Rashin Gata 146-150


🌼🌼RASHIN GATA🌼🌼

```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

*NAH*
```FOUR STAR'S```✨✨✨✨

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI SHEHU
(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HASSAN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRA BUKAR
(CUTE ZARAH)```

146-150

      Tana shiga toilet ta sake sakin wani kukan wanda yafi na farko data yi, ta daɗe tanayi har sai da taji ana buga k'ofar bayin sannan tayi yin k'urin fara wankan wanda tanayi ne tana share hawaye da majina.
  Tana fitowa tayi saurin shiga ɗaki dan karma wani ya tsaida ita, Mama ce ta shigo ɗak'in tare da mik'a mata kaya tace "oya saka kaya game makeup can tana jiranki" karɓa tayi tare da cewa "gaskiya ni Mama babu wata kwalliya da za'ayi min" tana faɗa ta mik'e tana saka kayan ranta a haɗe.
   kallon ta kawai tayi amma batayi magana ba tabar ɗakin cike da mamakin Nana, nan ta turo masu makeup ɗin suka shigo suna mata tsiya kasan cewar su abokan wasan  Sameer ne saidai an gargaɗe su  karsu sanar da ita cewar Sameer ne mijinta.

     Duk abinda suke yi uffan bata ce ba har aka gama.
  Nan mutane suka dinga shigowa suna kallonta ana mata guɗa, harta Nama da bata taɓa ganinta tayi kwalliya ba yau sai taga ta koma kamar wata Nana daban da ba tata ba, tayi murmushi kawai tare da k'arasawa wajanta tana zama kowa yabar ɗakin dan su tattauna.

     Nana kam k'in k'allan Mama tayi, dan gani take tamkar ta dena sonta yanzu, hakan da Mama ta lura ne yasa tayi gyaran murya tare da cewa.
   "khadita tah"
shiru tayi t'aki magana, Mama tayi dariya mai matuk'ar kyau sannan tace haba Nana ta, konayi wani laifine wanda ya hana a kalleni sannan ya hana ayi min magana?

   Sai yanzu ta ɗago suka haɗa ido, Mama ta gyara mata mayafin jikinta sannan tace "to Nana zaki tafi, zaki tafi gidan mijinki fatana gareki kiyi mai biyayya kamar yadda nasan iya bak'in kok'ari na horeki da ita, biyayya kansa miji ya kara son matar shi" jin abinda Mama tace ne tasa Nana cewa yoni dama ai bason shinake ba bare nasa ran samun k'ari, ta faɗi haka cikin ranta tana faman jin Mama nata nasiha wadda duk rabi ta ɗayan kunnen yake bi dan baji take ba.

    Lokacin da sukaji kawu mu'azzam na cewa ai gara a fito a tafi dan abuja ba nan bace, nan da nan Nana ta kara shiga wani ruɗa nan hankalinta ya kuma tashi ta rushe da kuka tare da kankame Mama kamar zata shige cikinta...
   Gaba ɗaya suka sa kuka wanda kowa da irin abinda yake sakawa, Mariya shiga ki fito da yarinyar nan kun sa mutane na jiranku bayan kunsan ku ake jira," suka jiyo muryar kawu Mu'azzam yana kuma faɗa cikin murya mai faɗa² haka suna ji suna gani aka rabasu wadda aka kira da mariya ta ja hannun Nana suka wuce wajan da aka tanadi Motocin tafiyar.

   Kowa fatan alk'airi yake musu haka akaja mota suka bar kofar gidan, har suka karasa abuja Nana kuka take suna zuwa ta ganta gidan su Umman Sameer nan ta fara mamakin to meya kawo su nan! ganin babu amsa yasa tayin shiru amma kam tana da tarin tambayoyi.
   "Nana tah" cewar Umma data shigo ɗakin fuskarta fal murmushi da murna, cik'in kunya Nana ta sakko kasa tare da cewa "ina yini Umma?" lafiya lau yata taso muje kici abinci, duk da batajin yunwa amma ta kasa yi mata gaddama ta mike suka wuce gurin Momy inda take kokarin haɗa mata kayan abincin wanda duk anyi sune da kayan haɗi na amare (mukam 4star muka ce lallai Sameer ɗan gata).

  Sosai Momy tasa taci abincin tasha wani haɗin yought da aka yi mata shi tun daga kasar saudiya Umma tasa hajja baseera tayo mata, yana da kyau sosai..
    "wajan 12:30am kowa ya samu gurin kwanci, Nana kwance ga ɗinbin tambayoyi cikin ranta, wai shin ya akai suka zo gidan nan bayan tasan gidan mijin da aka bata za'a kaita tunani kala kala babu wanda batayi ba har ta fara tunanin ko taje ta tambayi Sameer? kai a'a haram domin yanzu ta zama matar wani magana ma yanzu ba kasafai zata na yi mai ba, sannan kuma ga maganar daya raɗa mata cikin kunnenta rannan dasuka haɗu, sai ta samu kanta da yin murmushi wanda har cikin ranta taji daɗin shi komai yasa haka oho.

Washe gari aroung 6:00am, tunda Sameer yayi Sallah wadda yanzu tunda ya shiga ruɗanin rashin Nana ya ɗan farayi saidai har yau baya yinsu akan lokacin su, yana idarwa ya bar gidan dan yasan matar da aka aura mai jiya aka kawota tana gidan kuma Umma saita neme shi hakan yasa ya bar gidan ba tare da yaje ya gano Momy ɗinshi ba duk da itama harda ita aka hadu aka yimai auren dole.
    Direct office ya wuce ba wanka ba gayun nan daya saba, wannan kuma duk yana ɗaya daga cikin punishment ɗin daya shiryawa kanshi har sai bayan ya gano abar sonshi farin cikin shi heartbeat ɗinsh sannan zai koma normal.

    Karfe 5:00pm su Momy sun gama shirya Nana dan mikata gidan mijinta wanda yanzu Nana kejin tamkar ta mutu dan bakin ciki da takaici.
    Wajen Daddy suka kaita nan ma nasiha ya mata akan tabi mijina sau da k'afa "Nana nasan zaki mamakin yanda aka kawoki gidanan nine nacema Mamarki akawoki nan dan yanzu baki da wani uba daya wuceni inasan kirik'e sirrin mijinki kimashi biyayya watarana komi zai koma daidai" haka ya dinga mata nasiha daga karshe yayi umurni da a wuce da ita gidanta....
   Kuka ta saka sabo su kansu su Umma tausanta ya kamasu, haka aka d'auketa aka wuce da ita gidanta dake Area 8, tunda suka shiga gate d'in take kuka haka aka fito da ita aka nufi cikin gida da ita...
   Sakin baki yan kai amarya sukayi suna kallon gida, parlour uku sai bedroom hud'u kowane bedroom akwai toilet, sai balcony da aka k'awatashi da throw pillows kitchen ma ya sha gyara gida dai ya had'u iya had'uwa kamar gidan wata d'iyar shugaban k'asa ita kanta Nana sakin baki tayi tana kallon gidan dan tasan idan da basu Umma ba babu wanda zai mata wannan gatan, ji takeyi inama gidan wanda take mafarkin samu ya zama mijinta ne da sunyi rayuwa mai cike da farin ciki....

Four stars🌟🌟🌟🌟

Comments

Popular posts from this blog

TUNA BAYA 10-105

Rashin Gata 166-170

Rashin Gata 106-110