TUNA BAYA 2-9

[5/16, 8:23 PM]


🌪🕸 TUNA BAYA 🌪🕸

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

©ZAINAB Y HUSSEIN

DEDICATED TO  AUNTY YABI BABBA KAITA & MEENA D'AN MUSA💎

Page 1⃣

           KANO

   Unguwar Gwammaja layin sectaria dake garin Kano k'aramar hukumar Dala. Mota ce k'irar KIA tabiyo layin a hankali take tafiya cikin nutsuwa daga bayan ta yara nagani k'anana mace da namiji kamar su d'aya macen kanta yasha gyara sai kyalli yake abin sha'awa anyimata two baby d'in nan da pink d'in ribbons.

  Bin motar nai nima dan naga ko suwaye?.Mace ce ke driving d'in wow they look like sosai dan namijin ma Har yafi kama da matar daga gani dai itace Maman su driving d'inta take cikin kwanciyar hankali bata tsaya a ko'ina ba sai makarantar 'Yan Dutse dake nasarawa gidan governor.

  Cikin nutsuwa ta fito daga cikin motar ta bud'ewa yaran nata k'ofar motar, Oya Zahra afito anzo school, namijin ne yace Momma kicewa sister tadena dukan mutane da rashin kunya?, ido ta zaro kai! Zahra fad'a cikin school?, lallai zamu b'ata, ku shiga amma Idan kika dawo naji bayani fad'a ba kyau maintain ur self babyn Mama.

   Ok Momma, shima fa Ya Ammar yana dukan yara, koh to shikenan duk zan zaneku amma yau kada ayi fad'a?, tom Momma a haka suka fito peck tabawa kowannan su a left nd right na kumatun sa.

   Lunch box nasu ta bawa kowa wanda agaban motar yake kusa da ita, hannu suka d'aga mata suna dariya bye Momma, bye my kids ayi karatu sosai kufi Amaah babyn Aunty Lubie especially u Zahra kada Ya Ibrahim d'in Aunty Yabi yace Amaa yake so bake ba.
  B'ata fuska tai tace Momma bayan ya IB yaqi zuwa 9ja saidai Aunty tazo munyi fad'a ma, dariya Momman tai tace to ba ruwana da har yana cewa zaizo yayi hutunsa anan?, really Momma? Yes Zahra to naji zanyi karatu sosai. Ok atafi class direct plx Zahra?, Tom.

   Haka ta fito daga cikin gate d'in tanajin farin cikin yau itace da yara har biyu, motarta ta shiga taimata key sai gida.

  Horn tai maigadin yanaji da sauri yazo ya bud'e, sannu da zuwa Madam? Yauwa malam kalla yau najima nasami go slow a wajan Fagge kamar ba safiya ba, wallahi haka abin yake Madam Zahra antafi makaranta?, eh na sauke su.

Parking tai tafito, wayarta dake kujera mai zaman banza ta d'auka ta shige gidan. Direct  upstairs tai bata tsaya a parlour ba, murd'a handle d'in tai ta shiga kan gadonta ta fad'a, wash nagaji jiya nasha aiki da yawa shiyasa, d'an kwalin kanta ta cire gashinta wanda yasha kitso k'anana shiyazubo a bayanta da gaban fuskar ta. baya ta mai dashi kafin tayi wani abu wayar ta tai k'ara da sauri ta tashi ta janyo ta dama kan dressing mirror ta ajiye ta.

   Habeeby tagani akan screen d'in wayar yana yawo, da murmushin ta ta d'aga.

  "Assalamu alaikum Habeeby"
"Wa alaiki salam Hayatee. murmushi sukai a tare.

  Ya kike kin tashi lafiya, ya yarana ya zaman gwauranci?, hmm dukkan mu lafiya lou muke saidai rashin ka kusa, gwauranci kam sai kai dan ni ina kusa da yara na.

   Lallai haka kikace ko kice gwauranci yana nan amma shine zakice haka?, bafa haka nace ba, ok ya Zahra?, Zahra anje school shigo wata kenan ma zan d'an kwanta ka kira. Osh baby nasan kingaji bara nabarki kiyi baccin ki kada Babyn mu ya cigaba da wahalar dake, hmm ni single nake.

   Lallai wallahi ba single kike ba yarinya amma tunda kink'i yadda bara na dawo aga mai gaskiya?, ok Allah ya kaka lafiya, Ameen matata sai anjima koh nima zan fita nace sainaji muryar Hayatee.

   Nagode sosai da kula dani da kake, haba dai ai wajibi ne akaina na kula da ke da komai naki matuqar ina numfashi ki kula da kanki kinji?, insha Allah you too take care? Insha Allah zan kula.

   Wayar ta zare daga kunanta, hannu tasaka hawaye ta share lallai Mohd d'an halak ne, nayi dace da miji nagari Allah kabarni da shi har ranar lahira. Ameen tace.
   Bashida buri a duniya d'aya wuce ya farantan rai kullum fatan sa yaga murmushi da kwanciyar hankali a fuskata.

   Kwanciya tai idonta na kallon silin d'akin zuciyar tace tafara haskomata rayuwarta ta baya da abubuwan da tayi da komai

  

     @ut@r h@jiy@ ce.
[5/16, 8:23 PM]


🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

©ZAINAB Y HUSSEIN

Dedicated to Aunty YBK & Meena D'an Musa

Page 2⃣

"K'ulululu k'arar murd'awar cikin ta shine yai dalilin dayasa Maman Zahra ta farka daga dogon nazarin da ta tafi.

   Cikin tane ya k'ara murd'awa bashiri ta diro daga gadon tai hanyar fita.
Downstairs tai anan tabi wata yar corridor wadda itace zata sada mutum da ainihin madafar gidan.

  Shiga tai flask na tea da plates guda biyu ta d'ebo wanda nikaina bansan ko mainene ciki ba, zama tai a k'asa bayan ta dire kayan hannun ta, bismillah tai tea ta had'a sai chips da kwai wanda sune cikin plate d'in.

  Cup guda ta zuba, a hankali take sha harta gama, a inda take bata motsa ba, tajiyo sallamar qawarta.

" Assalamu alaikum Maman Zahra na gida?, daga bakin k'ofar parlour d'in take maganar. Wa alaika salam yar uwa Deedoh Maman Zahra na nan, ok na iya shigowa yanzu, shiga tai da murmushi kwance a fuskarta tanason Zainab kodan kirkin ta.

   Hmm Allah Deedoh wataqil a hanya zaki haihu kalli cikin ki inda yai k'asa amma bazaki bar fita ba, ko da yake laifin Ahmad ne daya ke barin ki amma ace mace bazata dena Haihuwa ba
   Haka kike gani amma fa bai isa Haihuwa ba, cikin ne wannan karon mai girman tsiya. Haba nayi Haihuwa d'aya biyu uku aikam nasan yanayin da d'a ya kusa zuwa duniya.

  Hhh lallai kam ga na hud'u a cikin ki dole ki sani. Kee ! bangane ba wai ya akayi ake gane inada ciki?, tanayi tana shafa cikin ta, mhm wallahi haka Abban su Zahra yake gayan wai inada ciki bayan kuma koni bansan yadda yake ba saidayakai wata biyu zuwa uku.

   Amma ke uwar kwakwaf kingani, dariya Deedoh tasaki saboda yadda Zainab tai maganar a shagwab'e saikace tana gaban Mohd ko Iya Mai kalwa

    Maman Zahra nidai nagani wallahi duk wanda yaganki yasan kinada ciki saboda kin canja sosai fin yadda kike samun ciki ma.

   Hoo nashiga dad'i Allah dai yaraba lafiya, komai daga Allah yake amma wallahi nayi allura last 3 months fa, Ashe tsarin Allah yafi gaban wasa nayi nawa shi yayi nasa lokacin danake ganin kamar nawan zaiyi aiki.

      Wallahi haka ne Zainab nima nayi planing amma baiyi ba, kinga akan su Hassy saida nayi amma baiyi ba wannan ma haka, shima baiyi ba nidai nama dena insha Allah saboda baiyi ba, haka Allah dai yake son gani na shiyasa baiyi aiki cikin jiki na ba.

    Tabbas haka ne Deedoh da zamu gane planing ba wani abu bane face tura Haihuwar ka gaba, bangane ba?.

  Eh mana Idan Allah yai nufin yara 5 zaki haifa kin haifi 2 kika fara tsarin iyali kinga kenan haihuwar ki ki ka tura gaba kina girma Kuma Haihuwa na jiran ki abinda ake so ka huta Idan girma yazo to kai ka tura ta gaba duk wayon ka dole ragowan su fito.

    Kwarai da gaske fatan mu Allah yaimana mai kyau, yabamu yara nagari. Ameen yar uwa.
    Bank'i Idan akace kana wahala wajan haihuwar ba, ko Kuma talauci yayi muku sallama bakuda abinda zaki Iya ci da yaran ko Kuma irin kwanikan nan kake saika yi shima daidai, amma Idan babu d'aya daga ciki nidai a nawa tsarin planing baiyi ba, wanda nai a baya shima dan ina kwad'ayin aikin Hajji ne.
    Eh to ! amma kina ganin cewa mutum shike ciyar da kansa da Iyalan sa?, Allah shine yabaka Kuma shine yasan yadda zaiyi da kai da Iyalan ka, Allah dai kaimana mai kyau. Ameen
  
   Hira suka zauna sunayi sosai Kamar me tama manta da wani damuwa data tuno a rayuwar ta.

   Ba Deedoh tabar gidan ba saida lokacin tashin yara yai daga makaranta sannan itama Zainab ta mik'e key ta d'akko suka fita tare a gidanta ta sauke ta tunda ita batazo da Mota ba, saboda cikin ta.

  Tana ajiye ta sauri tai ta tafi d'akko yaran ta. A bakin gate na farko ta gansu tare da Amaa da Muneeb suna wasa bayan su Aunty Rose ce tsaye tana kula da su.

   Gaisawa sukai sannan taiwa yaran magana saboda taga basu kula ma tazo ba.
Zahran na bakiga Mamma ba?, da sauri ta d'ago yeh Momma tazo d'aukan mu Amaa ba'a zo ba kinga saimu tafi mu barta ko Mamma?
A'a Zahra bara naiwa Maman ta waya Idan bata tawo ba saina kaita amma bazan barta ba.
Bata ma kira ba tajiyo maganar Maman ta, itama gaisuwa sukai anan suka d'an tab'a hira itama saida tace a'a an k'unso wani ashe?, lallai to Allah yaraba lafiya.

   Ameen Ameen sai anjima yau da Gwadabe Maitasa kada su makara dan Malam Auwal ko Malam Haruna (yanamu) basa tausayin yara duka suke kamar sunsami jakai.

   Hhhhh yar uwa ashe kin gane? nima shiyasa wallahi Idan ba k'addara ba, banson Amaa tai latty, ah to haka kawai adukarmaka yara. Mota kowacce ta shigewar ta suna d'agawa juna hannu haka suka fice daga gate d'in.

   A hanya sai zuba mata surutu suke amma ita hankalin ta tashe yake saboda batayi musu  lunch ba gashi 1 tayi 2 Kuma suke shiga kafin tai musu wanka su shirya har suyi Sallah time ya k'ure.

   Juyawa tai my Zahra yau Mamma batayi girki ba me zakuci?, Mamma muje green park kawai musha tea ma is ok banjin yunwa sosai I can manage har na dawo daga Islamiyya.

   A'a nidai indomei zanci ko chip kinsan indomein green park akwai dad'i saimu biya Yahuza musayi ko 1 chicken ne ko Toma's.

   Kai ta jinjina alamar OK. kwana tai kawai ta d'auki hanyar wajan, dai dai kwanar ne Zahar tace Momma Maman su Mashkoor bata kasu ba yau, eh sunje Bauchi biki dats why yar gidan Mamma.

   Gudu gudu sauri sauri tai tabada cash aka zubo musu Zahra harda ita wajan cin Indomei Momman su itace ke fifitawa sannan ta sawa kowa a baki a haka har suka gama.

    Wajan kowa kallon su yake yanda sukaga Matar na kula da yaran ta, daga nan suna fitowa yahuza suka tsaya nan ma aciki tabarsu ta shiga da kanta tunda taga kamar babu yara a wajan da zasu karb'i kud'in.

   Kaa musu tai acikin motar suka ci har suka kai gida.
In 20 minutes harta shiryasu sunyi Sallah takamo hanyar kaisu Islamiyya (kaga uwa tagari mai son ilimin yaran ta, sab'anin wasu iyayen da sune zasuce yaran su zauna).

@ut@r h@jiy@
[5/16, 8:23 PM]

🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

©ZAINAB Y HUSSEIN

Dedicated to Aunty YBK & Meena D'an Musa

Page 3⃣

  A mota fad'an datasaba yimusu shi take musu su  ringa zama a gaba Kuma banda surutu da fad'a karatu shiya kaisu kuma shi ta umarce su da su yi.
"Cikin qanqanin lokaci harta isa cikin makarantar. A bakin k'ofar makarantar ta sauke su sannan ta jiyo.
Ba go slow a hanya shi yasaka tai saurin isa gida cikin qanqanin lokaci, parking tai a ma'adanar ajiye motoci sannan ta shiga gida.
Mayafin jikin ta ta cire da abayar data saka gefe, daga ita sai under sai vest cikin ta ta kalla a hankali ta shafa ya d'an fara tasowa kad'an addu'a tai ta tofa a hannu sannan ta maida cikin nata.
" Kitchen tai, cak ta tsaya tarasa mai zata d'ora ga shi yaudai batajin take away zasu yi, so gara tai girki da kanta.
Freezer ta bud'e kaji ne cikin ice a yanyanke cikin Leda kajin Hausa ne bana turawa ba, Leda d'aya ta d'akko kan sink taje sai roba data d'akko ciki tasaka wankewa su tai tsaf sannan ta zuba cikin tukunya albasa ta yanka da kayan k'amshi sai na'ana da garlic datasaka kad'an kayan spices ta zuba tamaida murfin ta d'ora.
"Couscous ta d'akko ta ajiye sai flour 3 cup data d'ebo zarayi Roti da samosa.
Lokacin kad'an k'amshi ya gauraye gidan na girkin ta, kayan fruits tayi blending ta tace saiga lemo ya had'u 5:30 daidai tagama komai wanke wanke tafarayi sauri take taga lokacin tashi yayi.
" ohp nagaji amma duk da haka saina gyara gidan nan, shara da mopping tai saurin yi ta gama wankan ma batayi ba ta tafi d'akko yara.
  Rayuwar Zainab a gidan ta da yaran ta abin sha'awa komai cikin tsari takeyin sa komai da ka'idar sa batada sakaci cikin alamranta. Yaranta kansu abin sha'awa tana tattalin lafiyar kowa baran mijin ta abin alfaharin ta.
Wanka shi tafara yiwa yaran ta tasamusu kaya sannan tace kowa yaje yai alwala lokacin sallah yayi.Itama wankan ta shiga k'al ta fito material blue tasaka da sarka milk tai make up nata mai kyau already dama da alwalan ta so kodata fito yaran su har sunyi sallah itama tata tayi addu'a suka zauna sukai,  yaran Mamma ayiwa Abba addu'a Allah yabashi sa'a akan aikin sa ya d'aukaka sa kinji?
Tom Momma haka suka zauna ana kallo har akayi Isha'i sannan akatafi kan dining.
Wow Mamma wannan k'amshin fa?, bud'e flask din Zahra tafara, waih Mamma yau zanci abinci da yawa Allah yasa cikina yazama na zani inacin abinci yana zubewa daga gani zaiyi sweet.
A kujera suka zauna itadai Mamman kallon ta kawai yake, Zahra tafiya surutu zuba musu tai cikin one plate couscous din sai roman kaza da kayan snacks d'in.
Ido Zahra ta bud'e kaiii ....! Mamma  gaskiya adenama take away kiringa girki da kanki wallahi Ji yadda gidan nan ya d'auki k'amshi ina sallah ina ina tunanin abincin nan naki Momma.
Zahra Allah ya shirya ki Ameen Momma. Tsam ta mike daga kan kujerar data ke kan table din dining da aka zuba abinci shi ta zauna ta tankwashe k'afa tai bismillah ta saka hannu, ko a jikin ta Zahra bare taga kallon da Momman ke mata, kai Zainab ta jinjina tana addu'ar Allah yasa Zahra bazata yi rashin kirki ba.
A haka suka ida cin abincin, kafin nan suka d'ebo Home work Zainab ta taimaka musu akan Home work d'in.
9:30 suka gama  kayan kallon ta kashe ta kwashe kwanukan abincin flask da samosa kawai ta d'iba tai d'aki dashi .
"Tare da yaranta ta kwanta bayan sun cire kayan su, sun maida na bacci addu'a sukai sannan ta kashe wutar NEPA taja musu bargo suka rufa.
    Tana kwance shiru shiru saidaga can taji saukar numfashin su, kan yaran nata ta Shafa tana son su bakin zahra ta shafa woo Zahra magana.
Wayarta ta janyo kafin tashiga wani abu tafara ringing mijin tane sun jima suna waya daga baya itace tace masa zatayi bacci sannan sukai sallama ta ajiye wayar.

©@ut@r H@jiy@
[5/16, 8:23 PM]

🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

®NWA

©ZAINAB Y HUSSEIN

Dedicated to Aunty YBK & Meena D'an Musa

Page 4⃣

  WAIWAYE ......

  Rano local government garine mai girma yana tsakankanin Kibiya da Bunkure yana qasan garin Kano ta dabo yana Kuma d'aya daga cikin qananan hukumomi 44 na garin Kano d'in.
Gari ne mai kyau daidai misali akwai 'yan kasuwa cikin sa masu noma masu saida abubuwa dai gashi nan Tumaki  da shanu Man gyad'a da sauran su
Acikin garin akwai unguwan ni da dama  ciki harda tsohon gari wanda yana kusa da ainihin cikin birnin qauyen, kusa yake da kasuwar garin da Kuma motor park na qauyen, kai a takaice dai Tsohon gari Kamar birni ne.
   Baba mai kalwa mace ce tsohuwa wadda kowa yasanta ta shahara akan sana'arta ta saida kalwa badan komai ba, saidon ta iya sosai ba algus bare aje ga saka waken suya ko wani abu, kaf qauyen na Rano sunsan da zaman ta, kowa Kuma ya tashi siya ko sari wajan Baba Maikalwa zashi tanada rufin asirinta daidai gwargwado.
Yaran ta biyu kaf maza babban shine Aliyu saimai bimasa Umar wanda tsakanin su akwai tazara ta wajan shekara 9 su ne kad'ai yaran ta batada mace ko d'aya tanason yaran ta sosai.
Aliyu yayi makarantar sa boarding school a Kibiya, daga nan Kuma yashiga makarantar maza ta garin na Rano, yayi karatunsa cikin sa'a lokacin daya gama babbar makarantar sakandire alokacin shi Umar yake ma primary, Aliyu yana son qanin sa sosai badan yaso ba ya tafi ya barsu tunda Allah yabashi sa'ar shiga makarantar gaba da secondary wato FCE dake ainihin cikin birnin Kano.
Baba Maikalwa tanada wata 'ya ita yar qanwar tace take riqewa tanason ta sosai itama tana aji uku a primary tare suke tafiya da Umar wanda yanzu yana secondary aji uku jinin su yazo d'aya.
Rahma yar qanwar Baba ce zaman ta a wajan ta yasamo asali ne lokacin da Mahaifiyar ta ta rasu mahaifin ta shima haka shiyasa ta d'akko ta take riqeta, riqo na tsakani da Allah ba kyashi ko cutar wa cikin zaman su.
Aliyu karatu yai gaba sannu a hankali lokaci na wucewa har Allah yaka ranar da suka kamalla makarantar abokin sa shiyai masa jagora da taimakon mahaifin sa yasamu BUK inda yafara karantar Medicine dama gashi da qoqari kowa yasan Aliyu kwaro cikin makarantar Idan ka ganshi bakace a cikin Rano yake ba dama ba laifi gashi kyakyawa son kowa qin wanda yarasa
"Baba tana son yaran ta, Aliyu dai cikin ikon Allah yagama karatun sa cikin nasara da sa'a tare da d'umbin kyaututtuka daga malaman makarantar  da Kuma k'arfin addu'ar Mahaifiyar sa da qanin sa da Kuma Rahma.
" Result d'in sa yai kyau direct yasamu aiki a AKTH matsayin mai girma kuwa tareda Mota da gida kuma gashi a lokacin Allah ya had'a sa da mace yar kirki Asma'u.
Baba ta yaba da Asma'u ta Kuma godewa Allah inda ya d'auka ka mata d'anta, kuma gashi Aliyu yanason Babar sa da qanin sa komai zaiyi saida shawarar ta shiyasa yake ganin bud'i da falala akoda yaushe (sabanin wad'an da suke gujewa iyayen su Idan rufin asiri yazo musu).
   "A unguwar Gadon Kaya gidan da aka bashi yake wajen gidan Alhaji Mohd D'ansararin Kano ana layin gidan sa yake.
'Yan uwa sunyi masa kara wajan zuwa kaimasa kayan kud'in zance da kayan aure tunda lokaci d'aya akasaka da ita Asma'un da yayan ta so ba wani lokaci abin zai d'auka ba.
Umar da Rahma a yanzu suna secondary Kuma alhamdulillah sun maida kai wajan karatun su, Baba a kullum burinta d'aya Allah yasa Umar yaso Rahma taso Aliyu ya aureta amma Allah baiyi ba kuma Ba zatayi tallan 'yarta ba.
Lokacin biki yazo, ansha shagali sosai dan a nan Ranon ba qaramin biki akayi ba Baba kud'in Kalwa yai aiki sosai. Amarya itama tai abubuwa Kuma a ranar lahadin bayan d'aurin auren aka tarkato suka tawo Rano da amaryar.
Kwanan su uku a garin suka koma Baba tai murna dan bata zata yarinyar zatayi hankali ba amma saitaga sab'anin haka yarinya mai kamun kai da tarbiyya.

  ***** Bayan Shekara 5

Acikin sharkarar anyi abubuwa da dama ciki harda haihuwar Asma'u inda tasami d'anta namiji inda yaci sunan MOHD, Sunan Abban Aliyu ne.
  Anyi suna da shagali sosai taro biyu gana Rano na Baba gana uwar yaro komai sai san barka.

@ut@r h@jiy@
[5/16, 8:23 PM]

: 🌪🕸 TUNA BAYA🌪🕸

®NWA

© ZAINAB Y HUSSAIN

Dedicated to Aunty YBK & Meena Dan Musa.

Page 5

  Haka rayuwar take tafiya sannu a hankali komai kuma cikin sauqi.
Yaro yana girma son kowa qin wanda yarasa gashi mai hankali tun yana yaro.
Abban kano yaso su Baba su koma kano amma taqi
" tace nan ne mahaifarta so babu inda zata anan zata zauna harta mutu ba yadda ya iya haka ya kyaleta saidai yamata gyara sosai a gidan aansanja abubuwa da yawa daga ciki.
Ansaka dogwayen katangu a tsakankanin maqotan su da sauran ragowar wuraren dake cikin gidan.
Tunda dama bawai Baban ita daya bace a gidan da akwai matan qanin mijin ta da kuma yayun sa
Shekara kwana gamai yawan rai tunda gashi ayau Rahma tagama secondary school dinta kuma soyayya ta qullu tsakanin ta da Umar wanda cikin gidan babu wanda bai sani ba saboda murna da d'okin da Baba take.
  Umar kasuwanci ya zaba yana qare makaranta baitsaya yin wata ba yanunawa d'an uwan shifa kasuwanci yake so, Abban Mohd baiso ba amma haka ya daure ya nunamasa ba komai shago ne aka siyamasa a kasuwar garin Zannuwa ne acikin shagon gefe kuma kayan sanyi dangin su lemuka ruwa madara gasu nan dai.
    Baba itace tamatsa ayi biki saboda ita tanason ganin jikokin ta na wajan Rahma, to kusan shima Umar din haka yake so shiru kawai yayi amma Baba na maganar yanuna amincewar sa.
Shima Abban Mohd yaso yace afara maganar aure saiyai shiru yasan halin Baba idan ba ita taso abu ba, amma yanzu datayi fine.
Ba wani dogon lokaci suka d'auka ba wata uku kacal akasaka shima dan gyare gyaren da za'ayi ne a sashin su acikin gidan zai zauna saidai shi bangaren sa daban qofa dai daya ce sai abinda ba'arasa ba
  Cikin wata uku amarya Rahma tasha kyau da gyara dan Baba tanaji da rahma ba kadan ba tana sonta kulkum fatan ta Allah yakai Rahma inda za'a ganta da daraja ko wani cikin yaran ta yasota saigashi Rahma zatayi aure da d'an ta kuma su zauna waje d'aya.
  Baba wai mekike tunani haka ko d'an tsohon ki kike tunawa? uwaki nake Rahma ina dai murna zamu zauna waje guda ko ke bakiyi?
Inayi mana jikin ta ta fada wash k'afafun zaki qarasa mata tashi maza akanta Umar ne mai maganar.
Hararensa tai tace na zauna wani idan yaso ya zauna, haba nifa sainace nafasa, " to kifasa mana, dama ai kece kika nacen.
Rahma da sauri ta miqe "tace enye lallai amma ka yanken nice ma nake maqalemaka? Eh mana Umar yace "to naji nidai banso yanzu kashafan lafiya kaje kanemi wata can ba Rahma ba.
Dariya Baba takeyi, " tace kunji dashi tashi kubani waje kada kucikan kunne, idan yaso akayi auren kwa qarata can.
  Haka lokaci yake ta tafiya, har Allah yakawo  lokacin bikin a yanzu haka ana cikin satin rabon goro, komai ya kankama shagali sosai ake cikin bikin.
  Kayan d'aki daga kano aka kamata Abban Mohd ne yasiyo mata kayan kitchen da tarkacen amarya babu wanda bashi ya siyo ba, wannan abin da yai yaqara d'aga darajar sa wajen Baba da dangin su.
Rahma y'ar gata komai yimata akayi baba sai murna.
A yau aka daura aure takuma tare cikin gidan mijin ta Umar bayan shagali da addu'oi da suka sha.
Abin dariya wai saiga Baba na kuka sosai itada Rahma, dariya suka bawa mutane bayan gida d'aya zasu zauna amma suke wani kuka, kona mene oho?.
  Zaman Rahma da Umar zamane na amana da yadda da juna, Rahma tasan takan Umar tunda tare suka tashi tasan meyake so da wanda baya so, abinci ita take kayan ta , ta kuma d'aukewa Baba yin girki, komai ma ita Rahman ita take zuwa tai mata shiyasa Baba ko da wasa bata barin Umar yaimata ba daidai ba.
Mama. Matar Abban kano itama tana zuwa Ranon sosai, dama tasaba da Rahma idan kagansu bakace faccaloli ne ba, saboda yadda da juna, Mohd shima yasaba da Rahma sosai.
Yanzu haka anyi hutu yana wajen ta, Komai Mohd shima Aunty sosai yaron ya shiga ranta, bashida b'arna ko surutu maganar sa da Rahma ne ko Baba, itama baya kulata saitamasa magana.
  Abban Kano yaran sa biyu, mace da namiji, anyiwa Mohd qanwa, Zahra sunan ta itama tanason zuwa Rano amma wannan karon bada ita akazo ba.
  

  autarhajiya ce
[5/16, 9:09 PM]

: 🌪🥗🕸TUNA BAYA🌪🥗🕸

©ZAINAB Y HUSSEAIN
   
     ®NWA

Page  7

A yau ne Allah yayiwa Rahma rasuwa, sakamakon ciwon ciki na lokaci kad'an daya kamata, wanda aqoqarin su nasukaita asibiti aduba lafiyar ta ALLAH yai ikonsa.
A d'akin ta kan gadon ta ta cika, kusa da ita jaririyar tace Zainab yar kimanin wata tara.
Inalillahi wa Inna ilaihi rajiuun, Rahma ! dama ke bamai tsahon rai bace?, Rahma yazakimun haka, bayan kinsangartani da kyawawan halayen ki abin koyi ga duk wata d'iya mace.
"Rahma kitashi game din is over, yazakiyi da baiwar Allah dazakice zaki tafi kibarta?, Rahma....... jijjigata yake Umar yana kuka yana sunbatu sakamakon sanin cewa ta Allah ta kasance akanta, tunda alamu sun nuna tsofaffin gidan sun shaida Rahma ta amsa kiran mahalicin ta.
Ganin yadda Umar yafita a hayyacin sa hankalin sa ya daga yasaka manyan wajen fita da shi.
Baba kuwa ba'asan inda kanta yake ba, dan tun lokacin da tai duba izuwa gangar jikin Rahma tasan cewa Allah yayi ikon sa, daga nan ta zube a qasa.
Allahu akhbar duk mai rai mamaci ne, Rahma da akayi sallar Azahar da ita amma gashi wai babu ita meyafi wannan tashin hankali?.
Dangi kuka, ga babyn ta itama sai kuka, kowa kagani kokawa yake a wajen.
Abban kano da mutuwar ta riskeshi akan hanyar sa ta zuwa garin, hakan ne yasaka yace driver nasa yai sauri suje ko dogon suma ne.
"Ta mutu shikenan abinda Umar yake fad'a kenan, abin tausayi haka akaimata wanka, Abban kano ya sallace ta yana kuka nabayan sa nayi aka kaita gidan ta na gaskiya wanda ni danake rubutawa nima sainaje shi ko ba dade ko ba jima mutuwa rigar kowa, tana kan kowa babu wanda zata shallake kodan kai wani ne, dame kake taqama?
Mulki, Sarauta Izza da d'agawa, cin dukiyar daba taka ba, kodan kai shugaba ne mai fada aji, ko kai group admin ne?.
Hhhhh to ita mutuwa bataduban kai waye ko ke wace, lokacin ki nayi zata d'auke ki batare da tayi duban ke marainiya bace, ko ke jinjirace ko tsuhuwa,Allah kasa mu dace da dacewar ka.
Baba ba ita ta farfad'o ba sai bayan ankaita andawo ma. Abban kano idan sa jajur saboda kuka, Umar kam ba'a cewa komai.
   Bayan kwana 7.
Anshare makoki, yarinya Baba "tace ita zata d'auka, babu musu akace to.
Umar abin tausayi yazama kullum cikin tunani da zaman d'aki gani yake kamar Rahma zata zo ko zaiga wucewar ta, amma shiru tafiya tai tafiya.
ZAINAB nasamun kulawa sosai wajen Baba, kuka wannan Baba bataso ZAINAB tayi, Kamu madara shiitake sha abinta ba kuka ko hayaniya.
    Shekara hud'u gaba.
Cikin shekarar ne Umar yayi aure, ya auri wata Amina, to gata nan dai amma kirkin nata kad'an ne saidai, atafi a haka.
ZAINAB yarinya so cute, kamar ba rainon Baba ba, ko dayake Abban kano shiyake mata komai, kayan wasa gasu nan birjik.
Tana zuwa makaranta sosai, duk da tana yarinya amma idan kaji karatu da zance abakin ta, abin ya b'aci.
Matsala guda, rashin kunya, zainab number one ce, a four years amma ta iya zagi, harara murgud'a baki.
Baban ta idan yaga tana zagi ko harara sosai yake mata fad'a, amma inaa Baba naji zata fara sababi marainiyar Allah ba za'a barta ta wataya ba, ai zata dena yarinta ce.
Gata da b'arna dan akwai lokacin da Baba ta had'a kalwar ta, ta wajen 50k, Zainab tasamata ruwa da yawa, waih ranar taci duka wajen Baban ta.
Baba kam tana zuwa, "tace inaa batasan zance ba, kud'in sane?, ko kayan sane?, dazai kamamata 'ya da kuka.
Saidayayi danasanin dukan ta, dan kuka tasaka "wai ta lura baya qaunar zainab ko matar sace ta sakashi?, ita zata barmusu gidan haka kawai akama ajibgi 'yar ta, ranar sunga tashin hankali har faccalolin ta saida suka saka baki sannan magana ta wuce.

Autar hajiya ce
[5/16, 9:09 PM]

🌪🕸TUNA BAYA🌪🕸

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

© ZAINAB Y HUSSEAIN

Page 6

Baba abinda take fata da buri shi yasamu dan Rahma ciki gare ta, wajen wata hud'u kenan, d'oki hooo saidai ayi shiru.
Aiki tahanata, abinci ita ke dafa musu, shara wanke wanke duk ita keyi, "tace tafison ganin Rahma a zaune tana bata ganta tana aiki ba.
Rahman ce ma taqi, "tace Baba nidai kibari zanyi shara da wanke wanke, girki naji kiyi, da qyar ta yadda da haka, "tace ni ina ruwa na, ke 'yata ce ba suruka ba, matar Aliyu kinaga inaimata ne? ko ina zuwa gidan su?
A'a Rahma "tace, yauwa kinga ke amana ce a wajena, fatana Allah yabani lafiyar da zanmiki abu, ke 'yace wajena yar qanwata kike wadda nake so sosai, bayan haka nina riqeki nabaki tarbiyya daidai to danme bazan miki abinda yake wajibi a gareni ba?
Baba nifa ba wani abu nace ba, nice dai banson ganin ki kina aiki, nafison ganin ki cikin hutu, tsufa yazo miki kamata yai ace ko aikin kalwar nan kindena shi zamanki cikin dakin ki yafi.
Hoo 'yar nema kina magana kamar mutuniyar arziqi, Rahma kece abar tausayi ai baki ganin abinda ke gaban ki?.
Baba nifa bai takurani cikin nan, kece kike ganin kamar da wuya wataran har mantawa nake inada ciki ma.
A'a Rahma kiringa kula kina lura kinji? Tom Baba. Yauwa mezakici yau?, kwaad'an Rama nake so asaka sugar ciki amma kada asaka albasa tumatir da koren tattasai kawai.
Yauwa bara natashi, kamar kinsani jiya danaje Tuwan garwa nasiyo Rama me yawa kuwa, bara na had'amiki, kafin na dawo kiyi wankan kince zafi kikeji? Eh Baba, yauwa to maza kiyi wankan kafin nan na hadomiki.
  Fita Baba tai, itakuma ta mik'e ahankali tai toilet. batajima ba tafito daga wankan, T shirts tasaka sai zani data d'aura, cikin ta gashi nan harya fito abinta, gwanin sha'awa.
  Shara tafara sauri sauri, tana gamawa sai wanke wanke, zaman ta kenan saiga Baba. Yauwa Rahma kinfito maza ga ramar har kunu na tsamiya nai miki ko baki so?. Inaso mana yau shar dani kinsan jiya da daddare kasa cin Taliyar nan nai, saida natashi nai kunun daga yau shizan ringa yi.
Ah kice nabada a surfe mana geron, tunda kinaso, bara umar yazo saiyaje kasuwa yasamo sabuwar tsamiya dan zatafi.
  Allah mai lokaci, cikin Rahma yashiga wata na tara, baiyi wani qato ba, ba wahala a tare da ita, haihuwa ko yau ko gobe, anci burin suna dan Abban kano shima kansa murna yake, Mohd kam a yanzu yana Hassan gwarzo Jss 1 going to  2 .shekaransa goma sha biyu, sai Zahra qanwar sa mai pri 3.
   Alhamdulillah, Allah ya sauki Rahma lafiya cikin Gen Hospital dake garin na Rano inda Allah ya azurta ta da samun d'iya mace, qatuwa dan kowa a asibitin saiya ce Tabarkallah kamar ba Rahma ta haifo ta ba, dan cikin ta bai nuna zata haifi qatuwar yarinya haka ba.
Lafiya lou ta haihu, basu jima a asibitin ba, akabasu sallama. Baba wajen ta tai da ita, anan aka sakamata katifa itada yarinyar ta.
   Yarinya Mashaa Allah kamar ba diyar Hausawa ba, baqa ce dai dan kunnuwan ta sun nuna alama, amma a yanzu jajir take gashin kanta kwance yake cinkus da yawa fuskar ta duk gashi ne ido mashaa Allah
Kama tai da Abban kano, konace da uwar ta, dan ita Rahma da Yaya Aliyu wato Abban kano take kama, kusan dai da Baba mai kalwa duk suke kama dan Baba badan rayuwa ba kace tsada ce wajen fari ga gashi mijin ta ma haka yake da kyau yarinya dai ita kowanne b'angare ta dakko dan tafi uwa da uba kyau.
'Yan barka kota ina zuwa suke, Baba ta mutane. Abokan Abban kano d matan su, suma sunyita turuwa wajen zuwa kenan, sunsami kayan barka Mashaa Allah.
  Baba tana kula da yarinya da uwar ta, dan jaririya kullum kazo tana hannun Baba har dariya ake mata, Baba "kodai ke zaki riqe yarinyar irin wannan so haka?, "Takan ce ai kunsan ance abin cikin kwai yafi kwai dadi, to haka yake waje na yarinya kuwa ai Tawa ce dan dani akayi rainon ciki, dariya take bawa mutane idan tace haka.
ZAINAB shine sunan da akasakawa yarinya, sunan Baba ne, wayyo zokaga murna Baba anyi takwara.
Suna anyishi lafiya an qare lafiya sai fatan Allah yabata sa'ar shayarwa.
  Rahma taci gaba da rainon yarta cikin kwanciyar hankali tare da taimakon Baba da Abban ta, yarinya mai haquri batada kuka wataran idan Baba ta fita da ita sakai la'asar basu dawo ba, gidan suna ko biki qa'ida da ZAINAB za'aje.
  Sun sakaya sunan ana kiranta da Nana duk d ita Baba batason Nana ZAINAB take kiranta dashi.

RANAR BAKIN CIKI...

  A yau Talata 12-12-2012, Ciwon ciki lokaci guda, yatasar mata, batare da taci wani mugun abu ba, daga Allah, dama ance idan ajali yai kira koba ciwo sai anje haka ta faru da .....

Autar Hajiya ce

TUNA BAYA

ZAINAB Y HUSSEIN

نغرة ريتس اسوسيشين NWA

Page 8

Yau kam Zainab gidan su tashiga, wajen matar Abban ta, da shigarta ta tarar da manja da man kuli, batayi wata wata ba kuwa ta had'esu gu guda, sannan ta dauki cokali tana wasa da shi tanasawa a fusk.
Lalalala Zainab ! Eh lallai zakici uban ki rashin mutuncin naki yai kauri, kin wuce na gida kinzo kaina zanci uwarki kuwa yau.
Tsinke na kwakwa ta ciro, tafara tsula mata ganin zatai mata ihu yasaka ta rufe qofa ta toshemata baki saidata jibgeta son ranta sannan ta qyaleta a wajen tabarta ga rana "tace idan ta miqe saitaimata dukan dayafi wannan.
Tun wajen 10am take wajen har 1na rana tana kwance baccin wahala shiya tafi da ita, ita Amina ma tamanta da wata Zainab a wajen saidata fito ta gan ta, sannan kuma lokaci daya taji bugun kofa Baba ce "kecewa ke kina ina yar amana shiru banganta ba kota na nan?.
Baba mekika ce?, "eh cewa nai takwara ta shigo?. Ehmm..... banganta ba tun yaushe? To bazaki bude kofar ba a haka zanmiki magana eyeh?.
Da sauri Amina ta dauki Zainab ta fara gogemata hawayen fuskar ta tana gyarata kan gado ta ajiyeta tace ke kimun shiru dayake ta farka.
Bud'e qofar tai "tace Baba to ina tashiga?, nikuma ina runfa bacci ya daukeni amma bara naduba ko cikin gida ne?.
Hmm nafa duba koina to ina zainabu tashiga?.
Baba baradai na d'akko mayafi, da sauri ta shiga cikin uwar d'aka tana laluben qarya.
Lailaha ilallah! Baba zokiga?, mezangani nidai kiyi sauri kawai, kishigo dai kiga.
Mts kinga banson shirme, hannu ta tafa tace lallai Zainabu wato ta gudo harda kwanciya a gado?, to nayi nan idan ta tashi kimata wanka ta tafi makaranta, idan kuma zatayi kuka kibarta tai wasan qasan ta kibata goma tasiyo yashin madina ko tsami gaye kinji?.
Tom Baba zan mata saikin dawo, to saina dawo kinga"ko wankan ne idan taqi kibarrta.
Tom naji tana magana tana yatsine baki"cikin zuciyar ta kam takaici kamar ya kasheta wai wankan ma a kyaleta idan bataso.mts zakici uban ki yau kam.
Tunda jiya akanki Baba taxage iyayena tas. Me kike jira ne wai? Ba komai saikin dawo, TO zainabu gashi zan fita baki nan oh Allah yasa bazatayi kuka ba? Ameen Amina tace sabida takaici bata bari Baban ta tafi ba ta juya daki abinta.
Ido ta zaro ganin Zainabu a bakin qofar dakin nata wanda d'aga labule kad'ai ya ragemata Baba ta ganta da sauri ta figeta sai uwar d'aka, ke! bakida hankali banace kada ki fito ba, eh to halin naki ya motsa kunnan ta ta kama ta murd'e hawaye Zainabu kawai ke fiddawa ganin azabar tai yawa yasaka ba shiri zainabu takama hannun Amina ta gantsara mata cizo.
Kee ni kike ciza cikani, hhh zainabu kam qara datsa mata haqori tai saidataga jini na fita sannan ta cikata ta fita da gudu tana dariya.
Kuka Amina tasaka saboda yadda taga cizon yai yawa fatar wajen ta fice gashi abin takaici shegiya dariya taga tanai mata tab lallai tasiyowa kanta duka, haka tagama maganganun ta tashi zuwa gyara hannun ta.

***********

Can ita kuma zainabu tana fita bata zame koina ba sai wajen Deedoh qawar ta da Anker, tana zuwa kuwa taga Anker natsokanar mai agwaluma batayi qasa a qwiwa ba itama tabi layi sukafara tsokanar sa wai duk tsami sannan ga tsutsa cikin ta.
Duk wanda yazo siya sai Anker tace malam kada kasiya kaga tawa duk tsutsu haka take, sukam mutane idan sukaga haka sai su wuce aqi siya
Takaici yahana mai Agwaluma cewa komai, bashiri ya debi guda uku ya rabamusu yace kuje tsinannu kedai anyi shegiya gara gara ma waccen yanuna Deedoh wadda batasamusu baki cikin sabgar su.
Anker ita ala dole saiya basu kyauta, shikuma ya hana, shine fa tasamo agwaluma mai tsusa take cewa tasa ce.
Tafiya sukai suna dariya sunsamu ta bati.

Autar Hajiya ce

TUNA BAYA

ZAINAB Y HUSSEAIN

®NWA

Page 9

Amina kina ina nadawo banji motsin Zainabu ba tana ina kotaje makarantar?.
Baba aikinsan halin zainabu, wanka zanmata wallahi yarinyar nan saboda rashin mutunci da rashin ganin girma na ban tsammni ba naji cizo a hannu na akan nace saitazo anyi wanka.
Hannu Baba tafara tafawa, iyee kikace zainabu batada mutunci to uwarki kika zaga, amma zainabu tanada Kirki, sunana nefa akasawa zainabu, amma zakice haka shegiya mara galihu aina lura da rashin qaunar ki wa zainabu to ahir dinki kuma maza ki fita ki nemomin  yarinya marainiyar Allah maza tashi kifita, haka Baba tatasa Amina agaba sai data fita.
Mita babu irin wadda Amina batai ba akan zainabu qarin haushi babu inda bataje ba, bataganta ba gashi abokanan wasan nata ma batagansu ba,  dole tasa ta juyo gida sashin Baba tai dan gayamata bataga zainabu ba, b'acin rai ganin ta tai itada qawayen ta suna langa Baba kuma na gefe tana dariya.
Juyawa zatayi, saijin maganar Baba tai.
"Amina ya haka aisaikice baki ganta ba, bakya juyawa ba, ashe ma tana wajen Laraba, abin da zakiyi ruwa zaki d'oramata naga batayi wanka ba, d'ora yanzu maza nima na kwara dan nagaji.
Ihu ne kawai Amina batayi ba, haka ta dora ruwan yai zafi kuma takamusu, zainabu ce tace Baba nifa a bayi zanyi akaimun ciki. To kinji kaimata cikin bayin.
Harara Amina tasakarwa zainabu itakam ko ajikin ta saima qeta datake mata.

*******
Abba idan kaje kano kace ina gaida Zahra zanzo wataran tabaka alewa ka kamun.
"Naqi nafad'a mata shashasha ita tanada hankali kuma tana zuwa makaranta ba irin ki bace marajin magana mai rashin kunya, zainabu bakisan girma kike ba wannan rayuwar da kika d'aukar wa kanki ba inda zata kaiki sai tashar danasani, inajiyemiki gaba, ke ko girkin nan ma baki iyaba shekara goma sha biyu ace kina zaune daga rashin kunya saicin kayan mutane.
Amina ce "tace, hmm kama dena mata fad'a dan zainabu ta ginu da rashin kunya, Baba batai mata gata na arziqi ba, kwanaki wallahi yarinyar nan abuta ta zubamun k'aik'ayi saidana kama ruwa tashin da zanyi naji qaiqayi kamar me?, haka na kwana na yini inajin sa a jiki na danagayawa Baba saicewa tai yarinta ce. Zainabu kam saidai addu'a amma halin ta babu na d'auka.
Abban ta kam tagumi yai yamarasa me zaice, Rahma batayi haka ba, ko abokin fad'a Rahma batadashi amma ga 'yarta kamar dage akan fad'a.
"Hmm Amina garake ta gida ce, jiya dawowa ta daga kasuwa wallahi mutum uku suka tareni akan tadaki yaran su, d'ayan kam zagi ta uwaka ubaka taimasa akan yace mata taringa zuwa makaranta shikenan itada Baba sukaje har gidan sa suka zagesa ita tanayi Baba tanayi abin takaici.
Narasa yazanyi?, aikawai kakaita boarding school sa koyamata hankali a can kuma ka zaneta yanzu shegiya ai Baba bata iya bada tarbiyya ba, nikaina haka suke mun.
"Ohoo wato kiran dakaimata kenan akan kazaunar da ita kaida matar ka kuna zagin ta abin ma yakai hardani wai ban iya bada tarbiyya ba, to sake ta yanzu taje ta auri wadda uwar sa take bada tarbiyya boarding kuma saikiyi a gidan ku koba haka ba yar gidan Baba?.
Haka ne Baba zainabu tabata amsa tana dariya. Amina kam ido ya raina fata, rantsuwa tafara akan Baba tai haquri, Baba kam ta kafe akan saki dole.
Ganin kukan nata yai yawa yasaka zainabu tace Baba a kyaleta amma idan taqara duka na saita tafi gidan su kawai.
Duka! yaushe ta dekeki bansani ba?, rannan nan ta zayyanomata komai, wai ranar Baba kam tai jaraba, qarshe dai saidata ce taje ta huta idan suma suka huta saita dawo.
Amina kam ido yaraina fata, Abba kam yanaji yana gani ta tarkata kayan ta tai gaba,shima baibi takan su ba yai ficewar sa.
 

@ut@r H@jiy@ ce

Comments

Popular posts from this blog

TUNA BAYA 10-105

Rashin Gata 166-170

Rashin Gata 141-145