azumi uku akan haka?, nasani to bazan yi ba matuqar kema kin cika naki alqawarin.
Mene shi?, inason yau d'aya kiban haqqi na ki farantan sosai kamar dama can kina sona.
Ki ban farin cikin da miji ke samu wajen matar sa na awowi ka d'an idan kikai min haka tabbas zancikamiki alqawarin ki.
Bravo amma kafin nan fara rubutan kaban a hannu sai komai ya biyo baya.
Ashsha! Pretty ai idan namiji yasaki mace to babu abinda yai saura a tsakanin su, katuwar katanga ce tashiga tsakiyar su.
Hannun sa yasaka yakama nata, a hankali yake murzawa yana yaba kyan jan lallen dake 'yan yatsun ta.
Pretty waiting ooo, naji na yadda indai kaima zaka cika zan cika.
Wallahi narantse da wanda yai saman bakwai da qassai bakwai, wanda ya hallici Anabin farko dana qarshe ni MOHD zan cikamiki burin ki.
Ok na yadda, baijira komai ba y sunkuce ta sama sai OGA BEDROOM.
MOHD soyayyar daya jima yana qissimawa tun farkon zaman sa matured, tanadin dayake akan so tattali kulawa da bajin ta ayau kaf shi yaiwa Pretty yanajin sa tamkar wanda sukai hannun riga da tashin hankali.
Ga pretty ma haka yake, soyayyar da suke tad'in zasuyiwa mazajen su, kulawar da zasu basu, yau itama batasan Lokacin data fara zubawa MOHD ba.
Jin su suke wata duniya daban, suka d'ai ba iyayen saka ido irin su......
Bayan kamalluwar komai cikin nishad'i da annashuwa MOHD ya miqe toilet ya shiga baijima ya fito, towel ya d'aura baibi takan taba illa kautar da kansa da yai ya fice.
D'akin sa ya shiga, kan gado ya zauna, baisan Lokacin daya fashe da kuka ba, me yaiwa zainabu da zafi haka take gwadamasa qiyayya haka?, a yau yanda yaji yadda matar sa take sosai dabaimata alqawari ba wallahi ko bakin bindiga bazaisaka shi ya saki zainabu ba, amma yasan komai muqaddari ne daga Jallah, idan da sauran zaman su toh? Idan babu... Da sauri ya rufe bakin sa.
A b'angaren pretty ma, tabbas soyayyar MOHD taimata irin kulawa da tattalin datake burin samu kenan.
Tanason harkar turai wato kiss da romance, gashi kuma MOHD expert ne a wajen sau biyu suka tab'a kasancewa amma ta fusknci haka tun ana farko.
Tashi itama tai, wanka tai kodata fito, gyara jikin ta tai da mayuka masu qamshi kanta hand drayer tasamasa dan yai saurin bushewa.
Kayan ta already dama ta had'a sai abinda ba'a rasa ba.
Janyo trolley d'in tai, kicib'us tai da shi zai shigo ita kuma zata fita.
Pretty kin fito? Eh tace masa, hawaye ya goge baibari sun had'a ido ba ya danqamata takardar ta a hannu da sauri ya shige d'aki yana wani irin kuka mai cin rai.
Tabbas badan.... Oh nimaizance ma?, Allah kafini sanin abinda ke b'oye Allah kasa da rabon sake zamana da zainabu kai kasamun qaunar ta Ya Allah, Kaikuma zaka ciren Allah kaban juriyar da haquri na rashin zainabu.
Ameen yace da kansa kana yaci gaba da share hawaye masu zafi.
Ita kam ko sauraran sa bataiba, burin ta takaranta abinda ke ciki.
Alhamdulillah ya saketa, saki guda cal tare da roqon tasake bashi damar qara zama da ita akaro na biyu.
Tsaki taja, sannan ta janyo trolley nata sai cikin motar sai gida.

@ut@r h@jiy@ CE.
[5/17, 10:26 AM] 🍀: 🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

      ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEIN

      2017/1438AH

PAGE 93-96

Da gudu take sharan mota ita zuwan cikin farin ciki take Allah yarabata da ala qaqai a haka ta isa gida.
Part nasu ta zarce direct, Baba sallah take so d'aki tai abinta jakar tata ma anan ta ajiye ta tsakar parlour d'in.
Ko da Baba ta idar da sallah shiga d'akin tai tana duban zainabu wadda tai rashe rashe akan gado da waya a hannun ta, tana turawa group nasu na FOUR STARS saqo "cewa itafa Allah yaimata lud'ufi yarabata da MOHD.
Inalillahi da Salati sukafara rubutowa saboda firgici da shiga rud'u.
Feedoh ce tai qarfin halin bugo mata waya duk abinda take Baba na bayan ta tana jiran ta juyo ta ganta.
"Hello pure blood mainaji kin fad'a yanzu?, oh mun rabu ya rubutan saki, bakiji ba jinake kamar na sauke kaya ne akaina yau single nake Alhamdulillah.
Ashsha pure blood kinyi wauta a duniya, tabbas saikinyi nadama da danasani mara amfani, wallahi kinji kunya wayon ki yazama na banza.
Dubemu kaf ba alfahari ba, mijin ki yafi namu komai da komai.
Kyau Ilimi arziqi ko baifisu arziqi ba amma kulawa da farin ciki da baki full time dayake yafi namu.
Pure blood a yau kikace ga abinda kike so Dr yimiki zaiyi amma butulci da nunawa Allah baimiki daidai ba yasa kika kaishi maqura ya sake ki.
Feedoh kya tsaya ki amshi uzuri na bakisani gaba ba, kamar 'yar ki ta cikin ki kinamun fad'a, nayi kiyi abinda zakiyi kuma zamuzo gidan ne sai anjima oga ya dawo naji tsayuwar motar sa.
Mts bazaku gane SO da QI ba.
Zainabu yadai naganki da jaka nakuma ji kuna wata magana?, Eh Baba Ya MOHD ya sake ni
Saki! Oh ni 'yar nan amma yaron nan ya cuceni, Allah ya isa tsakanin mu da shi, mugu azzalumi bara uban nasa ya dawo.
A'a Baba ninace ya saken bashi ne ba, alfarma d'aya zakimun kada ki yawaita fad'a saboda nice silar komai.
Bangane ba ya sakeki sannan kizo kice laifin ki, amma MOHD yacika butulu saidayagama tsotseki shine zai sakar mun ke, to ta Allah batasa ba kyau ko d'an sarki saiya kyasa ki bakida makusa ko d'aya a yau badan Idda ba nasan zaki sami mai son ki.
Baba nidai kada kice komai, naji.
A nan ta zauna abin ta sunashan hira da Baba hare bacci ya kwasheta.
MOHD bawan Allah zazzab'i ciwon kai Lokaci d'aya sukai masa rufdugu har yanzu kuma baibar zubar da hawaye ba kuka ne sosai a Idon sa Sallah ma da qyar ya samu yayi yana idarwa yakoma kan gado.
Washe gari Iyayen nasu gaisar da Baba suka zo yi, saiganin zainabu sukai a zaune da alama ma anan ta kwana.
Kallon juna sukai, Abban tane yai qarfin fara cewa zainabu yanaganki haka?.
Yabazaka ganta ba kuwa, Sakin ta yai, zata zauna masa a gida ne ai dole ta dawo.
Saki Baba!, kwarai gama takardar shaida, "Inalillahi wa Inna ilaihi rajiuun.
MOHD da hankalin sa yai haka, amma bai kyauta ba.
A'a Yaya kasan halin zainabu tabbas akwai abinda taimasa amma MOHD bazai sake ta haka ba.
Umar kome tamasa baikamata ya sake ta ba, kiramun shi a waya yazo.
Dr kam da qyar ma ya miqewa yaje d'akin sa yaiwa kansa taimako na saukar zazzab'in kwanciyar sa kenan Abba ya shaidamasa kiran da suke masa
Wanka yayi, ya fito ya tafi.
Da sallama ya shiga amma Abban zainabu ne kawai ya amsa, Baba da Abban sa da mugun kallo suka bishi.
Zama yai a qasa."Ina kwana Abba kun tashi lafiya?, Mari shine amsa gaisuwa.
MOHD ka cuceni, wallahi nazata kaime riqe zainabu ce da amana ko bayan ranmu, Amma ba komai ka kuma kyauta abinda kai.
Abba kuyi haquri sharrin.....Tas tas kake jin saukar mari Abban sa naimasa shi, da sauri zainabu ta miqe tana Abba kayi haquri kadena marin sa dan Allah saitin fuskar sa tai anan Abba itama ya zubamata nata marin, da sauri yace zainabu tashi gashi kinsa na mareki, kalla abinda nakemaka takejin zafi batai duban qasqancin da kaimata ba.
Magana zatayi kenan, Abban ta shima yafara zubamata nata kason da qyar aka kwaceta dan duka yafara kaimata takoina.
Baba kuka tasaka zai kashemun yarinya, nashiga uku da qyar suka kwaceta amma fa ta jibgu sosai.
Fita iyayen sukai, shima MOHD bayan su yabi yai gidan sa.
Zainabu an doku duka banawasa ba, dan bakin ta saidaya fashe da goshin ta, ruwan d'umi Baba taimata take itama zazzab'i yakamata sai bacci.

Autar Hajiya ce
[5/17, 10:26 AM] 🍀:

🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

       ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEIN

       2017/1438AH

PAGE 97-100

Dr kam saida abokin sa Raheem yazo ya dubashi, asibiti ma kwanan sa uku kenan baije ba, amma yanzu Alhamdulillah jiikin yai sauqi.
Pretty dai itama taji jiki, dan kwananta biyu tana ciwon kai da zazzabi itamadai yai sauqi
Yau wayar ta ta janyo, zata shiga FOUR STARS tai hira, saitaga anyi removing nata, dubawa tai sosai really an fidda ta, garin yaya kenan?
Akwai Labari taje nan ma still bata ciki, to meya faru batada amsa haka ta ajiye wayar zata fara bacci kenan tajiyo sallama da gudu ta miqe FOUR STARS ne dukkan su, STYLISH, CUTE ZAHRA and FEEDOH.
Rungume su tai tana dariya, Allah yanzu nagama masifa zanje ayi hira sai gani nai ban ciki meya faru.
Kowacce jikin ta tajanye daga nata, kana suka sami waje suka zauna fuska ba far a'a suke duban ta.
Kukuma yau me kuke ji, bara nakamuku lemo da cake. A'a pretty mun qoshi banda abinki ai daga gidajen mu muke, muncika cikin mu da abincin mazajen mu STYLISH itace tagayamata haka itada batada magana ma.
Feedoh ce "tace gayamata dai stylish.
Oh kinga bakya cikin group koh?, eh tace cikin sanyin jiki.
Ok gaskiya ninacireki, dalili?, muntashi daga FOUR STARS mun koma THREE STARS ke kuma kinzama ONE STAR.
Zahra bangane ba, meye haka?, eh zaki gane kinga mu da auren mu da mazajen mu wataqil ma ciki garemu duka, munason mazajen mu sosai, muna binsu muna kiyaye umarnin su da fushin su.
Kinga kuwa bazamu zauna dake ki b'ata mana tarbiyya ba, muzamo muma cikin zawarawan da za'a irga, indai muna tare dake to kuwa zamu koyi halin ki shiyasa mukaga gara mu rabu da juna kowa yakama tashar sa.
Ada kowacce cikin mu tanajin maganar kowacce, kanmu a had'e yake abin koyi da alfahari wajen kowa amma ke a yanzu mun raba kai.
Kwarai maganar ki Zahra daidai ce, zaman mu dake yazo qarshe munai miki fatan alkhairi mu zamu koma mijina yana gida, inji Feedoh wadda hawaye yawankewa fuska sun mata haka ne danta gyaru badan cin fuska ba.
Amma duk da haka taji zafin maganar da Zahra ta gasawa qawar ta.
Munason ki sosai 'yar uwar mu dole tasaka zamu juya miki baya.
Gara ku suna gida ni yau zaidawo, kunsan a Lagos yake so yana hanya zanje gyaran jiki da gyaran gida kutawo inji Zahra.
To pretty saduwar alkhairi saimun qara had'uwa kuka dukkan su suke, ganin sun miqe yasakata tashi tabisu a bay.
Yi zaman ki kinji, basai kin rakamu ba. Pure blood ni kukewa haka yau, amintar kenan nagode, muma haka agaida Baba idan ta dawo.
Da gudu ta koma ciki tana kuka, Feedoh ce zata bita itama kukan take sosai, saijin hannun ta tai cikin na Abba.
Kada kibita kici gaba da zama jaruma wajen gyara tarbiyyar qawar ku, tabbas kune qawayen da za'ayi alfahari daku kuncika FOUR STARS dole na jinjinawa tsarin ku.
Naji duk abinda kuke fad'a kun birgeni matuqa, Insha Allah qawar ku zata gyaru tadena abinda take, kukan kuma ya isa haka yarana Allah yaimuku albarka.
Ameen sukace, kowacce hawaye take sharewa, sunason pretty much amma kodan tai rayuwa ingantacciya sa gyaramata halin ta.
D'agawa juna hannu sukai, kowa ta shiga motar ta suka fice.
Birgima sosai pretty keyi, sai yanzu take ganin wautar ta, Ya MOHD ya had'u over yanada qualities d'in da ba wacce zata qishi, uwa uba haquri amma taimasa haka?.
Inama baya zata dawo, sosai tafara tunanin moments nasu Lokacin datake gidan.
Rayuwa tafaraiwa zainabu zafi, Abban ta yadena kula ta, Zahra ma haka Mama kam da kunya tace zata wajen ta.
Ginshiqin ta FOUR STARS ko flashing idan taimusu basu d'auka ba halin fita kuma.
Baba kullum saidai taitaimata fad'a akan wai ta canja kisaki ranki ita yazatayi.
Yau tun safe ta miqe sakamakon amai dayazo mata , yinsa tai ba qaqqautawa duk ta galab'aita saida Baba ta taimakamata sannan ta iya miqewa.
Kwanan ta wajen uku tana fama, abinci indai ba Taliya da manja ba bata iya cin komai.
Sai kwaro da Kashu datake so.
Ganin ba sarki sai Allah dole Baba ta kirawo Abba yakaita asibiti.
Atamfa purple tasaka super, mayafinta da takalmi purple sunmata kyau.
Powder da lipstick tasaka kawai suka tafi, a mota sai janta yake da hira amma inaa takasa sakewa a yanzu tafara nadama zuciyar ta MOHD kawai take haskomata.
Baran idan tashiga group 5 nayi kowacce tafara, nidai sai anjima lokacin girki, wata tace oga ya dawo wata tace zasu umguwa itada oga amma ita saidai tai gefe.
Da yawa matan kyawawa ne, amma mazajen nasu kaikace arami akan tonusu dan baqi da muni, wasu cikin matan sunfita kyau class da komai.
Amma ita Allah ya kashe yabata, maison ta tsakani da Allah mai kula da ita mai aji da kwarjini taqi shi.
Babban tashin hankalin ta (yar gata ce) data karanta na (Meimi vee) yadda taga zee ta wulaqan ta Al'ameen shi maiyimata komai da komai amma taqisa, da ya sake ta ta auri Adeel d'in ga rayuwa yadda taimata kowa ya tsane ta nikam zainabu naga takaina.
Ya MOHD kayi haquri, tun banjima a gida ba nafara ganin abinda na shuka mahaifina ya rabu dani akan ka qawayena na yarin ta.
To ni ai ba wanda nake so, ba wanda yake sona, wama zan aura dana bari nai saken danarasa gwarzon miji like u Likitana.
Kuka taji ya kwacemata, sannu take share hawayen wai dan kada Abba yagani, amma ina kaf abinda take yana gani, yasan kuma laifin na wajen zainabu dan MOHD yagayamasa komai fatana Allah ya qara daidai taku zainabu tafara gane rayuwa.
A haka suka qaraso, cikin asibitin AKTH d'in.
Wajen MOHD yakaita lokacin ya fita, zauna zainabu kafin ya dawo yanzu zai shigo tunda naga layi duk shi suke jira inada theatre zani kafin ya dawo, Tom Abba
Waje tasamu ta zauna kafin yazo.

Autar Hajiya ce
[5/17, 10:26 AM] 🍀: [3/9, 8:50 PM] Re@l @ut@r H@jiy@🤳🏻:

🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

      ®NWA

©ZAINABU Y HUSSEIN

    2017/1438AH

PAGE 101-105

A layin data zauna mata ne masu class, kowacce idan ta bud'i baki alkhairin mijin ta takeji ana fad'a.
Wasu ma magana suke akansa.
"Aisha yaufa Insha Allah zan gayamasa inason sa, DR ya had'u over, Allah yasa ya amshi tayina ina and qaunar sa gashi simple daga ganin sa idan na aureshi na more wallahi zan masa duk abinda yake so koda zai zaneni kullum inason sa haka bara yazo shiyasa ma nazo da wuri.
Das taji a qirjin ta, batagama dawowa hayyacin taba, a bayan ta ma hakan take wajen sa sukazo akan maganar nan dai d'aya mai kalma bakwai SOYAYYA.
Da da hali zainabu tashi zatayi, tagaji da jin takaici wayar ta ta kunna Dandalin Autar Hajiya ta shiga.
Nan ma ba sauqi, hira Auta take akan masu wulaqanta miji da qarshen su baya kyau.
Oh kuna ina kuji wata sabuwa, wai mata da kansu suke wulqanta maza amma abin baiba, kodan kasamu good record kayi abin kirki nan fa kowacce tafara fad'ar bakin ta wasu suce ai saita auri d'an giya wasu suce sukam idan d'an sune sakin ta ma zaiyi abin ba sauqi dole dai datar ta kashe tab zqunat jugum.
Oh Hansatu kinji wai Umar ya auri Farida kuwa?, naji mana wallahi tamin daidai, ai Sakina tab cuci kanta Allah yabaki miji na nunawa sa'a amma kiringa wulaqantashi ke ba kyau kika fishi ba, ba komai ba qawar ki tana baki shawara kika qi, gashi nan ya auro qawar tanaimasa komai.
Wallahi kuwa ance yama canjawa Faridan gida, yo ko nice mai kyautata maka wataqil ma ya saki sakinan Allah yasa yasaketa kuwa ita ganin ta bazai iya qaro aure ba gashi ya qaro qawar ta ma.
Ihu kad'ai pretty bata saka ba. Lallai nayi wauta, ko ya MOHD zai maidani? Haba zainabu aikin gasa shi ko rashin bashi haqqin sa da abinci ai ya auro wata wadda zatai masa.
Gama misali a kusa dake "tace ko dukan ta zaiyi itadai tanaso a haka.
Qamshin turaren sa data shaqa shine ya ankarar da ita yazo, kafin ta d'ago ya shiga office.
Layi aka fara kira, sannu kowacce ta fito "tace sai anjima Allah yasa mudace.
Ganin layin yaqi qarewa yasakata miqewa ba magana taje kusa da ita wurin, Massenger yana ganin ta tsugunawa yai ya gasheta ya bud'emata qofa ta shiga.
Da sallama ta shiga, da sauri ya d'ago jin kamar miryan pretty tasa, itace kallon kallo suka fara babu wanda ya iya d'auke idan sa daga na kowa.
Ita sai yau ma take ganin kyan kayan ta, nan da nan kishi ya tasomata wai wata zatace ya sota da yawa ma.
Shine yai qarfin halin "cewa pretty ya kike?, maimakon amsa sai harara, dariya yai yace ok.
Maizance ko bakida lafiya ne?, kai ta d'aga, Ido ya zaro tun yaushe ne meke damunki?
Bayani taimasa yanayin yadda takeji, kallon tai yai ikon Allah, tabbas zargin sa zai tabbata dan yaga alama amma bara dai yaga.
Kinga shiga ki fitsari kikamun, batayi musu ba kuwa ta shiga takamasa.
Fita yai baijima ba yadawo wajen test yaje da sauri ya auna tabbas cikine wata biyu Alhamdulillah murna ce takamashi tun a wajen.
Shigowa yai allura ya had'a wajen biyar yace oya bud'e amiki allura, ni wallahi banso, bakiso?, dole kam ayita, yarinya tashi, ganin zataimasa nuqu nuqu ya miqar da ita jikin sa ya rungume ta a hankali yafara zame zanin ta qara tasaki kafin ma ya soka.
Kinga rufe idon ki a hankali zanmiki, yauwa rife, rifewa tai qarin armashi harda maida hannun ta bayan sa ta zagayo tashiga salon so batasan ya tsira alluran ba.
Shima yarda sirinji yai yabi sahun ta.
Sunman ta inda suke gaba d'aya sun shagala oh Allah ya kyauta.
Cikin zuciyar sa yace naidaki mata ta inason ki sosai ally yasa kema haka yanzu.
Juyo da ita yai sosai yaga taimasa kyau sai rama data yi, lips d'in sa yakai kan nata....nidai baya na juya bazan iya ganin komai ba.
Ganin shirun yai yawa yasaka na juyo, da sauri naqara juyawa harda haki na waih.
Kwankwasa kofar da akene ya dawo dasu hayyacin su da sauri suka cika juna itakam idon tane a kulle dariyama tabashi waih pretty da kunya kodai tafara sona? baida amsa.
Gyarawa yai ya kame akan kujeran visitors itakam tasa kujeran ya maidata ta zauna.
Abba ne ya shigo, a'a kaikuma shiru haka, anata nocking yaya meke damun ta?
Abba ka kusa zama Kaka, pretty nada shigar ciki wata biyu Abba kace dan Allah tasoni mukoma auran mu?.
Ciki Alhamdulillah Allah abin godiya Allah mungodemaka.
Itakam cin maganar tai wata iri, tunani tai lallai amai bacci yanacikin sign namasu ciki, kunya taji takamata sosai.
Ranar dai Dr kasa aikin yai dole sai wani akasaka da kansa ya riqemata jakar yakama hannun ta suka fito.
Itama d'aya ganin ana kallon su yasakata kwanto da kanta kafad'ar sa haka suka fita har suka isa gida.

Autar Hajiya

Comments

Popular posts from this blog

Rashin Gata 166-170

Rashin Gata 106-110