Rashin Gata 151-155


🌼🌼 *RASHIN GATA* 🌼🌼

```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

*NAH*
```FOUR STAR'S```✨✨✨✨

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI SHEHU
(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HASSAN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRA BUKAR
(CUTE ZARAH)```

151_155

 
   Bayan yan kai amarya sun tamata nasiha, suka kama hanyar komawa gida kuka takeyi sosai da duk Wanda ya ganta sai ya tausaya mata, tana nan kan gado a zaune ko motsi ta hana kan tayi gashi lokaci sai tafiya yake, 3:30am agogon dakinta yanuna.

Take tsoro da fargaba suka cika zuciyar Nana. Fadawa tayi kan gado, tana mai cigaba da kukanta, wayyo ni Khadija, wanan wane irrin aure ne Mamata tayi min, yanzu? *rashin gata* har yakai a yiman auren dole.

Yunwa ta faraji har jikinta yafara rawa saboda wata masifafiyar yunwa data keji, dan rabonta da abinci tun safe shima kuma ba abincin kirki bane, ledojin da Momy ta hadata dashi ta janyo kajine da lemo da yought, take tabude tafara ci saida tayi kat kana tasamu nutsuwa, toilet tafada ta daura alwalah tafito kayan jikinta ta canza zuwa marasa nauyi nafiloli ta shigayi tana godiya ga Allah da yarayata har zuwa yanzu da kuma addua'ar Allah ya dorata akan mijin yasaketa dan ita ba kaunar auran takeba tashafa taje tarufe dakinta tayi addua'ar kwanciya ta kwanta.

Sameer ne kwance a dakinsa sai zabga tunani yake wai shi yau aka daurawa aure da wata ba *dream girl* dinsa ba, nan take wasu hawaye masu uban zafi suka gangaro daga fuskar Sameer shi dai har ga Allah yanzu ya yarda son Nana yake, to mai yasa ita bata sona yanzu yazanyi darashin Nana?  My life is not incomplete without khadijat, itace Rabin raina da kuma rayuwata, da wanan tunani har aka kira sallah asuba a kunnansa, ya mik'e yaje yayo alwalah yatafi masallaci (wai mukam 4stars mukace basabanba yau Sameer da sallar asuba dazuwa massallaci).

6:30am agogon dakinta ya nuna, sai a lokaci Nana ta mike tayi sallah tajawo littafan addou'in ta da tataho dasu. Azkar ta shiga karantawa tana gamawa ta duk'ufa da addou'i har sai da gari ya waye sanan ta koma barci, bayan kamar awa 3 tafarka, fitowa tayi tana zaga ko ina tana kallon gidan, yanda aka tsara mata gidan ya matuk'ar burgeta babu tantama komawa aka daura mata aure dashi maiji da kud'i ne...

   A ranta tafara sakawa kilama tsoho mahaifiyarta ta aura mata, sai kuma tasaka kuka

Karfe 7:00am Sameer ya shiga gidansu direct d'akinshi yaje ya kwanta bai tashiba sai kusan 1:32pm mikewa yayi ya shiga toilet yayi wanka yana fitowa ya tada sallah yana gamawa yayi dakin Dady dinsa domin gaisheshi.

  Bayan yafito ne yawuce part dinsu Umma, cikin murna da farin ciki suka tarbesa bayan sun gama gaisawane suke tambayarsa amarya, wuce amaryar kuma? "Au mukake tambaya don ubanka kajimin yaro" umma tafad'a cikin fada. Hmmmm nifa Umma banga wata amarya ba jiya Dan ni sai wajan 2 nashiga gidan, kuma nasan lokacin tariga tayi barci, shiyasa direct nayi dakina kuma koda na tashi bayan nayi sallah gida nayo, nayi barci don jiya bansamu damar yin barci ba.....
   Sakin baki Umma tayi tana kallonshi, tsawa ta daka mashi "tashi kabamu wuri marar mutunci tun ban kifama mari ba, murmushi yayi ya mik'e yabar wurin, cikin ranshi yace "aiko bazata tab'a ganina ba har tagaji ta kama gabanta dan da visa na ya fito k'asar zan bari..." ta gumi Umma tayi tace "Mummyn Sameer anya bamu shiga hakkin Nana ba? Murmushi tayi tace "karki damu Umma kina nan zasu shirya kansu raina na bani kwanannan zasu daidaita kansu" Ajiyan zuciya tayi tace "Allah ya kawo lokacin da wuri" Amin Umma..
   Kwance take tana tunani wannan wane irin aure tayi? Ace tun jiya mijinka bai nemeka ba bai san halin da kake ciki ba baisan kaci ko baka ci ba tabbas yau ta tabbatar da shima ba santa yake ba. Ashe akwai Wanda yafi Sameer mugunta a rayuwa? Dan tasan idan Sameer ne bazai mata haka ba....

   Bai shigo gida ba sai biyun dare, yana shigowa d'akinshi ya wuce dan dama yasan tayi bacci..
   Tanajin shigowarshi tai saurin fitowa dan taga waye wannan mijin nata amma cikin rashin sa'a kafin ta fito har ya maida d'akinshi ya rufe d'aki ta koma ta fad'a kan gado ta fashe da sabon kuka mai tsuma rai, "wannan wace irin rayuwa ce? Dama haka ake aure? Nikuma tawa k'addaran kenan tabbas yau nasan Mama tadaina sona tunda harta aura man wanda baisan darajata ba" haka ta dinga surutu har bacci yayi gaba da ita...            

   Kuka yake sosai kamar ranshi zai fita, dafashi tayi tace "Sameer lafiya?" D'agowa yayi ya harareta yace "koma miye kece kika jamana, kince kin tsaneni bazaki tab'a sona ba sanadiyar haka an ban wadda ba zab'ina ba" kuka ta fashe dashi tace "wallahi Sameer ina sanka kai nakeso ka taimakeni" Khadeeja is to late yanzu hak'uri zamuyi da juna yana fad'ar haka ya mik'e yana hawaye Sameer! Sameer!! Sameer!!! Haka ta dinga kiranshi Amma bai juyo ba kuka takeyi sosai. Firgigit ta farka ta fara waige waige tabbas mafarki takeyi to mike shirin faruwa kodai shima Sameer d'in anmashi aure kamar yanda akamata? Kuka ta fashe dashi ta dad'e tana  kuka taga kukan bai mata ta mike ta d'auro alwalla ta fara nafila tana neman d'auki akan halin da take ciki....

*#team RGT* ❤

Four star's✨✨✨✨

Comments

Popular posts from this blog

TUNA BAYA 10-105

Rashin Gata 166-170

Rashin Gata 106-110