Rashin Gata 156-160


🌼🌼RASHIN GATA🌼🌼

```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

*NAH*

```FOUR STAR'S```✨✨✨✨

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI SHEHU
(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HASSAN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZARAH BUKAR```
```(CUTE ZARAH)```

#team RGT

156-160

   Yau kwananta biyu batasa mijinta a ido ba, sai dai babu abinda tarasa a gidan, dan Umma ma ta turamata mai aiki kullum take zuwa da safe ta tafi da yamma, yanzu babban burinta shine takoma gurin aikinta duk da 2weeks suka bata, sai taji duk zaman gidan ya dameta.

   Bayan kwana uku su Momy sunje mata harda Dady, taji dad'in zuwansu sosai, aman bata wani nuna musu cewa bata tare da mijinta ba, ko bama ta tab'a ganinsa ba, Dan koda suka tambayeta yana ina cewa tayi ya tafi Kasuwa, dan batasan ma aikin dayake ba....

  Momy ce  tayi karfin halin tambayarta kodai tana sa damuwa a ranta ne? Tace  "a'a" dan sosai ta rame, haka su Umma suka kai mata har yamma  sanan sukace zasu koma, anan ne fa tasa musu kuka ita sai tabisu, baki sukai ta bata daban hakuri, dakyar ta hakura ta zauna Umma harda Yar kwallanta...
  Yau ma kamar kullum tayi shirin barci, ta rufe  idonta dan tayi barci, aman ina barci yaki zuwa sai moment din Abun da ya faru tsakaninta da Sameer ranar da suka had'u yake tambayarta damuwarta take ta tunawa tana faman murmushi.

Ita a yan kwanakin nan ta rasa gane kanta ya zatayi da auran wani gashi bakon al amari yana  ziyartar zuciyarta, badai son Sameer nake ba, yaron daya tsaneni fiye da komai a yaruwarsa, saboda tsana da yayi mani ko gidanmu bai zo ba tunda aka fara bikina,  kuma nasan su Mummy sun sanar masa auren dole akayi mani, aman yakasa nemana komai ya hanasa zuwa gurin daurin aurena?, wata zuciyarta tace saboda bai kaunarki kuma ya tsaneki.
   Ah ah Sameer bai tsaneni ba na dad'e da ganin soyayyata cikin idonshi kawai nasan zai d'auka bansanshi ne shiyasa har na yarda na auri wani, sabon kuka ta fashe dashi har bacci ya d'auketa tana kuka....

Kaya yake had'awa cikin trolley da alamu tafiya zaiyi sai da yagama had'awa kaf kana ya shiga wanka, yana fitowa ya fara shiri yana gama shiryawa ya feshe jikinshi da spray d'in boss orange k'ana nan kaya ya saka na company HUGO BOSS kana ya feshe jikinshi da turaren boss orange, cumbing kanshi yayi wanda sai salki yake alamar yasha gyara kanshi ya kalla a mirror murmushi ya saki wanda ke k'arama fuskarshi kyau...
   Takalmi yasa na company Aldo, trolley yaja yabar d'akin yana fita driver yayi saurin amsar trolley, mota ya shiga ya zauna, dasauri driver ya ja mota sun kai bakin gate kenan ya tsaida driver fitowa yayi  ya nufi cikin gida, daidai d'akinta ya aje mata rapper 100 guda uku tare da writing note, yana ajewa ya juya ya tafi....
   Saida suka hau kan titi driver yace "Alhaji ina zamu?" Airport ya bashi amsa a tak'aice...
   Driver juya muje gidansu Nana, ba musu driver ya juya basu tsaya ko ina ba sai maitama suna isa sukayi horn da gudu maigadi ya bud'e masu gate, suna shiga ko parking ba'a ida ba ya fito yayi cikin gida da sauri yana kiran Mama..
  A falo sukaci karo ta fito daga d'aki ganin Sameer yasa ta fad'ad'a fara'anta, da sauri ya isa wurinta ya kama hannunta yace "Maaamma i miss you" i miss you so much Sameer, ya matarka? Tana nan lafiya lau Maaamma, hope kuna zaune lafiya? Eh sosai Mama, masha Allah haka mukeso... 
   Haka suka zauna suna ta fira rabin firan duk kan matarshi ne da takawo maganarta saiya canja dan baisan ya cigaba da mata k'arya zata ganoshi...
  Tunda ya zauna yake kallon k'ofan d'akin Nana ko zata fito amma shiru, gashi baisan tambayar Mama ita....
   Ji yayi firan duk ta gundureshi, hannunshi ya kalla yaga ya kusa lati tashi yayi yace "Maaamma tafiya zanyi na zo maki bankwana gashi na kusa lati" daidai yana aje mata rapper 100...
   Mik'ewa tayi tace "ina zakaje ne?" Wallahi zanje Germany akwai wani abu da zanyi na tsawon wata guda, toh Allah ya tsare na gode sosai da kulawa, murmushi yayi ya mata peck a hannu yace "bakomai Maaamma" rakashi tayi har wajen mota tana mashi adu'a.....
   Yana shiga mota ya kalli driver yace "sai kayi sauri nayi lati" da gudu driver yaja mota sai airport...
   Koda suka isa jirginsu ya fara boarding hamdala yayi ya sallami driver yaja trolley d'inshi....

   Dasauri ta diro daga kan gado ganin k'arfe bakwai yasa ta nufi toilet da sauri tana fitowa ta kabbara sallah ta dad'e tana azkar, yunwar data fara jine yasa ta tashi ta nufi hanyar fita...
   Jitayi tayi kwallo da abu, dasauri ta kalli wajen ganin kud'i yasa ta ja da baya, wata farar paper ta hango rubutun kan paper'n yaja hankalinta....
   Da sauri ta d'auki paper'n guntun rubutu ta gani wanda baifi layi uku ba, "ga kud'i nan kiyi buk'atunki kuma zaki iya komawa wajen aikinki..."
   Hawaye ne suka gangaro mata, tabbas yau tasan auren sadaka akayi da ita, dama haka ake aure? Wallahi da zan ganshi yau saiya sakeni aiba kud'i na aura ba, yamasan ina aiki kenan? Nikam Mama bata man adalci ba, haka ta k'araci surutanta da kukanta wanda ya zamar mata jiki tayi hanyar kitchen...
   Tea ta had'o tadawo d'aki tana sha tana share hawaye, ajiyan zuciya tayi tace "yau zan koma aiki nagaji da zaman shegen gidannan....
   Wayanta taji yayi ringing kamar bazata d'aga ba saida ta kusa tsinkewa ta d'auka sunan data ganine yasa ta saki murmushi...
    Dasauri ta d'auka "Hello Umma ina wuni" banji mi akace ba, Ah ah Umma ba matsala, dariya tayi tace "wallahi Umma babu.." toh Umma na gode ina gaida Mummy da Daddy, tana gamawa ta cilla wayan kan gado tasa sabon kuka...

   Saida tayi mai isarta ta tashi ta fad'a toilet, tana fitowa ta tsaya gaban mirror mai kawai ta shafa ta murza powder ta saka spray ta nufi wardrobe abaya ta d'auko red sai stones d'inta blue ta saka rolling tayi da red veil, duk da ba wata kwalliya tayi ba ga kuma Rama da tayi Amma duk da haka tayi kyau kamar balaraba ta fito....
   Handbag d'inta ta d'auka ta saka takalmi ta nufi hanyar fita saida ta kulle d'akinta kana ta fito tai sallama da mai aikinta akan zata koma aiki yau, tana fita ta nufi parking space sabuwar motar da Daddy ya bata ta ma key, tana ta dawa tayi horn maigadi ya wangale gate yana gaidata bata ko amsa ba ta fizgi motarta tabar haraban gidan.....
   Saida ta daidaita motarta kan titi kana ta d'auki hanyar asibiti...

   Yamma lik'is tabar asibiti, gidan Mama ta nufa dan tun da tadawo basu had'uba sai waya...
  Tana isa tayi horn ganinta yasa maigadi ya fara janta amarya bakya laifi, dariya tayi daidai tana fitowa daga mota tace "Baba kaima kazama Mama ko?" Dariya yayi yace na bari d'iyata haka suka gaisa cikin girmamawa...
   Da sallama ta shiga gida da sauri Mama ta tare ta rungume juna sukai Nana kam kuka ta saka, hannunta Mama yaja suka zauna da kyar ta lallasheta...
   Haba Nanana miye na kuka kuma? Ina cewa lafiya lau kuke zama yanzu komi ya daidaita d'azu mijinki kafin ya wuce airport ya biyo yaman sallama yace zashi Germany, na tambayeshi ke yace kina nan lafiya lau, Dan Allah ki kwantar da hankalinki...
   Ido Nana ta kafe Mama dashi mamaki ma ya hanata kuka cikin ranta tace "lallai guy d'innan ya rainani tafita zaiyi bai iya gayaman sai dai Mama zata gayaman shiyasa ya barman kud'i amman ya kasa gayaman zaiyi tafiya, nikam Nana naga takaina... "
   Yak'e tayi tace "shikenan Mama in shaa Allah zanyi yanda kikeso" rungumeta Mama tayi tana sa mata albarka...
   Tashi tayi tace "ni zan wuce Mama.."
  Rakota Mama tayi har gaban mota kana sukayi bankwana....
   Tana barin gidan ta fara kuka wannan wace irin rayuwa ce? Tabbas wannan mutumin yafi Sameer mugunta, haka ta dinga kuka harta isa gida.....

Four stars🌟🌟🌟🌟

Comments

Popular posts from this blog

TUNA BAYA 10-105

Rashin Gata 166-170

Rashin Gata 106-110