TUNA BAYA 1
🌪🕸 TUNA BAYA 🌪🕸
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
©ZAINAB Y HUSSEIN
DEDICATED TO AUNTY YABI BABBA KAITA & MEENA D'AN MUSA💎
Page 1⃣
KANO
Unguwar Gwammaja layin sectaria dake garin Kano k'aramar hukumar Dala. Mota ce k'irar KIA tabiyo layin a hankali take tafiya cikin nutsuwa daga bayan ta yara nagani k'anana mace da namiji kamar su d'aya macen kanta yasha gyara sai kyalli yake abin sha'awa anyimata two baby d'in nan da pink d'in ribbons.
Bin motar nai nima dan naga ko suwaye?.Mace ce ke driving d'in wow they look like sosai dan namijin ma Har yafi kama da matar daga gani dai itace Maman su driving d'inta take cikin kwanciyar hankali bata tsaya a ko'ina ba sai makarantar 'Yan Dutse dake nasarawa gidan governor.
Cikin nutsuwa ta fito daga cikin motar ta bud'ewa yaran nata k'ofar motar, Oya Zahra afito anzo school, namijin ne yace Momma kicewa sister tadena dukan mutane da rashin kunya?, ido ta zaro kai! Zahra fad'a cikin school?, lallai zamu b'ata, ku shiga amma Idan kika dawo naji bayani fad'a ba kyau maintain ur self babyn Mama.
Ok Momma, shima fa Ya Ammar yana dukan yara, koh to shikenan duk zan zaneku amma yau kada ayi fad'a?, tom Momma a haka suka fito peck tabawa kowannan su a left nd right na kumatun sa.
Lunch box nasu ta bawa kowa wanda agaban motar yake kusa da ita, hannu suka d'aga mata suna dariya bye Momma, bye my kids ayi karatu sosai kufi Amaah babyn Aunty Lubie especially u Zahra kada Ya Ibrahim d'in Aunty Yabi yace Amaa yake so bake ba.
B'ata fuska tai tace Momma bayan ya IB yaqi zuwa 9ja saidai Aunty tazo munyi fad'a ma, dariya Momman tai tace to ba ruwana da har yana cewa zaizo yayi hutunsa anan?, really Momma? Yes Zahra to naji zanyi karatu sosai. Ok atafi class direct plx Zahra?, Tom.
Haka ta fito daga cikin gate d'in tanajin farin cikin yau itace da yara har biyu, motarta ta shiga taimata key sai gida.
Horn tai maigadin yanaji da sauri yazo ya bud'e, sannu da zuwa Madam? Yauwa malam kalla yau najima nasami go slow a wajan Fagge kamar ba safiya ba, wallahi haka abin yake Madam Zahra antafi makaranta?, eh na sauke su.
Parking tai tafito, wayarta dake kujera mai zaman banza ta d'auka ta shige gidan. Direct upstairs tai bata tsaya a parlour ba, murd'a handle d'in tai ta shiga kan gadonta ta fad'a, wash nagaji jiya nasha aiki da yawa shiyasa, d'an kwalin kanta ta cire gashinta wanda yasha kitso k'anana shiyazubo a bayanta da gaban fuskar ta. baya ta mai dashi kafin tayi wani abu wayar ta tai k'ara da sauri ta tashi ta janyo ta dama kan dressing mirror ta ajiye ta.
Habeeby tagani akan screen d'in wayar yana yawo, da murmushin ta ta d'aga.
"Assalamu alaikum Habeeby"
"Wa alaiki salam Hayatee. murmushi sukai a tare.
Ya kike kin tashi lafiya, ya yarana ya zaman gwauranci?, hmm dukkan mu lafiya lou muke saidai rashin ka kusa, gwauranci kam sai kai dan ni ina kusa da yara na.
Lallai haka kikace ko kice gwauranci yana nan amma shine zakice haka?, bafa haka nace ba, ok ya Zahra?, Zahra anje school shigo wata kenan ma zan d'an kwanta ka kira. Osh baby nasan kingaji bara nabarki kiyi baccin ki kada Babyn mu ya cigaba da wahalar dake, hmm ni single nake.
Lallai wallahi ba single kike ba yarinya amma tunda kink'i yadda bara na dawo aga mai gaskiya?, ok Allah ya kaka lafiya, Ameen matata sai anjima koh nima zan fita nace sainaji muryar Hayatee.
Nagode sosai da kula dani da kake, haba dai ai wajibi ne akaina na kula da ke da komai naki matuqar ina numfashi ki kula da kanki kinji?, insha Allah you too take care? Insha Allah zan kula.
Wayar ta zare daga kunanta, hannu tasaka hawaye ta share lallai Mohd d'an halak ne, nayi dace da miji nagari Allah kabarni da shi har ranar lahira. Ameen tace.
Bashida buri a duniya d'aya wuce ya farantan rai kullum fatan sa yaga murmushi da kwanciyar hankali a fuskata.
Kwanciya tai idonta na kallon silin d'akin zuciyar tace tafara haskomata rayuwarta ta baya da abubuwan da tayi da komai
@ut@r h@jiy@ ce.
Comments
Post a Comment